PDF —
44 Aya Meccan PDF
Built right in your browser — download starts automatically

Surah Al-Ma'arij pdf — Sauke (Hausa)

Surah Al-Ma'arij pdf Hausa — Sauke Surah Al-Ma'arij Fassara. Surah Al-Ma'arij (Meccan) 44 Aya.

← Al-HaqqahSurah Al-Ma'arij Nuh →


44 Aya · Meccan · Hausa
bismillah
ﮮﮯﮰﮱﯓ
70:1 Wani mai tambaya yã yi tambaya game da azãba, mai aukuwa.
ﯔﯕﯖﯗﯘ
70:2 Ga kãfirai, bã ta da mai tunkuɗẽwa.
ﯙﯚﯛﯜﯝ
70:3 Daga Allah Mai matãkala.
ﯞﯟﯠﯡﯢﯣﯤﯥﯦﯧﯨﯩ
70:4 Malã'iku da Ruhi (Jibrila) sunã tãkãwa zuwa gare Shi, a cikin yini wanda gwargwadonsa, shẽkara dubu hamsin ne.
ﯪﯫﯬﯭ
70:5 Sabõda haka, ka yi haƙuri, haƙuri mai kyãwo.
ﯮﯯﯰﯱ
70:6 Lalle ne su, sunã ganin ta mai nĩsa.
ﯲﯳﯴ
70:7 Kuma Mu, Muna ganin ta a kusa.
ﯵﯶﯷﯸﯹ
70:8 Rãnar da sama zã ta kasance kamar narkakkar azurfa.
ﯺﯻﯼﯽ
70:9 Kuma duwãtsu su zama kamar saɓin sũfi.
ﯾﯿﰀﰁﰂ
70:10 Kuma abõki bã ya tambayar inda wani abõki yake.
ﭑﭒﭓﭔﭕﭖﭗﭘﭙﭚﭛ
70:11 Ana sanya su, su gajũna, mai laifi na gũrin dã zai iya yin fansa, daga azãbar rãnar nan, da ɗiyansa,
ﭜﭝﭞ
70:12 Da matarsa da ɗan'uwansa.
ﭟﭠﭡﭢ
70:13 Da danginsa, mãsu tattarã shi.
ﭣﭤﭥﭦﭧﭨﭩ
70:14 Da wanda ke a cikin dũniya duka gabã ɗaya, sa'an nan fansar, ta tsĩrar da shi.
ﭪﭫﭬﭭﭮ
70:15 A'aha! Lalle ne fa, ita ce Lazã,
ﭯﭰﭱ
70:16 Mai twãle fãtar goshi.
ﭲﭳﭴﭵﭶ
70:17 Tanã kiran wanda ya jũya bãya (daga addini) kuma ya kau da kai.
ﭷﭸﭹ
70:18 Ya tãra (dũkiya), kuma ya sanya ta a cikin jaka.
ﭺﭻﭼﭽﭾﭿ
70:19 Lalle ne mutum an halitta shi mai ciwon kwaɗayi.
ﮀﮁﮂﮃﮄ
70:20 Idan sharri ya shãfe shi, ya kãsa haƙuri.
ﮅﮆﮇﮈﮉ
70:21 Kuma idan alhẽri ya shãfe shi, ya yi rõwa.
ﮊﮋﮌ
70:22 Sai mãsu yin salla,
ﮍﮎﮏﮐﮑﮒ
70:23 Waɗanda suke, a kan sallarsu, su, mãsu dawwama ne.
ﮓﮔﮕﮖﮗﮘ
70:24 Kuma waɗanda a cikin dũkiyarsu, akwai wani haƙƙi sananne.
ﮙﮚﮛ
70:25 Ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hanã wa roƙon.
ﮜﮝﮞﮟﮠ
70:26 Da waɗannan da ke gaskata rãnar sakamako.
ﮡﮢﮣﮤﮥﮦﮧ
70:27 Da waɗannan sabõda azãbar Ubangijinsu, suna jin tsõro.
ﮨﮩﮪﮫﮬﮭ
70:28 Lalle ne, azãbar Ubangijinsu bã wadda ake iya amincẽwaba ce.
ﮮﮯﮰﮱﯓ
70:29 Da waɗanda suke, ga farjojinsu, mãsu tsarewa ne.
ﯔﯕﯖﯗﯘﯙﯚﯛﯜﯝﯞ
70:30 Sai fa a kan matan aurensu da abin da hannayensu na dãma suka mallaka. To lalle ne sũkam ba waɗanda ake zargi ba ne.
ﯟﯠﯡﯢﯣﯤﯥﯦ
70:31 To, duk wanda ya nẽmi abin da yake a bayan wannan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙetare iyãka.
ﯧﯨﯩﯪﯫﯬ
70:32 Kuma da waɗannan da suke ga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne.
ﯭﯮﯯﯰﯱ
70:33 Kuma da waɗanda suke, ga shaidarsu, mãsu dãgẽwa ne.
ﯲﯳﯴﯵﯶﯷ
70:34 Kuma waɗanda suke, a kan sallarsu, mãsu tsarẽwa ne.
ﯸﯹﯺﯻﯼ
70:35 Waɗannan, a cikin gidãjen Aljanna, waɗanda ake girmamãwa ne
ﯽﯾﯿﰀﰁﰂ
70:36 Mẽ yã sãmi waɗanda suka kãfirta, a wajenka, sunã gaugãwar (gudu).
ﰃﰄﰅﰆﰇﰈ
70:37 Daga jihar dãma, kuma daga jihar hagu, jama'a-jama'a!
ﰉﰊﰋﰌﰍﰎﰏﰐﰑ
70:38 Shin kõwane mutum daga cikinsu yana nẽman a shigar da shi a Aljannar ni'ima ne (ba da wani aiki ba)?
ﰒﰓﰔﰕﰖﰗﰘ
70:39 A'aha! Lalle Mũ, Mun halitta su, daga abin da suka sani.
ﰙﰚﰛﰜﰝﰞﰟﰠ
70:40 Sabõda haka ba sai Na yi rantsuwa da Ubangijin wurãren ɓullõwar rãna da wurãren fãɗuwarta ba, lalle Mũ, Mãsu iyãwa ne.
ﭑﭒﭓﭔﭕﭖﭗﭘﭙ
70:41 Ga Mu musanya waɗanda suke mafi alhẽri, daga gare su. Kuma ba Mu kasance waɗanda ake rinjãya ba.
ﭚﭛﭜﭝﭞﭟﭠﭡﭢ
70:42 Sabõda haka ka bar su, su dulmuya, kuma su yi wãsã, har su haɗu da rãnarsu wadda ake yi musu alkawari (da ita).
ﭣﭤﭥﭦﭧﭨﭩﭪﭫﭬ
70:43 Rãnar da suke fitowa daga kaburbura da gaugãwa, kamar sũ, zuwa ga wata kafaffiyar (tuta), suke yin gaugãwa.
ﭭﭮﭯﭰﭱﭲﭳﭴﭵﭶﭷ
70:44 Maƙaskanta ga idanunsu, wani walakanci yana rufe su. wannan shi ne yinin da suka kasance ana yi musa alkawari (a kansa.)

Al-Kur'ani


Wednesday, September 9, 2026

Don't forget us in your sincere prayers