Surah At-Tin Larabci da Hausa

Karanta Surah At-Tin tare da cikakkiyar fassarar Hausa da sauti. Fassara aya bayan aya. (8 Aya — مكية). At-Tin Saurara, At-Tin Fassara, At-Tin mp3, At-Tin pdf.

Karanta da Saurara Surah At-Tin

🎧 Aya
M Mishary Rashid Alafasy ✓
M Mahmoud Khalil Al-Husary ✓
A Abdurrahman As-Sudais ✓
M Mohamed Siddiq Al-Minshawi ✓
A Abdul Basit Abdul Samad ✓
A Ali Al-Hudhaify ✓
A Ahmed ibn Ali al-Ajamy ✓
A Abu Bakr Ash-Shaatree ✓
M Muhammad Ayyoub ✓
A Abdullah Basfar ✓
A Abdullah Al-Juhani ✓
M Maher Al Muaiqly ✓
—
x1
bismillah
وَالتِّينِ وَالزَّيْتُونِ ۝١
📖 Fassara Aya 1
Inã rantsuwa da Attinu da Azzaitũn.
وَطُورِ سِينِينَ ۝٢
📖 Fassara Aya 2
Da Dũr Sĩnĩna.
وَهَٰذَا الْبَلَدِ الْأَمِينِ ۝٣
📖 Fassara Aya 3
Da wannan gari amintacce.
لَقَدْ خَلَقْنَا الْإِنسَانَ فِي أَحْسَنِ تَقْوِيمٍ ۝٤
📖 Fassara Aya 4
Lalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa.
ثُمَّ رَدَدْنَاهُ أَسْفَلَ سَافِلِينَ ۝٥
📖 Fassara Aya 5
Sa'an nan, Muka mayar da shi mafi ƙasƙantar masu rauni
إِلَّا الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ فَلَهُمْ أَجْرٌ غَيْرُ مَمْنُونٍ ۝٦
📖 Fassara Aya 6
Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, saboda haka suna da sakamako wanda bã ya yankewa.
فَمَا يُكَذِّبُكَ بَعْدُ بِالدِّينِ ۝٧
📖 Fassara Aya 7
To, bãyan haka mẽ ya sanya ka ka ƙaryata sakamako (wanda za a yi a bãyan Tãshin ¡iyãma)?
أَلَيْسَ اللَّهُ بِأَحْكَمِ الْحَاكِمِينَ ۝٨
📖 Fassara Aya 8
Ashe Allah bã Shi ne Mafi mãsu hukunci kyãwon hukunci ba?
← 94 At-Tin (95/114) 96 →
Karatu Surah At-Tin Hausa – Fassara da Audio

95التين At-Tin 📚 8 Aya مكية



Al-Kur'ani


Monday, September 28, 2026

Don't forget us in your sincere prayers