Hausa translation of the meaning Page No 573

Quran in Hausa Language - Page no 573 573

Suratul Al-Jinn from 14 to 28


14. « Kuma lalle ne mũ akwai a cikinmu, waɗanda suka mĩƙa wuya, kuma akwai a cikinmu karkatattu. to, wanda ya mĩƙa wuya waɗancan kam sun nufi shiryuwa. »
15. « Kuma amma karkatattu sai suka kasance makãmashi ga Jahannama. »
16. « Kuma dã sun tsayu ( 1 ) sõsai a kan hanya, dã lalle Mun shãyar da su ruwa mai yawa. »
17. « Domin Mu jarraba su a ciki, kuma wanda ya kau da kai daga tuna Ubangijinsa, Ubangijinsa zai shigar da shi azãba mai hauhawa. »
18. « Kuma lalle ne wurãren sujada na Allah ne, saboda haka kada ku kira kõwa tãre da Allah ( da su, a cikinsu ) . »
19. « Kuma, lalle ne shi, a lõkacin da bãwan Allah ( 2 ) ke kiran Sa sun yi kusa su zama kamar shirgi a kansa. »
20. Ka ce: « lna kiran Ubangijina ne kawai, kuma bã zan tãra kowa da Shi ba. »
21. Ka ce: « Lalle ne, nĩ bã ni mallakar wata cũta gare ku, kuma bã ni mallakar wani alhẽri. »
22. Ka ce: « Lalle ne, nĩ kõwa bã ya iya cẽtona daga Allah, kuma bã zan iya sãmun mafaka ba daga gare Shi. »
23. « Fãce iyarwa, daga Allah, da manzancinsa. To, wanda ya sãɓa wa Allah da ManzonSa, to, lalle yana da wutar Jahannama suna mãsu dawwama a cikinta, har abada. »
24. Har idan sun ga abin da ake yi musu gargaɗi da shi, to, zã su san wanda ya zama mafi raunin mataimaki da mafi ƙarancin adadi.
25. Ka ce: « Ban sani ba a kusa ne abin da ake yi muku gargaɗi da shi, ko Ubangijina Ya sanya maSa dõgon ajali! »
26. « Shi ɗai ne Masanin fake sabõda haka, bã Ya bayyana gaibinSa ga kowa. »
27. « Fãce ga wanda Yã yarda da shi, wato wani manzo sa'an nan lalle ne, zai sanya ( 3 ) gãdi a gaba gare shi da bãya gare shi. »
28. « Dõmin Ya san lalle, sun iyar da sãƙonnin Ubangijinsu, kuma ( Shi Ubangijin ) Yã kẽwaye su da sani, kuma Yã lissafe dukan kõme da ƙididdiga. »
( 1 ) Tsayuwa sosai wato su bautawa Allah kamar yadda Allah Ya umarce su, su yi Masa ɗa'a saboda Yã wadãta su.
( 2 ) Bawan Allah shi ne duk wani mai wa'azi yana kira zuwa ga Allah. Bã ya halatta a gare shi ya bar waɗanda yake yi wa wa'azi su kai fagen bauta Masa shi kansa. Sai ya gaya musu gaskiyar matsayinsa, kamar yadda Allah Ya faɗa wa AnnabinSa, kuma Ya umarce shi da ya gaya wa waɗanda yake yi wa wa'azi.
( 3 ) ldan Allah Yã aiko wani manzonsa da wani umurni ko hani zuwa ga mutãne to zai sanya mala'iku gaba gare shi da bãya gare shi suna gãdin sa dõmin kada wani Shaiɗãni ya kusance shi har ya sanya shi mantuwa ko kuskure, har ya iyar da manzancin nan kamar yadda yake.