PDF —
52 Aya Meccan PDF
Built right in your browser — download starts automatically

Surah Al-Haqqah pdf — Sauke (Hausa)

Surah Al-Haqqah pdf Hausa — Sauke Surah Al-Haqqah Fassara. Surah Al-Haqqah (Meccan) 52 Aya.



52 Aya · Meccan · Hausa
bismillah
ﮯﮰ
69:1 Kiran gaskiya!
ﮱﯓﯔ
69:2 Mẽne ne kiran gaskiya?
ﯕﯖﯗﯘﯙ
69:3 Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽwa kiran gaskiya?
ﯚﯛﯜﯝﯞ
69:4 Samũdãwa da Ãdãwa sun ƙaryatar da kiran gaskiya mai dũkar zũciya!
ﯟﯠﯡﯢﯣ
69:5 To, amma Samũdãwa to, an halakãsu da tsãwa mai tsanani.
ﯤﯥﯦﯧﯨﯩﯪ
69:6 Kuma amma Ãdãwa to, an halaka su da wata iska mai tsananin sauti wadda ta ƙẽtare haddi.
ﯫﯬﯭﯮﯯﯰﯱﯲﯳﯴﯵﯶﯷﯸﯹﯺﯻ
69:7 (Allah) Ya hõre ta a kansu a cikin dare bakwai da yini takwas, biye da jũna, sabõda haka, kana ganin mutãne a cikinta kwance. Kamar sũ ƙirãruwan dabĩno ne, waɗanda suka fãɗi.
ﯼﯽﯾﯿﰀﰁ
69:8 To, kõ kanã ganin abin da ya yi saurã daga cikinsu?
ﭑﭒﭓﭔﭕﭖﭗ
69:9 Kuma Fir'auna yã zo da waɗanda ke gabãninsa, da waɗannan da aka kife ƙasarsu, sabõda laifi.
ﭘﭙﭚﭛﭜﭝﭞ
69:10 Dõmin sun sãɓã wa manzon Ubangijinsu, sabõda haka ya kãmã su da wani irin kãmu mai ƙãruwar (tsanani).
ﭟﭠﭡﭢﭣﭤﭥﭦ
69:11 Lalle ne, Mũ, a lõkacin da ruwa ya ƙẽtare haddi, Munɗauke aaku a cikin jirgin ruwan nan.
ﭧﭨﭩﭪﭫﭬﭭ
69:12 Dõmin Mu sanya shi, gare ku abin tunãwa kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye (shi).
ﭮﭯﭰﭱﭲﭳﭴ
69:13 To, idan an yi bũsa a cikin ƙaho, bũsa ɗaya.
ﭵﭶﭷﭸﭹﭺﭻ
69:14 Kuma aka ɗauki ƙasa da duwãtsu, kuma aka niƙa su niƙãwa ɗaya.
ﭼﭽﭾﭿ
69:15 A ran nan, mai aukuwa zã ta auku.
ﮀﮁﮂﮃﮄﮅ
69:16 Kuma sama zã ta tsãge, dõmin ita a ran nan, mai rauni ce.
ﮆﮇﮈﮉﮊﮋﮌﮍﮎﮏﮐ
69:17 Kuma malã'iku (su bayyana) a kan sãsanninta, kuma wasu (malã'iku) takwas na ɗauke da Al'arshin Ubangijinka, a sama da su, a wannan rãnar.
ﮑﮒﮓﮔﮕﮖﮗ
69:18 A rãnar nan zã a bijirã ku (dõmin hisãbi), bãbu wani rai, mai ɓoyewa, daga cikinku, wanda zai iya ɓõyẽwa.
ﮘﮙﮚﮛﮜﮝﮞﮟﮠﮡ
69:19 To, amma wanda aka bai wa littãfinsa a dãmansa, sai ya ce wa (makusantansa), "Ku karɓa, ku karanta littafina."
ﮢﮣﮤﮥﮦﮧ
69:20 "Lalle ne ni, nã tabbata cewa ni mai haɗuwa da hisãbina ne."
ﮨﮩﮪﮫﮬ
69:21 Sabõda haka, shi yana cikin wata rãyuwa yardadda.
ﮭﮮﮯﮰ
69:22 A cikin Aljanna maɗaukakiya.
ﮱﯓﯔ
69:23 Nunannun 'yã'yan itãcenta makusantã ne (ga mai son ɗĩba),
ﯕﯖﯗﯘﯙﯚﯛﯜﯝ
69:24 (Ana ce musu) "Ku ci, kuma ku sha a cikin ni'ima, sabõda abin da kuka gabãtar a cikin kwãnukan da suka shige."
ﯞﯟﯠﯡﯢﯣﯤﯥﯦﯧﯨ
69:25 Kuma wanda aka bai wa littãfinsa ga hagunsa, sai ya ce: "Kaitona, ba a kãwo mini littãfina ba!"
ﯩﯪﯫﯬﯭ
69:26 "Kuma ban san abin da (ke sakamakon) hisãbina ba!"
ﯮﯯﯰﯱ
69:27 "In dã dai ita, tã kasance mai halakã ni gabã ɗaya ce!
ﯲﯳﯴﯵﯶﯷ
69:28 "Dukiyãta ba ta wadatar da ni ba!"
ﯸﯹﯺﯻ
69:29 "Ĩkona ya ɓace mini!"
ﯼﯽﯾ
69:30 (Sai a ce wa malã'iku) "Ku kãmã shi, sa'an nan ku sanyã shi a cikin ƙuƙumi."
ﯿﰀﰁﰂ
69:31 "Sa'an nan, a cikin Jahĩm, ku ƙõna shi."
ﰃﰄﰅﰆﰇﰈﰉﰊ
69:32 "Sa'an nan, acikin sarƙa, tsawonta zirã'i saba'in, sai ku sanya shi."
ﰋﰌﰍﰎﰏﰐﰑ
69:33 "Lalle ne, shi ya kasance ba ya yin ĩmãni da Allah, Mai girma!"
ﰒﰓﰔﰕﰖﰗ
69:34 "Kuma ba ya kwaɗaitarwa ga (bãyar da) abincin matalauci!"
ﰘﰙﰚﰛﰜﰝ
69:35 "Sabõda haka, a yau, a nan, bã ya da masõyi."
ﭑﭒﭓﭔﭕﭖ
69:36 "Kuma bãbu wani abinci, sai daga (itãcen) gislĩn."
ﭗﭘﭙﭚﭛ
69:37 "Bãbu mai cin sa sai mãsu ganganci."
ﭜﭝﭞﭟﭠ
69:38 To, ba sai Nã yi rantsuwa da abin da kuke iya gani ba,
ﭡﭢﭣﭤ
69:39 Da abin da bã ku iya gani.
ﭥﭦﭧﭨﭩ
69:40 Lalle ne, shi (Alƙur'ani) tabbas maganar wani manzo (Jibirilu) mai daraja ne.
ﭪﭫﭬﭭﭮﭯﭰﭱﭲ
69:41 Kuma shi ba maganar wani mawãƙi ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku gaskata.
ﭳﭴﭵﭶﭷﭸﭹﭺ
69:42 Kuma bã maganar bõka ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku iya tunãwa.
ﭻﭼﭽﭾﭿ
69:43 Abin saukarwã ne daga Ubangijin halitta duka.
ﮀﮁﮂﮃﮄﮅ
69:44 Kuma dã (Muhammadu) yã faɗi wata maganã, yã jingina ta garẽ Mu.
ﮆﮇﮈﮉ
69:45 Dã Mun kãma shi da dãma.
ﮊﮋﮌﮍﮎ
69:46 sa'an nan, lalle ne, dã Mun kãtse masa lakã.
ﮏﮐﮑﮒﮓﮔﮕ
69:47 Kuma daga cikinku bãbu wasu mãsu iya kãre (azãbarMu) daga gare shi.
ﮖﮗﮘﮙ
69:48 Kuma lalle ne shi (Alƙur'ãni) tanãtarwa ce ga mãsu taƙawa.
ﮚﮛﮜﮝﮞﮟ
69:49 Kuma lalle, ne Mũ, wallahi Munã sane da cẽwa daga cikinku alwwai mãsu ƙaryatãwa.
ﮠﮡﮢﮣﮤ
69:50 Kuma lalle ne shi (Alƙarãni) wallahi baƙin ciki ne ga kãfirai.
ﮥﮦﮧﮨ
69:51 Kuma lalle, ne shi gaskiya ce ta yaƙshẽni.
ﮩﮪﮫﮬﮭ
69:52 Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangjinka, mai girma.

Al-Kur'ani


Wednesday, September 9, 2026

Don't forget us in your sincere prayers