6 Aya · Meccan · Hausa
bismillah
ﮀﮁﮂﮃﮄ
114:1 Ka ce "Ina nẽman tsari ga Ubangijin mutãne."
ﮅﮆﮇ
114:2 "Mamallakin mutane."
ﮈﮉﮊ
114:3 "Abin bautãwar mutãne."
ﮋﮌﮍﮎﮏ
114:4 "Daga sharrin mai sanya wasuwãsi, mai ɓoyewa."
ﮐﮑﮒﮓﮔﮕ
114:5 "Wanda ke sanya wasuwãsi a cikin ƙirãzan mutane."
ﮖﮗﮘﮙ
114:6 "Daga aljannu da mutane."

Al-Kur'ani


Wednesday, September 9, 2026

Don't forget us in your sincere prayers