Hausa translation of the meaning Page No 528

Quran in Hausa Language - Page no 528 528

Suratul Al Najm from 45 to 6


45. Kuma lalle Shĩ ne Ya yi halitta nau'i- nau'i, namiji da mace.
46. Daga wani ɗigon ruwa guda a lõkacin da ake jẽfa shi a cikin mahaifa.
47. Kuma a kansa ne ƙãga halitta ta biyu take.
48. Kuma lalle, Shĩ , Shĩ ne Ya azurta, kuma Ya wadãtar.
49. Kuma lalle, Shĩ, Shi ne Ubangijin Shi'ira ( 1 ) .
50. Kuma lalle, Shĩ , Shĩ ne Ya halaka Ãdãwa na farko.
51. Da Samũdãwa, sa'an nan bai rage su ba.
52. Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sũ sun kasance mafi zãlunci kuma mafi girman kai.
53. Da waɗanda aka birkice ( 2 ) ƙasarsu, Ya kãyar da su.
54. Sa'an nan abin da ya rufe su, ya rufe su.
55. To, da wace daga ni'imõmin Ubangijinka kake ( 3 ) yin shakka?
56. wannan ( Muhammadu ) mai gargaɗi ne kamar irin mãsu gargaɗi na farko.
57. Makusanciya ( 4 ) fa, tã yi kusa.
58. Bãbu wani rai, banda Allah, mai iya bãyani gare ta.
59. Shin, kuma daga wannan ( 5 ) lãbãri kuke mãmãki?
60. Kuma kunã yin dãriya, kuma bã ku yin kũka?
61. Alhãli kunã mãsu wãsã?
62. To, ku yi tawãli'u ( 6 ) ga Allah, kuma ku bauta ( masa ) .
Sũratul Ƙamar
Tanã karantar da cẽwa wanda ya nẽmi wata mu’ujiza, to, ita za ta zama sababin halakarsa.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Sã'a ta yi kusa, kuma wata ( 7 ) ya tsãge.
2. Kuma idan sun ga wata ãyã, sai su juya baya su ce: « Sihiri ne mai dõgẽwa! »
3. Kuma suka ƙaryata, kuma suka bi son zũciyarsu, alhãli kuwa kõwane al'amari ( wanda suke son su tũre daga Annabi ) an tabbatar da shi.
4. Kuma lalle, abin da yake akwai tsãwatarwa a cikinsa na lãbãraiya zo musu.
5. Hikima cikakka! Sai dai abũbuwan gargaɗi bã su amfãni.
6. Sabõda haka, ka bar su! Rãnar da mai kiran zai yi kira zuwa ga wani abu abin ƙyama.
( 1 ) Sũnan wasu taurãri biyu ne sunã fita a bãyan taurarin Jauza'a sunã tafiya daga kudu zuwa arẽwa karkace. Kabĩlar Lãrabãwa ta Khuza'a na bauta musu da umurnin Abu Kabshah, ɗaya daga cikin kãkannin Annabi na wajen uwa dõmin haka ne Ƙuraishãwa ke ce wa Annabi Ibn abĩ Kabshah, wanda ya ƙãga sãbon addinĩn da ya sãɓa wa na ubanninsa.
( 2 ) Mutãnen Lũɗu da aka birkice ƙasarsu da su.
( 3 ) Kamar abõkin magana kõ mai karãtu.
( 4 ) Makusanciya ita ce Ƙiyãma.
( 5 ) Al'ƙur'ãni.
( 6 ) Anã yin sujadar karatu a nan, amma bã ta a cikin sujadai na tĩlas.
( 7 ) Ƙuraishãwa suka nẽmi Annabi ya yi addu'a dõmin wata ya tsãge wani ɓalgace nãsa ya fãɗo a ƙasã; ya yi addu'ar, watã ya tsãge, wani abu daga gare shi ya fãɗo kamar yadda suka nẽma.