7 Aya · Meccan · Hausa
ﭑﭒﭓﭔﭕ
1:1 Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
ﭖﭗﭘﭙﭚ
1:2 Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu;
ﭛﭜﭝ
1:3 Mai rahama, Mai jin ƙai;
ﭞﭟﭠﭡ
1:4 Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako.
ﭢﭣﭤﭥﭦ
1:5 Kai muke bauta wa, kuma Kai muke neman taimakonKa.
ﭧﭨﭩﭪ
1:6 Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya.
ﭫﭬﭭﭮﭯﭰﭱﭲﭳﭴ
1:7 Hanyar waɗanda Ka yi wa ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba.

Al-Kur'ani


Tuesday, September 29, 2026

Don't forget us in your sincere prayers