PDF —
26 Aya Meccan PDF
Built right in your browser — download starts automatically

Surah Al-Ghashiyah pdf — Sauke (Hausa)

Surah Al-Ghashiyah pdf Hausa — Sauke Surah Al-Ghashiyah Fassara. Surah Al-Ghashiyah (Meccan) 26 Aya.

← Al-A'laSurah Al-Ghashiyah Al-Fajr →


26 Aya · Meccan · Hausa
bismillah
ﭽﭾﭿﮀﮁ
88:1 Lalle ne labãrin (¡iyãma) mai rufe mutãne da tsoronta yã zo maka?
ﮂﮃﮄﮅ
88:2 Wasu huskõki a rãnar nan ƙasƙantattu ne.
ﮆﮇﮈ
88:3 Mãsu aikin wahala ne, mãsu gajiya.
ﮉﮊﮋﮌ
88:4 Zã su shiga wata wuta mai zãfi.
ﮍﮎﮏﮐﮑ
88:5 Ana shãyar da su daga wani marmaro mai zãfin ruwa.
ﮒﮓﮔﮕﮖﮗﮘ
88:6 Ba su da wani abinci fãce dai daga danyi.
ﮙﮚﮛﮜﮝﮞﮟ
88:7 Bã ya sanya ƙiba, kuma bã zai wadãtar daga yunwa ba.
ﮠﮡﮢﮣ
88:8 Wasu huskõki a rãnar nan mãsu ni'ima ne.
ﮤﮥﮦ
88:9 Game da aikinsu, masu yarda ne.
ﮧﮨﮩﮪ
88:10 (Suna) a cikin Aljanna maɗaukakiya.
ﮫﮬﮭﮮﮯ
88:11 Bã zã su ji yãsassar magana ba, a cikinta.
ﮰﮱﯓﯔ
88:12 A cikinta akwai marmaro mai gudãna.
ﯕﯖﯗﯘ
88:13 A cikinta akwai gadãje maɗaukaka.
ﯙﯚﯛ
88:14 Da kõfuna ar'aje.
ﯜﯝﯞ
88:15 Da filõli jẽre,
ﯟﯠﯡ
88:16 Da katifu shimfiɗe.
ﯢﯣﯤﯥﯦﯧﯨ
88:17 Ashe to bã zã su dũbãwa ba ga rãƙumã yadda aka halitta su?
ﯩﯪﯫﯬﯭ
88:18 Da zuwa ga sama yadda aka ɗaukaka ta?
ﯮﯯﯰﯱﯲ
88:19 Da zuwa ga duwãtsu yadda aka kafa su?
ﯳﯴﯵﯶﯷ
88:20 Da zuwa ga ƙasa yadda aka shimfiɗã ta?
ﯸﯹﯺﯻﯼ
88:21 sabõda haka, ka yi wa'azi, kai mai yin wa'azi ne kawai.
ﯽﯾﯿﰀ
88:22 Ba ka zama mai ĩkon tanƙwasãwa a kansu ba.
ﭑﭒﭓﭔﭕ
88:23 Fãce dai duk wanda ya jũya bãya, kuma ya kãfirta.
ﭖﭗﭘﭙﭚ
88:24 To, Allah zai yi masa azãba, azãbar nan da take mafi girma.
ﭛﭜﭝﭞ
88:25 Lalle ne, zuwa gare Mu kõmõwarsu take.
ﭟﭠﭡﭢﭣ
88:26 Sa'an nan lalle ne aikinMu ne Mu yi musu hisãbi.

Al-Kur'ani


Wednesday, September 9, 2026

Don't forget us in your sincere prayers