PDF —
78 Aya Medinan PDF
Built right in your browser — download starts automatically

Surah Ar-Rahman pdf — Sauke (Hausa)

Surah Ar-Rahman pdf Hausa — Sauke Surah Ar-Rahman Fassara. Surah Ar-Rahman (Medinan) 78 Aya.



78 Aya · Medinan · Hausa
bismillah
ﭷﭸ
55:1 (Allah) Mai rahama.
ﭹﭺﭻ
55:2 Yã sanar da Alƙur'ani.
ﭼﭽﭾ
55:3 Yã halitta mutum.
ﭿﮀﮁ
55:4 Yã sanar da shi bayãni (magana).
ﮂﮃﮄﮅ
55:5 Rãnã da watã a kan lissãfi suke.
ﮆﮇﮈﮉ
55:6 Kuma tsirrai mãsu yãɗo da itãce sunã tawãlu'i.
ﮊﮋﮌﮍﮎ
55:7 Kuma samã Ya ɗaukaka ta, Kuma Yã aza sikẽli.
ﮏﮐﮑﮒﮓ
55:8 Dõmin kada ku karkatar da sikẽlin.
ﮔﮕﮖﮗﮘﮙﮚ
55:9 Kuma ku daidaita awo da ãdalci, kuma kada ku rage sikẽlin.
ﮛﮜﮝﮞ
55:10 Kuma ƙasã Yã aza ta dõmin tãlikai.
ﮟﮠﮡﮢﮣﮤ
55:11 A cikinta akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno mai kwasfa.
ﮥﮦﮧﮨﮩ
55:12 Da ƙwãya mai sõshiya da ƙamshi.
ﮪﮫﮬﮭﮮ
55:13 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangjinku kuke ƙaryatãwa?
ﮯﮰﮱﯓﯔﯕ
55:14 Yã halitta mutum daga ƙẽkasasshen yumɓu kumar kasko.
ﯖﯗﯘﯙﯚﯛﯜ
55:15 Kuma ya halitta aljani daga bira daga wutã.
ﯝﯞﯟﯠﯡ
55:16 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
ﯢﯣﯤﯥﯦ
55:17 Ubangjin mafita biyu na rãnã, kuma Ubangijin mafãɗã biyu na rãnã.
ﯧﯨﯩﯪﯫ
55:18 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
ﭑﭒﭓﭔ
55:19 Yã garwaya tẽku biyu (ruwan dãɗi da na zartsi) sunã haɗuwa.
ﭕﭖﭗﭘﭙ
55:20 A tsakãninsu akwai shãmaki, bã za su ƙetare haddi ba.
ﭚﭛﭜﭝﭞ
55:21 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
ﭟﭠﭡﭢﭣ
55:22 Lu'ulu'u da murjãni na fita daga gare su.
ﭤﭥﭦﭧﭨ
55:23 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
ﭩﭪﭫﭬﭭﭮﭯ
55:24 Kuma Yanã da manyan jirãge, waɗanda ake ƙãgãwa a cikin tẽku kamar manyan duwãtsu.
ﭰﭱﭲﭳﭴ
55:25 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
ﭵﭶﭷﭸﭹ
55:26 Dukkan wanda ke kanta mai ƙãrẽwa ne.
ﭺﭻﭼﭽﭾﭿﮀ
55:27 Kuma Fuskarar Ubangijinka, Mai girman Jalala da karimci, ita ce take wanzuwa.
ﮁﮂﮃﮄﮅ
55:28 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
ﮆﮇﮈﮉﮊﮋﮌﮍﮎﮏﮐﮑ
55:29 wanda ke a cikin sammai da ƙasã yanã rõƙon Sa (Allah), a kullum Allah na a cikin wani sha'ani.
ﮒﮓﮔﮕﮖ
55:30 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
ﮗﮘﮙﮚﮛ
55:31 Zã mu ɗauki lõkaci sabõda ku, yã kũ mãsu nauyin halitta biyu!
ﮜﮝﮞﮟﮠ
55:32 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
ﮡﮢﮣﮤﮥﮦﮧﮨﮩﮪﮫﮬﮭﮮﮯﮰﮱﯓ
55:33 Ya jama'ar aljannu da mutãne! Idan kunã iya zarcẽwa daga sãsannin sammai da ƙasã to ku zarce. Bã za ku iya zarcẽwaba fãce da wani dalĩli.
ﯔﯕﯖﯗﯘ
55:34 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
ﯙﯚﯛﯜﯝﯞﯟﯠﯡ
55:35 Anã sako wani harshe daga wata wutã a kanku, da narkakkiyar tagulla. To, bã zã ku nẽmi taimako ba?
ﯢﯣﯤﯥﯦ
55:36 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
ﯧﯨﯩﯪﯫﯬﯭ
55:37 Sa'an nan idan sama ta tsãge kuma ta zama jã kamar jar fãta.
ﯮﯯﯰﯱﯲ
55:38 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
ﯳﯴﯵﯶﯷﯸﯹﯺﯻ
55:39 To, a ran nan bã zã a tambayi wani mutum laifinsa ba, kuma haka aljani.
ﯼﯽﯾﯿﰀ
55:40 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
ﰁﰂﰃﰄﰅﰆﰇ
55:41 zã a iya sanin mãsu laifi da alãmarsu, sabõda haka sai a kãma kwarkaɗarsu da sãwãyensu.
ﭑﭒﭓﭔﭕ
55:42 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
ﭖﭗﭘﭙﭚﭛﭜ
55:43 Wannan Jahannama ce wadda mãsu laifi ke ƙaryatãwa game da ita.
ﭝﭞﭟﭠﭡﭢ
55:44 Sunã kẽwaya a tsakaninta da ruwan ɗimi mai tsananin tafasa.
ﭣﭤﭥﭦﭧ
55:45 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
ﭨﭩﭪﭫﭬﭭ
55:46 Kuma wanda ya ji tsõron tsayãwa a gaba ga Ubangijinsa yanã da Aljanna biyu.
ﭮﭯﭰﭱﭲ
55:47 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
ﭳﭴﭵ
55:48 Mãsu rassan itãce.
ﭶﭷﭸﭹﭺ
55:49 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
ﭻﭼﭽﭾ
55:50 A cikinsu akwai marẽmari biyu sunã gudãna.
ﭿﮀﮁﮂﮃ
55:51 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
ﮄﮅﮆﮇﮈﮉ
55:52 A cikinsu akwai nau'i biyu daga kõwane 'ya'yan itãcen marmari.
ﮊﮋﮌﮍﮎ
55:53 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
ﮏﮐﮑﮒﮓﮔﮕﮖﮗﮘﮙ
55:54 Sunã gincire a kan waɗansu shimfiɗu cikinsu tufãfin alharĩni mai kauri ne kuma nũnannun 'yã'yan itãcen Aljannar biyu kusakusa suke.
ﮚﮛﮜﮝﮞ
55:55 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
ﮟﮠﮡﮢﮣﮤﮥﮦﮧﮨ
55:56 A cikinsu akwai mãtã mãsu taƙaita ganinsu, wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗebe budurcinsu ba kuma haka wani aljani.
ﮩﮪﮫﮬﮭ
55:57 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
ﮮﮯﮰﮱ
55:58 Kamar dai su yaƙũtu ne da murjãni.
ﯓﯔﯕﯖﯗ
55:59 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
ﯘﯙﯚﯛﯜﯝ
55:60 Shin, kyautatãwa nã da wani sakamako? (Ã'aha) fãce kyautatãwa.
ﯞﯟﯠﯡﯢ
55:61 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
ﯣﯤﯥﯦ
55:62 Kuma baicinsu akwai waɗansu gidãjen Aljanna biyu.
ﯧﯨﯩﯪﯫ
55:63 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
ﯬﯭ
55:64 Mãsu duhun inuwa.
ﯮﯯﯰﯱﯲ
55:65 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
ﯳﯴﯵﯶ
55:66 A cikinsu akwai marẽmari biyu masu kwarãrar ruwa.
ﯷﯸﯹﯺﯻ
55:67 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
ﯼﯽﯾﯿﰀ
55:68 A cikinsu akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno darummãni.
ﰁﰂﰃﰄﰅ
55:69 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
ﭑﭒﭓﭔ
55:70 A cikinsu, akwai wasu mãtã mãsu kyaun hãlãye, mãsu kyaun halitta.
ﭕﭖﭗﭘﭙ
55:71 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
ﭚﭛﭜﭝﭞ
55:72 Mãsu farin idãnu da baƙinsu waɗanda aka tsare a cikin haimõmi.
ﭟﭠﭡﭢﭣ
55:73 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
ﭤﭥﭦﭧﭨﭩﭪ
55:74 Wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗẽbe budurcinsu ba, kuma haka wani aljani.
ﭫﭬﭭﭮﭯ
55:75 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
ﭰﭱﭲﭳﭴﭵﭶ
55:76 Sunã gincire a kan wasu matãsai mãsu kõren launi da katĩfun Abkara kyãwãwa.
ﭷﭸﭹﭺﭻ
55:77 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
ﭼﭽﭾﭿﮀﮁﮂ
55:78 Sũnan Ubangjinka, Mai girman Jalãla da Karimci, ya tsarkaka.

Al-Kur'ani


Wednesday, September 9, 2026

Don't forget us in your sincere prayers