La sourate Ad-Dhuha en Haoussa
وَالضُّحَىٰ(1) Inã rantsuwa da hantsi. |
وَاللَّيْلِ إِذَا سَجَىٰ(2) Da dare a lõkacin da ya rufe (da duhunsa). |
مَا وَدَّعَكَ رَبُّكَ وَمَا قَلَىٰ(3) Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙĩ kaba. |
وَلَلْآخِرَةُ خَيْرٌ لَّكَ مِنَ الْأُولَىٰ(4) Kuma lalle ta ƙarshe ce mafi alheri a gare ka daga ta farko. |
وَلَسَوْفَ يُعْطِيكَ رَبُّكَ فَتَرْضَىٰ(5) Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta bã ka kyauta sai ka yarda. |
أَلَمْ يَجِدْكَ يَتِيمًا فَآوَىٰ(6) Ashe, bai sãme ka marãya ba, sa'an nan Ya yi maka makõma? |
وَوَجَدَكَ ضَالًّا فَهَدَىٰ(7) Kuma Ya sãme ka bã ka da shari'ã, sai Ya shiryar da kai? |
وَوَجَدَكَ عَائِلًا فَأَغْنَىٰ(8) Kuma Ya sãme ka matalauci, sai Ya wadãtã ka? |
فَأَمَّا الْيَتِيمَ فَلَا تَقْهَرْ(9) Sabõda haka, amma marãya, to, kada ka rinjãye shi. |
وَأَمَّا السَّائِلَ فَلَا تَنْهَرْ(10) Kuma amma mai tambaya, kada ka yi masa tsãwa. |
وَأَمَّا بِنِعْمَةِ رَبِّكَ فَحَدِّثْ(11) Kuma amma ni'imar Ubangijinka, sai ka faɗa (dõmin gõdiya). |
Plus de sourates en Haoussa :
Téléchargez la sourate avec la voix des récitants du Coran les plus célèbres :
Téléchargez le fichier mp3 de la sourate Ad-Dhuha : choisissez le récitateur pour écouter et télécharger la sourate Ad-Dhuha complète en haute qualité.















Donnez-nous une invitation valide