Surah Al-Qari'ah Larabci da Hausa

Karanta Surah Al-Qari'ah tare da cikakkiyar fassarar Hausa da sauti. Fassara aya bayan aya. (11 Aya — مكية). Al-Qari'ah Saurara, Al-Qari'ah Fassara, Al-Qari'ah mp3, Al-Qari'ah pdf.

Karanta da Saurara Surah Al-Qari'ah

🎧 Aya
M Mishary Rashid Alafasy
M Mahmoud Khalil Al-Husary
A Abdurrahman As-Sudais
M Mohamed Siddiq Al-Minshawi
A Abdul Basit Abdul Samad
A Ali Al-Hudhaify
A Ahmed ibn Ali al-Ajamy
A Abu Bakr Ash-Shaatree
M Muhammad Ayyoub
A Abdullah Basfar
A Abdullah Al-Juhani
M Maher Al Muaiqly
x1
الْقَارِعَةُ ۝١
📖 Fassara Aya 1
Mai ƙwanƙwasar (zukata da tsõro)!
مَا الْقَارِعَةُ ۝٢
📖 Fassara Aya 2
Mẽnẽ ne mai ƙwanƙwasa?
وَمَا أَدْرَاكَ مَا الْقَارِعَةُ ۝٣
📖 Fassara Aya 3
Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa mai ƙwanƙwasa?
يَوْمَ يَكُونُ النَّاسُ كَالْفَرَاشِ الْمَبْثُوثِ ۝٤
📖 Fassara Aya 4
Rãnar da mutãne za su kasance kamar 'ya'yan fari mãsu wãtsuwa.
وَتَكُونُ الْجِبَالُ كَالْعِهْنِ الْمَنفُوشِ ۝٥
📖 Fassara Aya 5
Kuma duwãtsu su kasance kamar gãshin sũfin da aka saɓe.
فَأَمَّا مَن ثَقُلَتْ مَوَازِينُهُ ۝٦
📖 Fassara Aya 6
To, amma wanda ma'aunansa suka yi nauyi.
فَهُوَ فِي عِيشَةٍ رَّاضِيَةٍ ۝٧
📖 Fassara Aya 7
To, shi yana a cikin wata rayuwa yardadda.
وَأَمَّا مَنْ خَفَّتْ مَوَازِينُهُ ۝٨
📖 Fassara Aya 8
Kuma amma wanda ma'aunansa suka yi sauƙi (bãbu nauyi).
فَأُمُّهُ هَاوِيَةٌ ۝٩
📖 Fassara Aya 9
To, uwarsa Hãwiya ce.
وَمَا أَدْرَاكَ مَا هِيَهْ ۝١٠
📖 Fassara Aya 10
Kuma me ya sanar da kai mece ce ita?
نَارٌ حَامِيَةٌ ۝١١
📖 Fassara Aya 11
Wata wuta ce mai zafi.
← 100 Al-Qari'ah (101/114) 102 →
Karatu Surah Al-Qari'ah Hausa – Fassara da Audio

101القارعة Al-Qari'ah 📚 11 Aya مكية



Al-Kur'ani


Tuesday, August 18, 2026

Don't forget us in your sincere prayers