Hausa translation of the meaning Page No 519

Quran in Hausa Language - Page no 519 519

Suratul Qaf from 16 to 35


16. Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta mutum kuma Mun san abin da ransa ke yin waswãsi da shi, kuma Mũ ne mafi kusanta zuwa gare shi daga lakar jannayẽnsa.
17. A lõkacin da mãsu haɗuwa biyu suke haɗuwa daga dãma, kuma daga hagu akwai wani ( malã'ika ) zaunanne.
18. Bã ya lafazi da wata magana fãce a lĩƙe da shi akwai mai tsaro halartacce.
19. Kuma mãyen mutuwa ya jẽ da gaskiya. Wannan shĩ ne abin da ka kasance daga gare shi kanã bijirẽwa.
20. Kuma aka hũra a cikin ƙaho. Wancan yinin ƙyacẽwar ne fa.
21. Kuma kõwane rai ya zo, tãre da shi akwai mai kõra da mai shaida.
22. ( Sai a ce masa ) : « Lalle ne, haƙĩƙa, ka kasance a cikin gafala daga wannan. To, Mun kuranye maka rufinka, sabõda haka ganinka a yau, mai kaifi ne. »
23. Kuma abõkin haɗinsa ( 1 ) ya ce: « Wannan shi ne abin da ke tãre da ni halarce. »
24. ( A ce wa Malã'iku ) , « Ku jẽfa, a cikin Jahannama, dukan mai yawan kãfirci, mai tsaurin rai. »
25. « Mai yawan hanãwa ga alhẽri, mai zãlunci, mai shakka. »
26. « Wanda ya sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, sabõda haka kujẽfa shi a cikin azãba mai tsanani. »
27. Abõkin haɗinsa ( 2 ) ya ce: « Ya Ubangijinmu! Ban sanya shi girman kai ba, kuma amma ya kasance a cikin ɓata mai nĩsa. »
28. Ya ce: « Kada ku yi husũma a wuriNa, alhãli Na gabãtar da ƙyacewa zuwa gare ku. »
29. « Ba a musanya magana a wuriNa, Kuma Ban zama Mai zãlunci ba ga bãyiNa. »
30. Rãnar da Muke cẽwa ga Jahannama « Shin, kin cika? » Kuma ta ce: « Ashe, ( 3 ) akwai wani ƙãri? »
31. Kuma a kusantar dã Aljanna ga mãsu taƙawa, ba da nĩsa ba.
32. « Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa'adi da shi ga dukan mai yawan kõmawa ga Allah, mai tsarewar ( umurninSa ) . »
33. « Wanda ya ji tsõron Mai rahama a fake, ( 4 ) kuma ya zo da wata irin zũciya mai tawakkali. »
34. ( A ce musu ) « Ku shige ta da aminci, ( 5 ) waccan ita ce rãnar dawwama. »
35. Sunã da abin da suke so a cikinta, kuma tãre da Mũ akwai ƙãrin ni'ima,
( 1 ) Malã'ika mai rubũtun aikinsa. Bã ya rabuwa da shi sai a hãlãye uku, wurin jimã'i da salga da wanka. Malã'ikan da aka haɗa shi da shi dõmin ya rubũta ayyukansa.
( 2 ) Shaiɗanin da ke tãre dashi. A cikin hadĩsi an ruwaito cẽwa kõwa yana da Shaiɗani tãre da shi, sai dai idan ya rinjãye shi, da abin da Allah Ya aza masa, ko kuma shi sai shaiɗãnin ya rinjãye shi da bin son zũciyarsa.
( 3 ) Wannan jawãbi na Jahannama yanã ɗaukar ma'anõni biyu. Ta farko tanã nũna ta cika ƙwarai, amma tanã kũkan a ƙara mata wani abu a cikinta. Wannan fassara ta yi daidai da ayãr da ta ce, « Lalle na cika Jahannama daga aljannu da mutãne gabã ɗaya. » Sura ta 32, ãyã ta 13. Fassara ta biyu, ita ce Jahannama nã nẽman ƙãri tanã hushi sabõda mãsu sãɓa wa umurnin Allah. Sũra ta 67 ãyõyi 6, 7 da 8.
( 4 ) Tsoron Allah a fake, shĩ ne a bauta masa, bã da riya ba, ɓayyane da ɓõye duka ɗaya.
( 5 ) Kõ kuma ku shiga da sallama.