Hausa translation of the meaning Page No 572

Quran in Hausa Language - Page no 572 572

Suratul Al-Jinn from 1 to 13


Sũratul Jinn
wa’azi ga mãsu bauta wa aljannu da mutãne domin nẽman tsari ko sãmu, da ladubban mai wa’azi da yadda ya kamata ya yi tawãli’u. son girman shugabanni da jahilcin mabiya ne ke sanya ana bautawa wanin Allah.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Ka ce: « An yi wahayi zuwa gare ni cewa wasu jama'a na aljannu sun saurũri ( karatuna ) , sai suka ce: Lalle ne mũ mun ji wani abin karantãwa ( Alƙui'ãni ) , mai ban mãmãki. »
2. « Yana nũni zuwa ga hanyar ƙwarai, sabõda haka mun yi ĩmãni da shi bã zã mu kõma bautã wa Ubangijinmu tãre da kõwa ba. »
3. « Kuma lalle ne shĩ girman Ubangijinmu, Ya ɗaukaka, bai riƙi mãta ba, kuma bai riƙi ɗã ba. »
4. « Kuma lalle ne shi, wãwanmu ya kasance yana faɗar abin da ya ƙetare haddi ga Allah. »
5. « Kuma lalle ne mũ, mun yi zaton mutum da aljani bã zã su iya faɗar ƙarya ba ga Allah. »
6. « Kuma lalle ne shi wasu maza daga cikin mutãne, sun kasance sunã nẽman tsari da wasu maza daga cikin aljannu, sabõda haka suka ƙara musu girman kai. »
7. « Kuma lalle ne sũ, sun yi zato, kamar yadda kuka yi zato, cewa Allah bã zai aiko kowa ba. »
8. « Kuma lalle ne mũ mun nẽmi ( hawan ) sama, sai muka, sãme ta an cika ta da tsaro mai tsanani da kuma yũlãye. »
9. « Kuma lalle ne mũ, mun kasance muna zama daga garẽta, a wurãren zama dõmin saurare. To wanda ya yi saurãre a yanzu, zai sãmi yũla, mai dãko dõminsa. »
10. « Kuma lalle ne mũ ba mu sani ba, shin, sharri ne aka yi nufi ga waɗanda ke cikin ƙasa, ko Ubangijinsu Yã yi nufin shiriya a gare su ne? »
11. « Kuma lalle ne mũ, akwai sãlaihai a cikinmu, kuma akwai a cikinmu waɗanda ba haka bã mun kasance ƙungiyõyi dabam- dabam. »
12. « Kuma lalle ne mũ mun tabbatã bã zã mu buwãyi Allah ba, a cikin ƙasa, kuma bã zã mu buwãye Shi da gudu ba. »
13. « Kuma lalle ne mũ, a lõkacin da muka ji shiriya, mun yi ĩmãni da ita. To wanda ya yi ĩimãni da Uhangijinsa, bã zai ji tsõron nakkasa ba, kuma bã zai ji tsõron zãlunci ba. »