Hausa translation of the meaning Page No 305

Quran in Hausa Language - Page no 305 305

Suratul Maryam from 1 to 11


Sũratu Maryam
Tanã karantar da hikimar sãmun iya da ’ya’ya ga mutãne da tsarkake Allah daga haka.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. K̃. H. Y. I . Ṣ̃.
2. Ambaton rahamar Ubangijinka ne ga BawanSa Zakariyya.
3. A lõkacin da ya kirãyi Ubangijinsa, kira ɓõyayye.
4. Ya ce: « Yã Ubangijina! Lalle ne nĩ, ƙashi na daga gare ni ya yi rauni, kuma kaina ya kunnu da furfura, kuma ban kasance marashin arziki ba game da kiranKa, yã Ubangiji! »
5. « Kuma lalle nĩ, na ji tsõron ( 1 ) dangi a bãyãna, kuma mãtãta ta kasance bakarãriya! Sai ka bã ni wani mataimaki daga wajenKa. »
6. « Ya gãjẽ ni, kuma ya yi gãdo daga gidan Yãƙũba. Kuma Ka sanya shi yardajje, yã Ubangiji! »
7. ( Allah Ya karɓa ) « Yã zakariyya! Lalle ne Mũ, Munã yi maka bushãra da wani yãro, sunansa Yahaya. Ba Mu sanya masa wani takwara ba a gabãni. »
8. Ya ce: « Yã Ubangijĩna! Yãya wani yãro zai kasance a gare ni, alhãli kuwa mãtãta ta kasance bakarãriya, kuma gã shi nã kai ga matuƙa ta tsũfa? »
9. Ya ce: « Kamar wancan Ubangijinka Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi ne, kuma haƙĩƙa Na halitta ka a gabãnin haka, alhãli ba ka kasance kõme ba. »
10. Ya ce: « Yã Ubangijina! Ka sanya mini alãma. » Ya ce: « Alamarka ita ce ka kãsa yi wa mutãne magana a darũruwa uku daidai. »
11. Sai ya fita a kan mutãnensa daga masallãci, sa'an nan ya yi ishãra zuwa gare su da cẽwa, « Ku yi tasbĩhi sãfe da yamma. »
( 1 ) Amfãnin sãmu ɗã ga mutumin kirki shi ne dõmin ya gãji kirkin kuma ya taimaki sauran danginsa, ya rãyar da gida. Kuma wanda ba mutumin kirki ba yana yiwuwa ya sãmi ɗan kirki mai shiryar da shi zuwa ga hanyar ƙwarai.