PDF —
55 Aya Meccan PDF
Built right in your browser — download starts automatically

Surah Al-Qamar pdf — Sauke (Hausa)

Surah Al-Qamar pdf Hausa — Sauke Surah Al-Qamar Fassara. Surah Al-Qamar (Meccan) 55 Aya.

← An-NajmSurah Al-Qamar Ar-Rahman →


55 Aya · Meccan · Hausa
bismillah
ﮬﮭﮮﮯﮰ
54:1 Sã'a ta yi kusa, kuma wata ya tsãge.
ﮱﯓﯔﯕﯖﯗﯘﯙ
54:2 Kuma idan sun ga wata ãyã, sai su juya baya su ce: "Sihiri ne mai dõgẽwa!"
ﯚﯛﯜﯝﯞﯟﯠﯡ
54:3 Kuma suka ƙaryata, kuma suka bi son zũciyarsu, alhãli kuwa kõwane al'amari (wanda suke son su tũre daga Annabi) an tabbatar da shi.
ﯢﯣﯤﯥﯦﯧﯨﯩ
54:4 Kuma lalle, abin da yake akwai tsãwatarwa a cikinsa na lãbãraiya zo musu.
ﯪﯫﯬﯭﯮﯯﯰ
54:5 Hikima cikakka! Sai dai abũbuwan gargaɗi bã su amfãni.
ﯱﯲﯳﯴﯵﯶﯷﯸﯹﯺ
54:6 Sabõda haka, ka bar su! Rãnar da mai kiran zai yi kira zuwa ga wani abu abin ƙyama.
ﭑﭒﭓﭔﭕﭖﭗﭘﭙ
54:7 ¡asƙantattu ga idanunsu zã su fito daga kaburburansu, kamar dai sũ fãri ne waɗandasuka wãtse.
ﭚﭛﭜﭝﭞﭟﭠﭡﭢﭣ
54:8 Sunã gaggãwar tafiya zuwa ga mai kiran, kãfirai na cẽwa, "Wannan yini ne mai wuya!"
ﭤﭥﭦﭧﭨﭩﭪﭫﭬﭭﭮ
54:9 Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, sai suka ƙaryata BawanMu, kuma suka ce: "Shi mahaukaci ne." Kuma aka tsãwace shi.
ﭯﭰﭱﭲﭳﭴ
54:10 Sabõda haka, ya kira Ubangijinsa (ya ce), "Lalle nĩ, an rinjãye ni, sai Ka yi taimako."
ﭵﭶﭷﭸﭹﭺ
54:11 Sai Muka bũɗe kõfõfin sama da ruwa mai zuba.
ﭻﭼﭽﭾﭿﮀﮁﮂﮃﮄ
54:12 Kuma Muka ɓuɓɓugar da ƙasã ta zama idãnun ruwa, daɗa ruwa ya haɗu a kan wani umurni da aka riga aka ƙaddara shi.
ﮅﮆﮇﮈﮉﮊ
54:13 Kuma Muka ɗauke Nũhu a kan (jirgi) na alluna da ƙũsõshi.
ﮋﮌﮍﮎﮏﮐﮑ
54:14 Tanã gudãna, a kan idãnunMu, dõmin sakamako ga wanda aka yi wa kãfircin.
ﮒﮓﮔﮕﮖﮗﮘ
54:15 Kuma lalle, Mun bar ta ta zama ãyã. To, Shin, akwai mai tunãni
ﮙﮚﮛﮜﮝ
54:16 To, yãyã azãbãTa take da gargaɗiNa?
ﮞﮟﮠﮡﮢﮣﮤﮥ
54:17 Kuma lalle ne, haƙĩkƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ãni, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
ﮦﮧﮨﮩﮪﮫﮬ
54:18 Ãdãwa sun ƙaryata, to, yãya azãbãTa take, da gargaɗiNa?
ﮭﮮﮯﮰﮱﯓﯔﯕﯖﯗ
54:19 Lalle Mũ, Mun aika da iska mai tsananin sauti a kansu, a cikin wani yinin nahĩsa mai dõgẽwa.
ﯘﯙﯚﯛﯜﯝﯞ
54:20 Tanã fizgar mutãne kamar dai sũ kututturan dabĩno tumɓukakku ne.
ﯟﯠﯡﯢﯣ
54:21 To, yãya azãbãTa take da gargaɗiNa?
ﯤﯥﯦﯧﯨﯩﯪﯫ
54:22 Kuma lalle ne, haƙiƙa Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
ﯬﯭﯮﯯ
54:23 Samũdãwa sun ƙaryata game da gargaɗin.
ﯰﯱﯲﯳﯴﯵﯶﯷﯸﯹﯺ
54:24 Sai suka ce: "Wani mutum daga cikinmu, shi kaɗai, wai mu bĩ shi! Lalle mũ a lõkacin, haƙĩƙa mun shiga wata ɓata da haukã.
ﯻﯼﯽﯾﯿﰀﰁﰂﰃﰄ
54:25 "Shin, an jẽfa masa Manzancin ne, a tsakãninmu? Ã'a, shĩ dai gawurtaccen maƙaryaci ne mai girman kai!"
ﰅﰆﰇﰈﰉﰊ
54:26 Zã su sani a gõbe, wãne ne gawurtaccen mai ƙaryar, mai girman kan?
ﰋﰌﰍﰎﰏﰐﰑﰒ
54:27 Lalle Mũ, mãsu aikãwa da rãƙumar ne, ta zame musu fitina, sai ka tsare su da kallo, kuma ka yi haƙuri.
ﭑﭒﭓﭔﭕﭖﭗﭘﭙﭚ
54:28 Kuma ka bã su lãbãri cẽwa ruwa rababbe ne a tsakãninsu (da rãƙumar), kõwane sha, mai shi yanã halartar sa.
ﭛﭜﭝﭞﭟ
54:29 Sai suka kira abokinsu, sai ya karɓa, sa'an nan ya sõke ta,
ﭠﭡﭢﭣﭤ
54:30 To, yãya azãbaTa take da gargaɗiNa?
ﭥﭦﭧﭨﭩﭪﭫﭬﭭ
54:31 Lalle Mũ, Mun aika tsãwa guda a kansu, sai suka kasance kamar yãyin mai shinge.
ﭮﭯﭰﭱﭲﭳﭴﭵ
54:32 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
ﭶﭷﭸﭹﭺ
54:33 Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata, game da gargaɗi.
ﭻﭼﭽﭾﭿﮀﮁﮂﮃﮄﮅ
54:34 Lalle Mun aika iskar tsakuwa a kansu, fãce mabiyan Lũɗu, Mun tsirar da su a lõkacin asuba.
ﮆﮇﮈﮉﮊﮋﮌﮍﮎ
54:35 Sabõda wata ni'ima ta daga gare Mu. Kamar haka Muke sãka wa wanda ya gõde.
ﮏﮐﮑﮒﮓﮔ
54:36 Kuma lalle, haƙĩƙa, ya yi musu gargaɗin damƙarMu, sai suka yi musu game da gargaɗin.
ﮕﮖﮗﮘﮙﮚﮛﮜﮝﮞ
54:37 Kuma lalle haƙĩƙa, su, sun nẽme shi ta wajen bãƙinsa, sai Muka shãfe idãnunsu. "To, ku ɗanɗani azãbaTa da gargaɗĩNa."
ﮟﮠﮡﮢﮣﮤ
54:38 Kuma lalle, haƙĩƙa, wata azãba matabbaciya tã wãye musu gari da yãƙi, tun da sãfe.
ﮥﮦﮧﮨ
54:39 To, ku ɗanɗani azãbãTa da gargaɗĩNa.
ﮩﮪﮫﮬﮭﮮﮯﮰ
54:40 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur, ani dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?
ﮱﯓﯔﯕﯖﯗ
54:41 Kuma lalle, haƙĩƙa, gargaɗin ya jẽ wa mabiyan Fir'auna.
ﯘﯙﯚﯛﯜﯝﯞﯟ
54:42 Sun ƙaryata game da ãyõyinMu, dukansu sai Muka kãma su, irin kãmun Mabuwãyi, Mai ĩkon yi.
ﯠﯡﯢﯣﯤﯦﯧﯨﯩﯪ
54:43 Shin, kãfiranku ne mafi alhẽri daga waɗancan, ko kuwa kunã da wata barã'a a cikin littattafai?
ﯫﯬﯭﯮﯯﯰ
54:44 Kõ zã su ce: "Mũ duka mãsu haɗa ƙarfi ne dõmin cin nasara?"
ﯱﯲﯳﯴﯵ
54:45 Zã a karya tãron, kuma su jũya bãya dõmin gudu.
ﯶﯷﯸﯹﯺﯻﯼ
54:46 Ã'a, Sã'a ita cẽ lõkacin wa'adinsu, kuma Sã'ar tã fi tsananin masĩfa, kuma ta fiɗãci.
ﯽﯾﯿﰀﰁﰂ
54:47 Lalle ne, mãsu laifi sunã a cikin ɓata da hauka.
ﰃﰄﰅﰆﰇﰈﰉﰊﰋﰌ
54:48 Rãnar da zã a jã su a cikin wuta a kan fuskõkinsu. "Ku ɗanɗani shãfar wutar Saƙar."
ﰍﰎﰏﰐﰑﰒ
54:49 Lalle Mũ, kõwane irin abu Mun halitta shi a kan tsãri.
ﭑﭒﭓﭔﭕﭖﭗ
54:50 Kuma umurninMu bai zamo ba fãce da kalma ɗaya, kamar walƙãwar ido.
ﭘﭙﭚﭛﭜﭝﭞ
54:51 Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun halaka irin gayyarku. To, shin, akwai mai tunãni?
ﭟﭠﭡﭢﭣﭤ
54:52 Kuma kõwane abu, da suka aikata shi, yanã a cikin littattafai.
ﭥﭦﭧﭨﭩ
54:53 Kuma dukkan ƙarami da babba, rubutacce ne.
ﭪﭫﭬﭭﭮﭯ
54:54 Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna da kõguna.
ﭰﭱﭲﭳﭴﭵﭶ
54:55 A cikin mazaunin gaskiya, wurin Mai ikon yi, Mai iya zartaswa.

Al-Kur'ani


Wednesday, September 9, 2026

Don't forget us in your sincere prayers