La sourate Az-Zalzalah en Haoussa
إِذَا زُلْزِلَتِ الْأَرْضُ زِلْزَالَهَا(1) Idan aka girgiza ƙasa, girgizawarta. |
وَأَخْرَجَتِ الْأَرْضُ أَثْقَالَهَا(2) Kuma ƙasa ta fitar da kayanta, masu nauyi. |
وَقَالَ الْإِنسَانُ مَا لَهَا(3) Kuma mutum ya ce "Mẽ neya same ta?" |
يَوْمَئِذٍ تُحَدِّثُ أَخْبَارَهَا(4) A rãnar nan, zã ta faɗi lãbãrinta. |
بِأَنَّ رَبَّكَ أَوْحَىٰ لَهَا(5) cewa Ubangijinka Ya yi umurni zuwa gare ta. |
يَوْمَئِذٍ يَصْدُرُ النَّاسُ أَشْتَاتًا لِّيُرَوْا أَعْمَالَهُمْ(6) A rãnar nan mutane za su fito dabam-dabam domin a nuna musu ayyukansu. |
فَمَن يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ خَيْرًا يَرَهُ(7) To, wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai gan shi. |
وَمَن يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ شَرًّا يَرَهُ(8) Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi. |
Plus de sourates en Haoussa :
Téléchargez la sourate avec la voix des récitants du Coran les plus célèbres :
Téléchargez le fichier mp3 de la sourate Az-Zalzalah : choisissez le récitateur pour écouter et télécharger la sourate Az-Zalzalah complète en haute qualité.















Donnez-nous une invitation valide