PDF —
30 Aya Meccan PDF
Built right in your browser — download starts automatically

Surah Al-Fajr pdf — Sauke (Hausa)

Surah Al-Fajr pdf Hausa — Sauke Surah Al-Fajr Fassara. Surah Al-Fajr (Meccan) 30 Aya.



30 Aya · Meccan · Hausa
bismillah
ﭤﭥ
89:1 Inã rantsuwa da alfijiri.
ﭦﭧﭨ
89:2 Da darũruwa gõma.
ﭩﭪﭫ
89:3 Da (adadi na) cikã da (na) mãrã.
ﭬﭭﭮﭯ
89:4 Da dare idan yana shũɗewa.
ﭰﭱﭲﭳﭴﭵﭶ
89:5 Ko a cikin waɗannan akwai abin rantsuwa ga mai hankali (da yake kange shi daga zunubi)?
ﭷﭸﭹﭺﭻﭼﭽ
89:6 Ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata da Ãdãwa ba?
ﭾﭿﮀﮁ
89:7 Iramawa mãsu sakon ƙĩrar jiki.
ﮂﮃﮄﮅﮆﮇﮈ
89:8 Waɗanda ba a halitta kwatankwacinsu ba a cikin garũruwa (na dũniya).
ﮉﮊﮋﮌﮍﮎ
89:9 Da samũdãwa waɗanda suka fasa duwãtsu a cikin Wadi suka yi gidãje)?
ﮏﮐﮑﮒ
89:10 Da Fir'auna mai turãku.
ﮓﮔﮕﮖﮗ
89:11 Waɗanda suka ƙẽtare iyãkarsu, a cikin garũruwa?
ﮘﮙﮚﮛ
89:12 Sabõda haka, suka yawaita yin ɓarna a cikinsu.
ﮜﮝﮞﮟﮠﮡ
89:13 Sabõda haka Ubangijinka Ya zuba musu bũlãlar azãba.
ﮢﮣﮤﮥ
89:14 Lalle ne, Ubangijinka Yana nan a mafaka.
ﮦﮧﮨﮩﮪﮫﮬﮭﮮﮯﮰﮱ
89:15 To, amma fa mutum idan Ubangijibsa Ya jarraba shi, wãto Yã girmama shi kuma Ya yi masa ni'ima, sai ya ce: "Ubangijina Ya girmama ni."
ﯓﯔﯕﯖﯗﯘﯙﯚﯛﯜﯝ
89:16 Kuma idan Ya jarraba shi, wãto Ya ƙuntata masa abincinsa, sai ya ce: "Ubangijina Ya walãkanta ni."
ﯞﯟﯠﯡﯢﯣﯤ
89:17 A'aha! Bari wannan, ai bã ku girmama marãya!
ﯥﯦﯧﯨﯩﯪ
89:18 Bã ku kwaɗaitã wa jũnanku ga (tattalin) abincin matalauci!
ﯫﯬﯭﯮﯯ
89:19 Kuma kuna cin dũkiyar gãdo, ci na tãrãwa.
ﯰﯱﯲﯳﯴ
89:20 Kuma kuna son dũkiya, so mai yawa.
ﯵﯶﯷﯸﯹﯺﯻﯼ
89:21 A'aha! Idan aka niƙa ƙasa niƙewa sosai.
ﯽﯾﯿﰀﰁﰂ
89:22 Kuma Ubangijinka Ya zo, alhãli malã'iku na jẽre, safũ- safu.
ﭑﭒﭓﭔﭕﭖﭗﭘﭙﭚﭛ
89:23 Kuma a ranar nan aka zo da Jahannama. A ranar nan mutum zai yi tunãni. To, inã fa tunãni yake a gare shi!
ﭜﭝﭞﭟﭠ
89:24 Yana dinga cẽwa, "Kaitona, dã na gabatar (da aikin ƙwarai) domin rãyuwata!"
ﭡﭢﭣﭤﭥﭦ
89:25 To, a rãnar nan bãbu wani mai yin azãba irin azãbar Allah.
ﭧﭨﭩﭪﭫ
89:26 Kuma bãbu wani mai ɗauri irin ɗaurinSa.
ﭬﭭﭮﭯ
89:27 Yã kai rai mai natsuwa!
ﭰﭱﭲﭳﭴﭵ
89:28 Ka koma zuwa ga Ubangijinka, alhãli kana mai yarda (da abin da Ya ƙaddara maka a dũniya) abar yardarwa (da sakamakon da zã a ba ka a Lãhira).
ﭶﭷﭸﭹ
89:29 Sabõbda haka, ka shiga cikin bãyiNa (mãsu bin umurui a dũniya).
ﭺﭻﭼ
89:30 Kuma ka shiga AljannaTa (a Lãhira).

Al-Kur'ani


Wednesday, September 9, 2026

Don't forget us in your sincere prayers