Hausa translation of the meaning Page No 571

Quran in Hausa Language - Page no 571 571

Suratul Nuh from 11 to 28


11. « Ya sako ( girgijen ) sama a kanku da ruwa mai ɓuɓɓuga. »
12. « Kuma ya yalwata muku game da dũkiya da ɗiya,Ya sanya muku ( albarka ) ga gõnaki, kuma Ya sanya muku koguna. »
13. « Me ya sãme ku, bã ku fãtar sãmun natsuwa daga Allah, »
14. « Alhãli kuwa, lalle ne, Ya halitta. ku, a cikin hãlãye? »
15. « Ba ku ga yadda Allah Ya halitta wasu sammai bakwai ɗabaƙõƙĩ a kan jũna ba? »
16. « Ya sanya watã a cikinsu, yana mai haske, Ya sanya rãnã babbar fitila? »
17. « Kuma Allah Ya tsirar da ku daga ƙasa ( kamar ganye ) tsirarwa. »
18. « Sa'an nan Ya mayar da ku a cikinta, kuma Ya fitar da ku fitarwa. »
19. « Kuma Allah Ya sanya muku ƙasa shimfidaɗɗiya. »
20. « Dõmin ku shiga a cikinta, hanyõyi mãsu fãɗi. »
21. Nũhu ya ce: « Ya Ubangijina! Lalle ne sũ sun saɓa mini sun bi wanda dukiyarsa da ɗiyansa ba su ƙãre shi da kõme ba sai da hasãra. »
22. « Kuma sun yi wani mãkirci, mãkirci babba. »
23. « Kuma suka ce: Faufau kada ku bar gumãkanku, kuma faufau, kada ku bar wadda, kuma kada ku bar suwã kuma kada ku bar Yagũsa da Ya'ũƙa da Nasra. »
24. « Kuma lalle ne sun ɓatar da ( mutãne ) mãsu yawa, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai ( kõme ) sai ɓata. »
25. Sabõda laifukansu na ganganci aka nutsar da su, sa'an nan aka sanya su a wuta. Saboda haka ba su sãmã wa kansu wani mataimaki wanin Allah ba.
26. Kuma Nũhu ya ce: « Ya Ublngijina! Kada Ka bari, a kan ƙasa, daga cikin kãfirai, wanda ke zama a cikin gida. »
27. « Lalle ne, Kai idan Ka bar su, zã su ɓatar da bãyinKa, kuma bã zã su haifi kowa ba fãce fãjiri mai yawan kãfirci »
28. « Ya Ubanginjina! Ka yi mini gãfara ( ni ) da mahaifana biyu, da wanda ya shiga gidana, yana mai ĩmãni, da mũminai maza da mũminai mãtã, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai kõme sai halaka. »