Hausa translation of the meaning Page No 521

Quran in Hausa Language - Page no 521 521

Suratul Al-Dhariyat from 7 to 30


7. Inã rantsuwa da samã ma'abũciyar hanyõyi ( na tafiyar taurãri da sautin rediyo ) .
8. Lalle kũ, haƙĩƙa, kunã cikin magana mai sãɓa wa juna ( game da Alƙur'ani ) .
9. Anã karkatar da wanda aka jũyar ( daga gaskiya ) .
10. An la'ani mãsu ƙiri- faɗi.
11. Waɗanda suke shagala a cikin zurfin jãhilci.
12. Sunã tambaya: « Yaushe ne rãnar sakamako zã ta auku? »
13. Ranar da suke a kan wuta anã fitinar su.
14. ( A ce musu ) : « Ku ɗanɗani fitinarku, wannan shĩ ne abin da kuka kasance kunã nẽman zuwansa da gaggãwa. »
15. Lalle mãsu taƙawa, sunã a cikin lambunan itãce da marẽmari.
16. Sunã mãsu dĩbar abin da Ubangijinsu Ya bã su. Lalle sũ, sun kasance mãsu kyautatãwa a gabãnin haka ( a dũniya ) .
17. Sun kasance a lõkaci kaɗan na dare suke yin barci.
18. Kuma a lõkutan asuba sunã ta yin istigfãri.
19. Kuma a cikin dũkiyarsu akwai hakki ga ( matalauci ) mai rõƙo da wanda aka hana wa rõƙo.
20. Kuma a cikin ƙasã akwai ãyõyi ga mãsu yaƙĩni.
21. Kuma a cikin rãyukanku ( akwai ãyõyi ) . To, bã zã ku dũbã ba?
22. Kuma a cikin sama arzikinku ( yake fitõwa ) da abin da ake yi muku alkawari.
23. To, kuma Ina rantsuwa da Ubangijin sama da ƙasã, lalle shĩ ( abin da ake yi muku alkawari ) , haƙĩƙa gaskiya ne, kamar abin da kuka zamo kunã karantãwa na magana,
24. Shin, lãbãrin Bãƙin Ibrãhĩm, waɗanda aka girmama, ya zo maka?
25. A lõkacin da suka shiga gare shi, sai suka yi sallama; ya ce « Aminci ya tabbata a gare ku, mutãne bãƙi! »
26. Sai ya jũya zuwa ga iyãlinsa, sa'an nan ya zo da maraƙi tutturna,
27. Sai ya kusantar da shi zuwa gare su, ya ce: « Bã zã ku ci ba? »
28. Sai ya ji tsõro daga gare su. Suka ce: « Kada kaji tsõro. » Kuma suka yi masa bushãra da ( haihuwar ) wani yaro mai ilmi.
29. Sai matarsa ta fuskanta cikin ƙyallõwa, har ta mari fuskarta kuma ta ce: « Tsõhuwa bakarãriya ( zã ta haihu ) ! »
30. Suka ce: « Kamar haka Ubangijinki Ya faɗa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai hikima, Mai ilmi. »