PDF —
40 Aya Meccan PDF
Built right in your browser — download starts automatically

Surah Al-Qiyamah pdf — Sauke (Hausa)

Surah Al-Qiyamah pdf Hausa — Sauke Surah Al-Qiyamah Fassara. Surah Al-Qiyamah (Meccan) 40 Aya.



40 Aya · Meccan · Hausa
bismillah
ﮊﮋﮌﮍﮎ
75:1 Bã sai Nã yi rantsuwa da Rãnar ¡iyãma ba.
ﮏﮐﮑﮒﮓ
75:2 Bã sai Nã yi rantsuwa da rai mai yawan zargin kansa ba.
ﮔﮕﮖﮗﮘﮙ
75:3 Sin, mutum yana zaton cẽwa bã zã Mu tãra ƙasusuwansa ba?
ﮚﮛﮜﮝﮞﮟﮠ
75:4 Na'am! Mãsu ĩkon yi Muke a kan Mu daidaita gaɓõɓin yãtsunsa.
ﮡﮢﮣﮤﮥﮦ
75:5 Ba haka ba! Mutum so yake, ya yi fãjirci, ya ƙaryata abin da yake a gabansa.
ﮧﮨﮩﮪﮫ
75:6 Yanã tambaya: "Yaushe ne Rãnar ¡iyãma?"
ﮬﮭﮮﮯ
75:7 To, idan gani ya ɗimauta (ya yi ƙyalli).
ﮰﮱﯓ
75:8 Kuma, watã ya yi husũfi (haskensa ya dushe).
ﯔﯕﯖﯗ
75:9 Aka tãra rãnã da watã
ﯘﯙﯚﯛﯜﯝ
75:10 Mutum zai ce a rãn nan "Ina wurin gudu?"
ﯞﯟﯠﯡ
75:11 A'aha! bãbu mafaka.
ﯢﯣﯤﯥﯦ
75:12 zuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a rãnar nan, yake.
ﯧﯨﯩﯪﯫﯬﯭ
75:13 Ana gayã wa mutum, a rãnar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar.
ﯮﯯﯰﯱﯲﯳ
75:14 Ba haka ba! Mutum, ga abin da ya shafi kansa, masani ne.
ﯴﯵﯶﯷ
75:15 Kuma ko da yã jẽfa uzurorinsa (bã zã a saurãre shi ba).
ﯸﯹﯺﯻﯼﯽﯾ
75:16 Kada ka mõtsar da harshenka game da shi dõmin ka yi gaugãwar riƙe shi (Alƙur'ãni).
ﯿﰀﰁﰂﰃ
75:17 Lalle ne, wãjibi ne a gare Mu, Mu tãra shi. Mu (tsare maka) karãtunsa.
ﰄﰅﰆﰇﰈ
75:18 To idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa.
ﰉﰊﰋﰌﰍ
75:19 sa'an nan, lalle wãjibi ne a gare Mu, bayãninsa.
ﭑﭒﭓﭔﭕ
75:20 A'aha! Bã haka ba kunã son mai gaugawar nan (duniya) ne.
ﭖﭗﭘ
75:21 Kunã barin ta ƙarshen (Lãhira).
ﭙﭚﭛﭜ
75:22 Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu annuri ne.
ﭝﭞﭟﭠ
75:23 Zuwa ga Ubangijinsu mãsu kallo ne.
ﭡﭢﭣﭤ
75:24 Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu gintsẽwa ne.
ﭥﭦﭧﭨﭩﭪ
75:25 Sunã zaton a sako musu masĩfa mai karya tsatso.
ﭫﭬﭭﭮﭯ
75:26 A'aha! Iadan (rai) ya kai ga karankarmai.
ﭰﭱﭲﭳﭴ
75:27 kuma aka ce: "Wãne ne mai tawada?"
ﭵﭶﭷﭸ
75:28 Kuma ya tabbata cẽwa rabuwa dai ce.
ﭹﭺﭻﭼ
75:29 Kuma ƙwabri ya lauye da wani ƙwabri.
ﭽﭾﭿﮀﮁ
75:30 Zuwa ga Ubangijinka, a rãnar nan, magargaɗa take.
ﮂﮃﮄﮅﮆ
75:31 To, bai gaskatã ba, kuma bai yi salla ba!
ﮇﮈﮉﮊ
75:32 Amma dai ya ƙaryata, kuma ya jũya baya!
ﮋﮌﮍﮎﮏﮐ
75:33 Sa'an nan, ya tafi zuwa ga mutãnensa, yana tãƙama.
ﮑﮒﮓﮔ
75:34 Halaka tã tabbata a gare ka, sa'an nan ita ce mafi dãcewa.
ﮕﮖﮗﮘﮙ
75:35 Sa'an nan, wata halaka tã tabbata a gare ka dõmin tã fi dãce wa.
ﮚﮛﮜﮝﮞﮟ
75:36 Shin, mutum nã zaton a bar shi sagaga (wãto bãbu nufin kõme game da shi)?
ﮠﮡﮢﮣﮤﮥﮦ
75:37 Bai kasance iɗgo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa (a cikin mahaifa)
ﮧﮨﮩﮪﮫﮬ
75:38 Sa'an nan, ya zama gudan jini, sa'an nan Allah Ya halitta shi, sa'an nan Ya daidaita gaɓõɓinsa;
ﮭﮮﮯﮰﮱﯓ
75:39 Sa'an nan, Ya sanya daga gare shi, nau'i biyu: namiji damace?
ﯔﯕﯖﯗﯘﯙﯚﯛ
75:40 Ashẽ wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rãyar da matattu?

Al-Kur'ani


Wednesday, September 9, 2026

Don't forget us in your sincere prayers