Surah Al-'Adiyat pdf — Sauke (Hausa)
Surah Al-'Adiyat pdf Hausa — Sauke Surah Al-'Adiyat Fassara. Surah Al-'Adiyat (Meccan) 11 Aya.
Related
- Surah Al-'Adiyat FassaraHausa
- Surah Al-'Adiyat mp3Saurara
- Quran Index Hausa114
More Surah PDF
Surah Al-'Adiyat

ﮱﯓﯔ
100:1
Ina rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki.
ﯕﯖﯗ
100:2
Mãsu ƙyasta wuta (da kõfatansu a kan duwatsu) ƙyastawa.
ﯘﯙﯚ
100:3
Sa'an nan mãsu yin hari a lokacin asuba.
ﯛﯜﯝﯞ
100:4
Sai su motsar da ƙũra game da shi.
ﯟﯠﯡﯢ
100:5
Sai su shiga, game da ita (ƙũrar), a tsakãnin jama'ar maƙiya.
ﭑﭒﭓﭔﭕ
100:6
Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa.
ﭖﭗﭘﭙﭚ
100:7
Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa dl haka.
ﭛﭜﭝﭞﭟ
100:8
Kuma 1alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne.
ﭠﭡﭢﭣﭤﭥﭦﭧﭨ
100:9
Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura.
ﭩﭪﭫﭬﭭ
100:10
Aka bayyana abin da ke cikin zukata.
ﭮﭯﭰﭱﭲﭳ
100:11
Lalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne?
Al-Kur'ani
Wednesday, September 9, 2026
Don't forget us in your sincere prayers







