Surah Al-'Alaq Larabci da Hausa

Karanta Surah Al-'Alaq tare da cikakkiyar fassarar Hausa da sauti. Fassara aya bayan aya. (19 Aya — مكية). Al-'Alaq Saurara, Al-'Alaq Fassara, Al-'Alaq mp3, Al-'Alaq pdf.

Karanta da Saurara Surah Al-'Alaq

🎧 Aya
M Mishary Rashid Alafasy
M Mahmoud Khalil Al-Husary
A Abdurrahman As-Sudais
M Mohamed Siddiq Al-Minshawi
A Abdul Basit Abdul Samad
A Ali Al-Hudhaify
A Ahmed ibn Ali al-Ajamy
A Abu Bakr Ash-Shaatree
M Muhammad Ayyoub
A Abdullah Basfar
A Abdullah Al-Juhani
M Maher Al Muaiqly
x1
اقْرَأْ بِاسْمِ رَبِّكَ الَّذِي خَلَقَ ۝١
📖 Fassara Aya 1
Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta.
خَلَقَ الْإِنسَانَ مِنْ عَلَقٍ ۝٢
📖 Fassara Aya 2
Ya hahitta mutum daga gudan jini.
اقْرَأْ وَرَبُّكَ الْأَكْرَمُ ۝٣
📖 Fassara Aya 3
Ka yi karatu, kuma UbangiJinka shi ne Mafi karimci.
الَّذِي عَلَّمَ بِالْقَلَمِ ۝٤
📖 Fassara Aya 4
Wanda Ya sanar (da mutum) game da alƙalami.
عَلَّمَ الْإِنسَانَ مَا لَمْ يَعْلَمْ ۝٥
📖 Fassara Aya 5
Ya sanar da mutum abin da bai sani ba.
كَلَّا إِنَّ الْإِنسَانَ لَيَطْغَىٰ ۝٦
📖 Fassara Aya 6
A'aha! Lalle, ne mutum haƙĩƙa, yana girman kai (ya ƙi karatu).
أَن رَّآهُ اسْتَغْنَىٰ ۝٧
📖 Fassara Aya 7
Dõmin yã ga kansa, yã wadãta.
إِنَّ إِلَىٰ رَبِّكَ الرُّجْعَىٰ ۝٨
📖 Fassara Aya 8
Lalle ne zuwa ga Ubangijinka makoma take.
أَرَأَيْتَ الَّذِي يَنْهَىٰ ۝٩
📖 Fassara Aya 9
Shin, kã ga wanda ke hana.
عَبْدًا إِذَا صَلَّىٰ ۝١٠
📖 Fassara Aya 10
Bãwã idan yã yi salla?
أَرَأَيْتَ إِن كَانَ عَلَى الْهُدَىٰ ۝١١
📖 Fassara Aya 11
Ashe, kã gani, idan (shi bãwan) ya kasance a kan shiriya?
أَوْ أَمَرَ بِالتَّقْوَىٰ ۝١٢
📖 Fassara Aya 12
Ko ya yi umurni da taƙawa?
أَرَأَيْتَ إِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ ۝١٣
📖 Fassara Aya 13
Ashe, kã gani, idan (shi mai hanin) ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya?
أَلَمْ يَعْلَم بِأَنَّ اللَّهَ يَرَىٰ ۝١٤
📖 Fassara Aya 14
Ashe, bai sani ba cewa Allah Yanã gani?
كَلَّا لَئِن لَّمْ يَنتَهِ لَنَسْفَعًا بِالنَّاصِيَةِ ۝١٥
📖 Fassara Aya 15
A'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, lalle ne zã Mu ja gãshin makwarkwaɗa.
نَاصِيَةٍ كَاذِبَةٍ خَاطِئَةٍ ۝١٦
📖 Fassara Aya 16
Makwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi.
فَلْيَدْعُ نَادِيَهُ ۝١٧
📖 Fassara Aya 17
Sai ya kirayi ƙungiyarsa.
سَنَدْعُ الزَّبَانِيَةَ ۝١٨
📖 Fassara Aya 18
Zã Mu kirayi zabaniyãwa (mala'iku mãsu girma).
كَلَّا لَا تُطِعْهُ وَاسْجُدْ وَاقْتَرِب ۩ ۝١٩
📖 Fassara Aya 19
A'aha kada ka bĩ shi. Kuma ka yi tawali'u, kuma ka nemi kusanta (zuwa ga Ubangijinka).
← 95 Al-'Alaq (96/114) 97 →
Karatu Surah Al-'Alaq Hausa – Fassara da Audio

96العلق Al-'Alaq 📚 19 Aya مكية



Al-Kur'ani


Tuesday, August 18, 2026

Don't forget us in your sincere prayers