لَا أُقْسِمُ بِيَوْمِ الْقِيَامَةِ(1) Bã sai Nã yi rantsuwa da Rãnar ¡iyãma ba. |
وَلَا أُقْسِمُ بِالنَّفْسِ اللَّوَّامَةِ(2) Bã sai Nã yi rantsuwa da rai mai yawan zargin kansa ba. |
أَيَحْسَبُ الْإِنسَانُ أَلَّن نَّجْمَعَ عِظَامَهُ(3) Sin, mutum yana zaton cẽwa bã zã Mu tãra ƙasusuwansa ba? |
بَلَىٰ قَادِرِينَ عَلَىٰ أَن نُّسَوِّيَ بَنَانَهُ(4) Na'am! Mãsu ĩkon yi Muke a kan Mu daidaita gaɓõɓin yãtsunsa. |
بَلْ يُرِيدُ الْإِنسَانُ لِيَفْجُرَ أَمَامَهُ(5) Ba haka ba! Mutum so yake, ya yi fãjirci, ya ƙaryata abin da yake a gabansa. |
يَسْأَلُ أَيَّانَ يَوْمُ الْقِيَامَةِ(6) Yanã tambaya: "Yaushe ne Rãnar ¡iyãma?" |
فَإِذَا بَرِقَ الْبَصَرُ(7) To, idan gani ya ɗimauta (ya yi ƙyalli). |
وَخَسَفَ الْقَمَرُ(8) Kuma, watã ya yi husũfi (haskensa ya dushe). |
وَجُمِعَ الشَّمْسُ وَالْقَمَرُ(9) Aka tãra rãnã da watã |
يَقُولُ الْإِنسَانُ يَوْمَئِذٍ أَيْنَ الْمَفَرُّ(10) Mutum zai ce a rãn nan "Ina wurin gudu?" |
كَلَّا لَا وَزَرَ(11) A'aha! bãbu mafaka. |
إِلَىٰ رَبِّكَ يَوْمَئِذٍ الْمُسْتَقَرُّ(12) zuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a rãnar nan, yake. |
يُنَبَّأُ الْإِنسَانُ يَوْمَئِذٍ بِمَا قَدَّمَ وَأَخَّرَ(13) Ana gayã wa mutum, a rãnar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar. |
بَلِ الْإِنسَانُ عَلَىٰ نَفْسِهِ بَصِيرَةٌ(14) Ba haka ba! Mutum, ga abin da ya shafi kansa, masani ne. |
وَلَوْ أَلْقَىٰ مَعَاذِيرَهُ(15) Kuma ko da yã jẽfa uzurorinsa (bã zã a saurãre shi ba). |
لَا تُحَرِّكْ بِهِ لِسَانَكَ لِتَعْجَلَ بِهِ(16) Kada ka mõtsar da harshenka game da shi dõmin ka yi gaugãwar riƙe shi (Alƙur'ãni). |
إِنَّ عَلَيْنَا جَمْعَهُ وَقُرْآنَهُ(17) Lalle ne, wãjibi ne a gare Mu, Mu tãra shi. Mu (tsare maka) karãtunsa. |
فَإِذَا قَرَأْنَاهُ فَاتَّبِعْ قُرْآنَهُ(18) To idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa. |
ثُمَّ إِنَّ عَلَيْنَا بَيَانَهُ(19) sa'an nan, lalle wãjibi ne a gare Mu, bayãninsa. |
كَلَّا بَلْ تُحِبُّونَ الْعَاجِلَةَ(20) A'aha! Bã haka ba kunã son mai gaugawar nan (duniya) ne. |
وَتَذَرُونَ الْآخِرَةَ(21) Kunã barin ta ƙarshen (Lãhira). |
وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ نَّاضِرَةٌ(22) Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu annuri ne. |
إِلَىٰ رَبِّهَا نَاظِرَةٌ(23) Zuwa ga Ubangijinsu mãsu kallo ne. |
وَوُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ بَاسِرَةٌ(24) Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu gintsẽwa ne. |
تَظُنُّ أَن يُفْعَلَ بِهَا فَاقِرَةٌ(25) Sunã zaton a sako musu masĩfa mai karya tsatso. |
كَلَّا إِذَا بَلَغَتِ التَّرَاقِيَ(26) A'aha! Iadan (rai) ya kai ga karankarmai. |
وَقِيلَ مَنْ ۜ رَاقٍ(27) kuma aka ce: "Wãne ne mai tawada?" |
وَظَنَّ أَنَّهُ الْفِرَاقُ(28) Kuma ya tabbata cẽwa rabuwa dai ce. |
وَالْتَفَّتِ السَّاقُ بِالسَّاقِ(29) Kuma ƙwabri ya lauye da wani ƙwabri. |
إِلَىٰ رَبِّكَ يَوْمَئِذٍ الْمَسَاقُ(30) Zuwa ga Ubangijinka, a rãnar nan, magargaɗa take. |
فَلَا صَدَّقَ وَلَا صَلَّىٰ(31) To, bai gaskatã ba, kuma bai yi salla ba! |
وَلَٰكِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ(32) Amma dai ya ƙaryata, kuma ya jũya baya! |
ثُمَّ ذَهَبَ إِلَىٰ أَهْلِهِ يَتَمَطَّىٰ(33) Sa'an nan, ya tafi zuwa ga mutãnensa, yana tãƙama. |
أَوْلَىٰ لَكَ فَأَوْلَىٰ(34) Halaka tã tabbata a gare ka, sa'an nan ita ce mafi dãcewa. |
ثُمَّ أَوْلَىٰ لَكَ فَأَوْلَىٰ(35) Sa'an nan, wata halaka tã tabbata a gare ka dõmin tã fi dãce wa. |
أَيَحْسَبُ الْإِنسَانُ أَن يُتْرَكَ سُدًى(36) Shin, mutum nã zaton a bar shi sagaga (wãto bãbu nufin kõme game da shi)? |
أَلَمْ يَكُ نُطْفَةً مِّن مَّنِيٍّ يُمْنَىٰ(37) Bai kasance iɗgo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa (a cikin mahaifa) |
ثُمَّ كَانَ عَلَقَةً فَخَلَقَ فَسَوَّىٰ(38) Sa'an nan, ya zama gudan jini, sa'an nan Allah Ya halitta shi, sa'an nan Ya daidaita gaɓõɓinsa; |
فَجَعَلَ مِنْهُ الزَّوْجَيْنِ الذَّكَرَ وَالْأُنثَىٰ(39) Sa'an nan, Ya sanya daga gare shi, nau'i biyu: namiji damace? |
أَلَيْسَ ذَٰلِكَ بِقَادِرٍ عَلَىٰ أَن يُحْيِيَ الْمَوْتَىٰ(40) Ashẽ wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rãyar da matattu? |