La sourate Al-Qariah en Haoussa
الْقَارِعَةُ(1) Mai ƙwanƙwasar (zukata da tsõro)! |
مَا الْقَارِعَةُ(2) Mẽnẽ ne mai ƙwanƙwasa? |
وَمَا أَدْرَاكَ مَا الْقَارِعَةُ(3) Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa mai ƙwanƙwasa? |
يَوْمَ يَكُونُ النَّاسُ كَالْفَرَاشِ الْمَبْثُوثِ(4) Rãnar da mutãne za su kasance kamar 'ya'yan fari mãsu wãtsuwa. |
وَتَكُونُ الْجِبَالُ كَالْعِهْنِ الْمَنفُوشِ(5) Kuma duwãtsu su kasance kamar gãshin sũfin da aka saɓe. |
فَأَمَّا مَن ثَقُلَتْ مَوَازِينُهُ(6) To, amma wanda ma'aunansa suka yi nauyi. |
فَهُوَ فِي عِيشَةٍ رَّاضِيَةٍ(7) To, shi yana a cikin wata rayuwa yardadda. |
وَأَمَّا مَنْ خَفَّتْ مَوَازِينُهُ(8) Kuma amma wanda ma'aunansa suka yi sauƙi (bãbu nauyi). |
فَأُمُّهُ هَاوِيَةٌ(9) To, uwarsa Hãwiya ce. |
وَمَا أَدْرَاكَ مَا هِيَهْ(10) Kuma me ya sanar da kai mece ce ita? |
نَارٌ حَامِيَةٌ(11) Wata wuta ce mai zafi. |
Plus de sourates en Haoussa :
Téléchargez la sourate avec la voix des récitants du Coran les plus célèbres :
Téléchargez le fichier mp3 de la sourate Al-Qariah : choisissez le récitateur pour écouter et télécharger la sourate Al-Qariah complète en haute qualité.















Donnez-nous une invitation valide