Alam tara ilal lazee Haaajja Ibraaheema fee Rabbiheee an aataahullaahul mulka iz qaala Ibraaheemu Rabbiyal lazee yuhyee wa yumeetu qaala ana uhyee wa yumeetu qaala ana uhyee wa umeetu qaala Ibraaheemu fa innal laaha yaatee bishshamsi minal mashriqi faati bihaa minal maghribi fabuhital lazee kafar; wallaahu laa yahdil qawmaz zaalimeen
📖 Fassara (Da Hausa)
📖 Da Hausa
Shin, ba ka gani ba zuwa ga wanda ya yi hujjatayya da Ibrãhĩm a cikin (al'amarin) Ubangijinsa dõmin Allah Yã bã shi mulki, a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: "Ubangijina Shi ne Wanda Yake rãyawa kuma Yana matarwa." Ya ce: "Nĩ ina rãyarwa kuma ina matarwa." Ibrãhĩm ya ce: "To, lalle ne Allah Yana zuwa da rana daga gabas: To, ka zo da ita daga yamma." Sai aka ɗimautar da wanda yakãfirta. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne azzãlumai.
"Ātāhul-mulk" : domin Allah ya ba shi sarauta da mulki.
"Yuḥyī wa yumīt" : yana rayarwa da kashewa.
"Fabuhita" : ya rude, ya shanye, ya kasa da hujja.
Fassarar Ayar:
Shin, ya kai ka labarin wanda ya yi jayayya da Annabi Ibrahim a game da Ubangijinsa? Wannan mutum shi ne Namrud, wanda Allah ya ba shi mulki, sai ya yi girman kai da zalunci. Ya tambayi Ibrahim: "Wane ne Ubangijinka?" Ibrahim ya amsa: "Ubangijina shi ne wanda ke rayarwa kuma yana kashewa." Sai Namrud ya ce: "Ni ma ina rayarwa kuma ina kashewa." Yana nufin cewa: ina kashe wanda na so, ina kuma barin wanda na so ya rayu. Sai Ibrahim ya kawo masa hujja mafi karfi, ya ce masa: "To, lalle ne Allah yana kawo rana daga gabas, to kai ka kawo ta daga yamma." A nan Namrud ya kasa, ya rude, ya shanye, hujjarsa ta karye. Kuma Allah ba ya shiryar da mutane masu zalunci zuwa ga gaskiya, saboda zaluncinsu da girman kai.
Fa’idojin Ayar:
Imani da cewa Allah shi kaɗai ne Mai rayarwa da kashewa, kuma babu wani halitta da ke da wannan ikon.
Nuna girman hikimar Annabi Ibrahim wajen yin hujja da kyakkyawar hanya, inda ya canza daga wata hujja zuwa wata mafi bayyanawa.
Kashedi ga masu girman kai da mulki cewa duk wani zalunci zai kai ga rashin shiryayya da Allah.
Ƙarfafa imani cewa Allah yana taimakon masu gaskiya, kuma yana baiwa annabawa nasara a kan magabata.
Nuna cewa hujja mai haske tana rinjayar da maƙiya, amma masu zuciya mai cike da girman kai ba su amfana da ita.
Shin, ba ka gani ba zuwa ga wanda ya yi hujjatayya da Ibrãhĩm a cikin (al'amarin) Ubangijinsa dõmin Allah Yã bã shi mulki, a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: "Ubangijina Shi ne Wanda Yake rãyawa kuma Yana matarwa." Ya ce: "Nĩ ina rãyarwa kuma ina matarwa." Ibrãhĩm ya ce: "To, lalle ne Allah Yana zuwa da rana daga gabas: To, ka zo da ita daga yamma." Sai aka ɗimautar da wanda yakãfirta. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne azzãlumai.
Bãbu tĩlastãwa a cikin addini, haƙĩƙa shiriya tã bayyana daga ɓata; Sabõda haka wanda ya kãfirta da ¦ãgũta kuma ya yi ĩmãni da Allah, to, haƙĩƙa, yã yi riƙo ga igiya amintacciya, bãbu yankẽwa agare ta. Kuma Allah Mai ji ne, Masani.
Allah Shi ne Masõyin waɗanda suka yi ĩmãni; Yana fitar da su daga duffai zuwa ga haske, kuma waɗanda suka kãfirta, masõyansu ¦ãgũtu ne; suna fitar da su daga haske zuwa ga duffai. Waɗannan abokan Wuta ne, sũ a cikinta madawwama ne.
Shin, ba ka gani ba zuwa ga wanda ya yi hujjatayya da Ibrãhĩm a cikin (al'amarin) Ubangijinsa dõmin Allah Yã bã shi mulki, a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: "Ubangijina Shi ne Wanda Yake rãyawa kuma Yana matarwa." Ya ce: "Nĩ ina rãyarwa kuma ina matarwa." Ibrãhĩm ya ce: "To, lalle ne Allah Yana zuwa da rana daga gabas: To, ka zo da ita daga yamma." Sai aka ɗimautar da wanda yakãfirta. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne azzãlumai.
Kõ kuwa wanda ya shũɗe a kan wata alƙarya, alhãli kuwa tana wõfintacciya a kan gadãjen rẽsunanta. Ya ce: "Yaya Allah zai rãyar da wannan a bãyan mutuwarta." Sai Allah Ya matar da shi, shẽkara ɗari; sa'an nankuma ya tãyar da shi. Ya ce: "Nawa ka zauna?" Ya ce: "Na zauna yini ɗaya ko kuwa rabin yini." Ya ce: "A'a kã zauna shẽkara ɗari." To, ka dũba zuwa ga abincinka, da abin shanka, (kõwanensu) bai sãke ba, kuma ka dũba zuwa ga jãkinka, kuma dõmin Mu sanya ka wata ãyã ga mutãne. Kuma ka duba zuwa ga ƙasũsuwa yadda Muke mõtsarda su sa'an nan kuma Mu tufãtar da su, da nãma", To, a lõkacin da (abin) ya bayyana a gare shi, ya ce: "Ina sanin cẽwa lalle Allah a kan dukan kõme Mai ĩkõn yi ne."
Kuma a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: "Ya Ubangijina! Ka nũna mini yadda Kake rãyar da matattu." Ya ce: "Shin, kuma ba ka yi ĩmãni ba?" Ya ce: "Na'am! Kuma amma dõmin zũciyãta, ta natsu." Ya ce: "To ka riƙi huɗu daga tsuntsãye, ka karkatar da su zuwa gare ka, ka yanka su, sa'an nan kuma ka sanya juzu'i daga gare su a kan kõwane dũtse, sa'an nan kuma ka kira su zã su zo maka gudãne. Kuma ka sani cẽwa lalle Allah Mabuwãyi ne, Masani."
SurahQuran.com was founded as a humble effort to serve the Noble Book and the pure Sunnah, to invite people to Allah, and to make the religious sciences accessible according to the methodology of the Quran and Sunnah. We praise and thank Allah for His grace, and we ask Him to accept our work and make it sincere for His noble Face.