Hausa translation of the meaning Page No 569

Quran in Hausa Language - Page no 569 569

Suratul Al-Ma'arji from 11 to 39


11. Ana sanya su, su gajũna, mai laifi na gũrin dã zai iya yin fansa, daga azãbar rãnar nan, da ɗiyansa,
12. Da matarsa da ɗan'uwansa.
13. Da danginsa, mãsu tattarã shi.
14. Da wanda ke a cikin dũniya duka gabã ɗaya, sa'an nan fansar, ta tsĩrar da shi.
15. A'aha! Lalle ne fa, ita ce Lazã,
16. Mai twãle fãtar goshi.
17. Tanã kiran wanda ya jũya bãya ( daga addini ) kuma ya kau da kai.
18. Ya tãra ( dũkiya ) , kuma ya sanya ta a cikin jaka.
19. Lalle ne mutum an halitta shi mai ciwon kwaɗayi.
20. Idan sharri ya shãfe shi, ya kãsa haƙuri.
21. Kuma idan alhẽri ya shãfe shi, ya yi rõwa.
22. Sai mãsu yin salla,
23. Waɗanda suke, a kan sallarsu, su, mãsu dawwama ne.
24. Kuma waɗanda a cikin dũkiyarsu, akwai wani haƙƙi sananne.
25. Ga ( matalauci ) mai rõƙo da wanda aka hanã wa roƙon.
26. Da waɗannan da ke gaskata rãnar sakamako.
27. Da waɗannan sabõda azãbar Ubangijinsu, suna jin tsõro.
28. Lalle ne, azãbar Ubangijinsu bã wadda ake iya amincẽwaba ce.
29. Da waɗanda suke, ga farjojinsu, mãsu tsarewa ne.
30. Sai fa a kan matan aurensu da abin da hannayensu na dãma suka mallaka. To lalle ne sũkam ba waɗanda ake zargi ba ne.
31. To, duk wanda ya nẽmi abin da yake a bayan wannan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙetare iyãka.
32. Kuma da waɗannan da suke ga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne.
33. Kuma da waɗanda suke, ga shaidarsu, mãsu dãgẽwa ne.
34. Kuma waɗanda suke, a kan sallarsu, mãsu tsarẽwa ne.
35. Waɗannan, a cikin gidãjen Aljanna, waɗanda ake girmamãwa ne
36. Mẽ yã sãmi waɗanda suka kãfirta, a wajenka, sunã gaugãwar ( gudu ) .
37. Daga jihar dãma, kuma daga jihar hagu, jama'a- jama'a!
38. Shin kõwane mutum daga cikinsu yana nẽman a shigar da shi a Aljannar ni'ima ne ( ba da wani aiki ba ) ?
39. A'aha! Lalle Mũ, Mun halitta su, daga abin da suka sani.