Hausa translation of the meaning Page No 520

Quran in Hausa Language - Page no 2 2

Suratul Qaf from 36 to 6


36. Kuma da yawa Muka halakar, a gabãninsu, ( mutãnen yanzu ) ɗaga waɗansu al'ummomi, ( waɗanda suke) sũ ne mafi ƙarfin damƙa daga gare su, sa'an nan suka yi bincike a cikin ƙasãshe: 'Kõ akwai wurin tsĩra'? ( 1 ) ( Babu ) .
37. Lalle ne, a cikin wancan, akwai tunãtarwa ga wanda zũciyarsa ta kasance gare shi, kõ kuwa ya jẽfa saurãro, alhãli kuwa yanã halarce ( da hankalinsa ) .
38. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu, a cikin kwãnaki shida, alhãli wata'yar wahala ba ta shãfe Mu ba.
39. Sabõda haka, ka yi haƙuri a kan abin da suke fadã, kuma ka yi tasĩhi ( 2 ) game da gõdẽ wa Ubangijinka ( watau ka yi salla ) a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin ɓacẽwarta.
40. Kuma daga dare, sai ka yi tasbĩhi a gare Shi da bãyan sujada.
41. Kuma ka saurãra a rãnar da mai kira ke yin kira daga wuri ( 3 ) makusanci.
42. Rãnar da suke saurãron tsãwa da gaskiya. Wancan shĩ ne yinin fita ( daga kabari ) .
43. Lalle Mũ ne haƙĩƙa, Mu ne ke rãyarwa, kuma Mũ ne ke kashẽwa, kuma zuwa gare Mu kawai ne makõmar take.
44. Rãnar da ƙasã ke tsattsãgẽwa daga gare su, sunã mãsu gaggãwa. Wancan tãrãwar mutãne ne, mai sauƙi a gare Mu.
45. Mũ ne mafi sani game da abin da suke faɗi, kuma bã zã ka zama mai tĩlasta su ba. Sabõda haka ka tunatar game da Alƙur'ani, ( 4 ) ga wanda ke tsõron ƙyacewaTa.
Sũratudh Dhariyat
Tanã karantar da gaggãwar saũkar azabar Allah ga waɗanda suka ƙi bin umurninSa ko suka sãɓa wa haninSa.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Inã rantsuwa da iskõki mãsu shẽkar abũbuwa, shẽƙẽwa.
2. Sa'an nan da girãgizai mãsu ɗaukar nauyi ( na ruwa) .
3. Sa'an nan da jirãge mãsu gudãna ( a kan ruwa ) da sauƙi.
4. Sa'an nan da Malã'iku mãsu rabon al'amari ( bisa umurnin Allah ) .
5. Lalle abin da ake yi muku alkawari ( da zuwansa ) , haƙĩƙa gaskiya ne.
6. Kuma lalle sakamako ( ga ayyukanku ) , haƙĩƙa, mai aukuwa ne
( 1 ) Sun nẽmi wurin tsĩra, ba su sãmu ba, sabõda haka kãfiran yanzu ma ba su iya samun wurin tsĩra, sai dai idan sunkõma ga Allah ta hanyar ManzonSa kawai, watau taƙawa ga Allah ke nan. Anã kãre azãbarSa da ibãdarSa kamar yadda Yake so.
( 2 ) Tasbĩhi game da gõde wa Allah a gabãnin fitar rãnã, shi ne sallar asuba, na gabãnin ɓacẽwarta, shi ne sallar Azahar da La'asar. Daga dare kuwa, shĩ ne sallar Magariba da Isha'i. Bãyan sujada, shĩ ne sallõli na nafila kuma ma'anarsa a nan tasbĩhi da tahmĩdi da kabbarõri a bãyan sallõli farillai talãtin da uku kõwace, sa'annan a cika ɗari da addu'ar da aka ruwaito a nan.
( 3 ) Mai kira shĩ ne Isrãfĩlu a cikin ƙaho a Baitil Maƙadis dõmin a nan ƙasa ta fi zama kusa da samã.
( 4 ) Wannan ya nũna ba a wa'azi da ilmin da bã daga Alƙur'ãni aka fitar da shi ba, sai fa idan bai sãɓa wa abin da ke cikin Alƙur'ani ba.