Surah Al-Ma'arij | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 568
Suratul Al-Haqqah from 35 to 10
35. « Sabõda haka, a yau, a nan, bã ya da masõyi. »
36. « Kuma bãbu wani abinci, sai daga ( itãcen ) gislĩn. »
37. « Bãbu mai cin sa sai mãsu ganganci. »
38. To, ba sai Nã yi rantsuwa da abin da kuke iya gani ba,
39. Da abin da bã ku iya gani.
40. Lalle ne, shi ( Alƙur'ani ) tabbas maganar wani manzo ( Jibirilu ) mai daraja ne.
41. Kuma shi ba maganar wani mawãƙi ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku gaskata.
42. Kuma bã maganar bõka ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku iya tunãwa.
43. Abin saukarwã ne daga Ubangijin halitta duka.
44. Kuma dã ( Muhammadu ) yã faɗi wata maganã, yã jingina ta garẽ Mu.
45. Dã Mun kãma shi da dãma.
46. sa'an nan, lalle ne, dã Mun kãtse masa lakã.
47. Kuma daga cikinku bãbu wasu mãsu iya kãre ( azãbarMu ) daga gare shi.
48. Kuma lalle ne shi ( Alƙur'ãni ) tanãtarwa ce ga mãsu taƙawa.
49. Kuma lalle, ne Mũ, wallahi Munã sane da cẽwa daga cikinku alwwai mãsu ƙaryatãwa.
50. Kuma lalle ne shi ( Alƙarãni ) wallahi baƙin ciki ne ga kãfirai.
51. Kuma lalle, ne shi gaskiya ce ta yaƙshẽni.
52. Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangjinka, mai girma.
Sũratul Ma‘ãrij
Tana bayãnin saukar azãba ga kãfirai, bãbu makawa, kuma tana bayanin cũtar rai da maganin cutar.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Wani mai tambaya yã yi tambaya game da azãba, mai aukuwa.
2. Ga kãfirai, bã ta da mai tunkuɗẽwa.
3. Daga Allah Mai matãkala.
4. Malã'iku da Ruhi ( Jibrila ) sunã tãkãwa zuwa gare Shi, a cikin yini wanda gwargwadonsa, shẽkara dubu hamsin ne.
5. Sabõda haka, ka yi haƙuri, haƙuri mai kyãwo.
6. Lalle ne su, sunã ganin ta mai nĩsa.
7. Kuma Mu, Muna ganin ta a kusa.
8. Rãnar da sama zã ta kasance kamar narkakkar azurfa.
9. Kuma duwãtsu su zama kamar saɓin sũfi.
10. Kuma abõki bã ya tambayar inda wani abõki yake.