PDF —
22 Aya Meccan PDF
Built right in your browser — download starts automatically

Surah Al-Buruj pdf — Sauke (Hausa)

Surah Al-Buruj pdf Hausa — Sauke Surah Al-Buruj Fassara. Surah Al-Buruj (Meccan) 22 Aya.



22 Aya · Meccan · Hausa
bismillah
ﭛﭜﭝﭞ
85:1 Inã rantsuwa da sama mai taurãrin lissafin shekara.
ﭟﭠﭡ
85:2 Da yinin da aka yi alkawarin zuwansa,
ﭢﭣﭤ
85:3 Da yini mai shaidu, da yini da ake halarta a cikinsa
ﭥﭦﭧﭨ
85:4 An la'ani mutãnen rãmi.
ﭩﭪﭫﭬ
85:5 Wato wuta wadda aka hura.
ﭭﭮﭯﭰﭱ
85:6 A lõkacin da suke a kan (gefen) ta a zazzaune.
ﭲﭳﭴﭵﭶﭷﭸ
85:7 Alhãli sũ, bisa ga abin da suke aikatãwa ga mũminai, sunã halarce.
ﭹﭺﭻﭼﭽﭾﭿﮀﮁﮂ
85:8 Kuma ba su tuhumce su ba, fãce kawai domin sun yi ĩmãni da Allah Mabuwãyi, wanda ake gõdewa.
ﮃﮄﮅﮆﮇﮈﮉﮊﮋﮌﮍﮎ
85:9 Wanda Yake shi ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma Allah a kan kõme halarce Yake.
ﮏﮐﮑﮒﮓﮔﮕﮖﮗﮘﮙﮚﮛﮜﮝ
85:10 Lalle ne waɗanda suka fitini mũminai maza da mũminai mãta, sa'an nan ba su tũba ba to, sunã da azãbar Jahannama, kuma sunã da azãbar gõbara.
ﮞﮟﮠﮡﮢﮣﮤﮥﮦﮧﮨﮩﮪﮫﮬﮭ
85:11 Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen. Wancan abu fa shi ne rabo babba.
ﮮﮯﮰﮱﯓ
85:12 Lalle ne damƙar Ubangijinka mai tsanani ce ƙwarai.
ﯔﯕﯖﯗﯘ
85:13 Lalle ne Shĩ, Shi ne Mai ƙãga halitta, kuma Ya mayar da ita (bãyan mutuwa).
ﯙﯚﯛﯜ
85:14 Kuma Shi ne Mai gãfara, Mai bayyana sõyayya.
ﯝﯞﯟﯠ
85:15 Mai Al'arshi mai girma
ﯡﯢﯣﯤ
85:16 Mai aikatãwa ga abin da Yake nufi.
ﯥﯦﯧﯨﯩ
85:17 Ko lãbãrin rundanõni yã zo maka.
ﯪﯫﯬ
85:18 Fir'auna da samũdãwa?
ﯭﯮﯯﯰﯱﯲ
85:19 Ã'aha! waɗanda suka kãfirta sunã cikin ƙaryatãwa.
ﯳﯴﯵﯶﯷ
85:20 Alhãli, Allah daga bãyansu, Mai kẽwaye su ne (da saninSa).
ﯸﯹﯺﯻﯼ
85:21 Ã'aha! Shi Alƙur'ãni ne mai girma.
ﯽﯾﯿﰀ
85:22 A cikin Allo tsararre.

Al-Kur'ani


Wednesday, September 9, 2026

Don't forget us in your sincere prayers