Hausa translation of the meaning Page No 495

Quran in Hausa Language - Page no 495 495

Suratul Zukhruf from 74 to 89


74. Lalle mãsu laifi madawwama ne a cikin azãbar Jahannama.
75. Bã a sauƙaƙar da ita ( azãbar ) daga gare su, alhãli kuwa sũ,a cikinta, mãsu kãsa magana ne.
76. Kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sũ ne suka kasance azzãlumai.
77. Kuma suka yi kira, « Ya Mãliku! Ubangijinka Ya kashe mu mana ( 1 ) » ( Mãliku ) ya ce: « Lalle kũ mazauna ne. »
78. Lalle ne, haƙĩƙa, Mun jẽ muku da gaskiya, kuma amma mafi yawanku mãsu ƙi ga gaskiyar ne.
79. Kõ kuma sun tukka wani al'amari ne? To, lalle Mũ, Mãsu tukkãwa ne.
80. Ko sunã zaton lalle Mũ, bã Mu jin asĩrinsu da gãnãwarsu? Na'am! Kuma manzannin Mu na tãre da su sunã rubũtãwa.
81. Ka ce: « Idan har akwai ɗã ga Mai rahama, to, nĩ ne farkon mãsu bauta ( wa ɗan ) . »
82. Tsarkin Ubangijin sammai da ƙasa, Ubangijin Al'arshi, ya tabbata daga abin da suke sifantãwa.
83. Sabõda haka, ka ƙyãlẽ su, su kũtsa kuma su yi wãsã har su haɗu da yininsu, wanda ake yi musu wa'adi da shi.
84. Kuma Shĩ ne wanda ke abin bautãwa a sama kuma abin bautãwa a ƙasa, kuma, Shĩ ne Mai hikima, Masani.
85. Kuma albarkar wanda ke da mulkin sammai da ƙasã abin da ke a tsakãninsu tã bayyana, kuma a wurinSa ne ilmin Sa'a yake, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku.
86. Kuma waɗanda suke kira baicinSa ba su mallaki cẽto ba, fãce wanda ya yi shaida da gaskiya, kuma sũ, sunã sane ( 2 ) ( da haka ) .
87. Kuma lalle idan ka tambaye su: « Wãne ne ya halitta su? » Lalle ne zã su ce Allah ne. To, yãya ake jũyar da su?
88. Kuma da ( ilmin ) maganarSa ( Annabi ) « Ya Ubangijĩna! Lalle waɗannan mutãne ne waɗanda bã zã su yi ĩmãni ba. »
89. To, sai ka kau da kai daga gare su, kuma ka ce, « salãmã. » Sa'an nan kuma zã su sani.
( 1 ) Watau sunã nẽman su mutu su huta da ɗaukar aZãba.
( 2 ) Su waɗanda suka yi shaida da gaskiya sun san bãbu mai mallakar cẽto ga wani fãce Allah. Sabõda haka Allah nã yi musu izni su cẽci wanda Yake son su cece shi, ba wanda su suke so ba. Ma'anar iznin da cẽto ga bãyin Allah sãlihai ita ce dõmin Allah Ya bayyana darajar mai cẽton ne kawai, bã don yanã da wani hakki ba, ga Allah. Allah Ya tsarkaka daga wata halittarSa ta sãmi wani hakki a kanSa. Kõwa bãwanSa ne.