La sourate Al-Adiyat en Haoussa
وَالْعَادِيَاتِ ضَبْحًا(1) Ina rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki. |
فَالْمُورِيَاتِ قَدْحًا(2) Mãsu ƙyasta wuta (da kõfatansu a kan duwatsu) ƙyastawa. |
فَالْمُغِيرَاتِ صُبْحًا(3) Sa'an nan mãsu yin hari a lokacin asuba. |
فَأَثَرْنَ بِهِ نَقْعًا(4) Sai su motsar da ƙũra game da shi. |
فَوَسَطْنَ بِهِ جَمْعًا(5) Sai su shiga, game da ita (ƙũrar), a tsakãnin jama'ar maƙiya. |
إِنَّ الْإِنسَانَ لِرَبِّهِ لَكَنُودٌ(6) Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa. |
وَإِنَّهُ عَلَىٰ ذَٰلِكَ لَشَهِيدٌ(7) Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa dl haka. |
وَإِنَّهُ لِحُبِّ الْخَيْرِ لَشَدِيدٌ(8) Kuma 1alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne. |
۞ أَفَلَا يَعْلَمُ إِذَا بُعْثِرَ مَا فِي الْقُبُورِ(9) Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura. |
وَحُصِّلَ مَا فِي الصُّدُورِ(10) Aka bayyana abin da ke cikin zukata. |
إِنَّ رَبَّهُم بِهِمْ يَوْمَئِذٍ لَّخَبِيرٌ(11) Lalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne? |
Plus de sourates en Haoussa :
Téléchargez la sourate avec la voix des récitants du Coran les plus célèbres :
Téléchargez le fichier mp3 de la sourate Al-Adiyat : choisissez le récitateur pour écouter et télécharger la sourate Al-Adiyat complète en haute qualité.















Donnez-nous une invitation valide