Kuma a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: "Ya Ubangijina! Ka nũna mini yadda Kake rãyar da matattu." Ya ce: "Shin, kuma ba ka yi ĩmãni ba?" Ya ce: "Na'am! Kuma amma dõmin zũciyãta, ta natsu." Ya ce: "To ka riƙi huɗu daga tsuntsãye, ka karkatar da su zuwa gare ka, ka yanka su, sa'an nan kuma ka sanya juzu'i daga gare su a kan kõwane dũtse, sa'an nan kuma ka kira su zã su zo maka gudãne. Kuma ka sani cẽwa lalle Allah Mabuwãyi ne, Masani."
فَصُرْهُنَّ إِلَيْكَ: Ka tattara su zuwa gare ka, sa’an nan ka yanka su ka gutsuttsura su.
ثُمَّ اجْعَلْ عَلَى كُلِّ جَبَلٍ مِنْهُنَّ جُزْءًا: Sa’an nan ka dora wani yanki daga cikin naman su a kan kowane dutse.
سَعْيًا: Suna zuwa da sauri.
Tafsirin Ayar:
Ka tuna, ya Manzo, lokacin da Annabi Ibrahim ya ce: “Ya Ubangijina! Ka nuna mini yadda kake rayar da matattu.” Allah ya ce masa: “Ashe, ba ka yi imani ba?” Ibrahim ya ce: “Na yi imani, amma ina so in ga abin da na yi imani da shi da idona don zuciyata ta natsu da kwanciyar hankali.” Sai Allah ya umarce shi da ya kama tsuntsaye huɗu, ya tattara su, ya yanka su, ya gutsuttsura su, sa’an nan ya dora wani yanki daga cikin su a kan kowane dutse a kewayensa, sa’an nan ya kira su. Da ya kira su, sai Allah ya rayar da su, kowane yanki ya koma wurinsa, suka zo masa da sauri. A ƙarshen ayar, Allah ya gaya wa Ibrahim cewa: “Ka sani cewa Allah Mai iko ne, babu abin da ya gagara, kuma Mai hikima ne a cikin dukan abin da ya yi da umarninsa da halittarsa.”
Wannan lamari ya nuna cewa Annabi Ibrahim ya kasance mai cikakken imani, amma ya so ya ƙara wa zuciyarsa natsuwa ta hanyar gani da ido, domin imani ya tashi daga ilmin tabbaci zuwa ganin tabbaci. Allah ya karɓi buƙatarsa kuma ya nuna masa wannan al’ajabi mai girma domin ya tabbatar masa da ikon Allah na rayar da matattu.
Fa’idodin Darasi:
Imani ba ya hana neman ƙarin tabbaci da natsuwar zuciya ba, domin hakan yana ƙara wa mutum yakini da kwanciyar hankali.
Allah yana jin yabon bayinsa kuma yana karɓar addu’o’insu, musamman idan sun kasance da niyyar neman ilimi da tabbaci.
Ƙarfin Allah babu iyaka, kuma rayar da matattu abu ne mai sauƙi a gare shi, don haka ya kamata mu ƙara dogaro gare shi a cikin dukan al’amuranmu.
Neman ilimi da fahimtar addini abu ne da Allah yake so, kuma yana ɗaga darajar bawa a gare shi.
Wannan ayar tana ƙarfafa mu mu yi tunani a kan halittar Allah da ikonsa, domin hakan yana ƙara mana imani da godiya.
Kuma a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: "Ya Ubangijina! Ka nũna mini yadda Kake rãyar da matattu." Ya ce: "Shin, kuma ba ka yi ĩmãni ba?" Ya ce: "Na'am! Kuma amma dõmin zũciyãta, ta natsu." Ya ce: "To ka riƙi huɗu daga tsuntsãye, ka karkatar da su zuwa gare ka, ka yanka su, sa'an nan kuma ka sanya juzu'i daga gare su a kan kõwane dũtse, sa'an nan kuma ka kira su zã su zo maka gudãne. Kuma ka sani cẽwa lalle Allah Mabuwãyi ne, Masani."
Shin, ba ka gani ba zuwa ga wanda ya yi hujjatayya da Ibrãhĩm a cikin (al'amarin) Ubangijinsa dõmin Allah Yã bã shi mulki, a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: "Ubangijina Shi ne Wanda Yake rãyawa kuma Yana matarwa." Ya ce: "Nĩ ina rãyarwa kuma ina matarwa." Ibrãhĩm ya ce: "To, lalle ne Allah Yana zuwa da rana daga gabas: To, ka zo da ita daga yamma." Sai aka ɗimautar da wanda yakãfirta. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne azzãlumai.
Kõ kuwa wanda ya shũɗe a kan wata alƙarya, alhãli kuwa tana wõfintacciya a kan gadãjen rẽsunanta. Ya ce: "Yaya Allah zai rãyar da wannan a bãyan mutuwarta." Sai Allah Ya matar da shi, shẽkara ɗari; sa'an nankuma ya tãyar da shi. Ya ce: "Nawa ka zauna?" Ya ce: "Na zauna yini ɗaya ko kuwa rabin yini." Ya ce: "A'a kã zauna shẽkara ɗari." To, ka dũba zuwa ga abincinka, da abin shanka, (kõwanensu) bai sãke ba, kuma ka dũba zuwa ga jãkinka, kuma dõmin Mu sanya ka wata ãyã ga mutãne. Kuma ka duba zuwa ga ƙasũsuwa yadda Muke mõtsarda su sa'an nan kuma Mu tufãtar da su, da nãma", To, a lõkacin da (abin) ya bayyana a gare shi, ya ce: "Ina sanin cẽwa lalle Allah a kan dukan kõme Mai ĩkõn yi ne."
Kuma a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: "Ya Ubangijina! Ka nũna mini yadda Kake rãyar da matattu." Ya ce: "Shin, kuma ba ka yi ĩmãni ba?" Ya ce: "Na'am! Kuma amma dõmin zũciyãta, ta natsu." Ya ce: "To ka riƙi huɗu daga tsuntsãye, ka karkatar da su zuwa gare ka, ka yanka su, sa'an nan kuma ka sanya juzu'i daga gare su a kan kõwane dũtse, sa'an nan kuma ka kira su zã su zo maka gudãne. Kuma ka sani cẽwa lalle Allah Mabuwãyi ne, Masani."
Sifar waɗanda suke ciyar da dũkiyõyinsu a cikin hanyar Allah, kamar sifar ƙwãyã ce wadda ta tsirar da zangarniya bakwai, a cikin kõwace zangarniya akwai ƙwãya ɗari. Kuma Allah Yana riɓinyawa ga wanda Ya so. Kuma Allah Mawadãci ne, Masani.
Waɗanda suke ciyar da dũkiyõyinsu a cikin hanyar Allah, sa'an nan kuma bã su biyar wa abin da suka ciyar ɗin da gõri, ko cũta, suna da sakamakonsu a wurin ubangijinsu, kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna baƙin ciki ba.
SurahQuran.com was founded as a humble effort to serve the Noble Book and the pure Sunnah, to invite people to Allah, and to make the religious sciences accessible according to the methodology of the Quran and Sunnah. We praise and thank Allah for His grace, and we ask Him to accept our work and make it sincere for His noble Face.