وَالنَّازِعَاتِ غَرْقًا(1) Ina rantsuwa da mala'iku mãsu fisgar rãyuka (na kafirai) da ƙarfi. |
وَالنَّاشِطَاتِ نَشْطًا(2) Da mãsu ɗibar rãyuka (na mũminai) da sauƙi a cikin nishãɗi. |
وَالسَّابِحَاتِ سَبْحًا(3) Da mãsu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo. |
فَالسَّابِقَاتِ سَبْقًا(4) Sa'an nan, su zama mãsu gaugãwa (da umurnin Allah) kamar suna tsẽre. |
فَالْمُدَبِّرَاتِ أَمْرًا(5) Sa, an nan, su kasance masu shirya gudanar da umurni. |
يَوْمَ تَرْجُفُ الرَّاجِفَةُ(6) Rãnar da mai girgiza abũbuwa (bũsar farko) zã ta kaɗa. |
تَتْبَعُهَا الرَّادِفَةُ(7) Mai biyar ta (bũsa ta biyu) nã biye. |
قُلُوبٌ يَوْمَئِذٍ وَاجِفَةٌ(8) Wasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne. |
أَبْصَارُهَا خَاشِعَةٌ(9) Alhãli idãnunsu na ƙasƙantattu. |
يَقُولُونَ أَإِنَّا لَمَرْدُودُونَ فِي الْحَافِرَةِ(10) Sunã cẽwa "Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu? |
أَإِذَا كُنَّا عِظَامًا نَّخِرَةً(11) "Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu?" |
قَالُوا تِلْكَ إِذًا كَرَّةٌ خَاسِرَةٌ(12) Suka ce: "Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya!" |
فَإِنَّمَا هِيَ زَجْرَةٌ وَاحِدَةٌ(13) To, ita kam, tsãwa guda kawai ce. |
فَإِذَا هُم بِالسَّاهِرَةِ(14) Sai kawai gã su a bãyan ƙasa. |
هَلْ أَتَاكَ حَدِيثُ مُوسَىٰ(15) Shin, lãbãrin Mũsã ya zo maka? |
إِذْ نَادَاهُ رَبُّهُ بِالْوَادِ الْمُقَدَّسِ طُوًى(16) A lõkacin da Ubangijinsa Ya kirãye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwã? |
اذْهَبْ إِلَىٰ فِرْعَوْنَ إِنَّهُ طَغَىٰ(17) Ka tafi zuwa ga Fir'auna, lalle ne shi, ya ƙẽtare haddi. |
فَقُلْ هَل لَّكَ إِلَىٰ أَن تَزَكَّىٰ(18) "Sai ka ce masa, Kõ zã ka so ka tsarkaka. |
وَأَهْدِيَكَ إِلَىٰ رَبِّكَ فَتَخْشَىٰ(19) "Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoronSa?" |
فَأَرَاهُ الْآيَةَ الْكُبْرَىٰ(20) Sai ya nũna masa ãyar nan mafi girma. |
فَكَذَّبَ وَعَصَىٰ(21) Sai ya ƙaryata, kuma ya sãɓa (umurni), |
ثُمَّ أَدْبَرَ يَسْعَىٰ(22) Sa'an nan ya jũya bãya, yanã tafiya da sauri. |
فَحَشَرَ فَنَادَىٰ(23) Sai ya yi gayya, sa'an nan ya yi kira. |
فَقَالَ أَنَا رَبُّكُمُ الْأَعْلَىٰ(24) Sai ya ce: "Nĩ ne Ubangijinku mafi ɗaudaka." |
فَأَخَذَهُ اللَّهُ نَكَالَ الْآخِرَةِ وَالْأُولَىٰ(25) Sabõda haka Allah Ya kama shi, dõmin azãbar maganar ƙarshe da ta farko. |
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَعِبْرَةً لِّمَن يَخْشَىٰ(26) Lalle ne, a cikin wannan haƙiƙa akwai abin kula ga wanda yake tsõron Allah. |
أَأَنتُمْ أَشَدُّ خَلْقًا أَمِ السَّمَاءُ ۚ بَنَاهَا(27) Shin, kũ ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta. |
رَفَعَ سَمْكَهَا فَسَوَّاهَا(28) Ya ɗaukaka rufinta, sa'an nan Ya daidaita ta. |
وَأَغْطَشَ لَيْلَهَا وَأَخْرَجَ ضُحَاهَا(29) Kuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta. |
وَالْأَرْضَ بَعْدَ ذَٰلِكَ دَحَاهَا(30) Kuma, ƙasa a bayan haka Ya mulmula ta. |
أَخْرَجَ مِنْهَا مَاءَهَا وَمَرْعَاهَا(31) Ya fitar da ruwanta daga gare ta da makiyãyarta. |
وَالْجِبَالَ أَرْسَاهَا(32) Da duwatsu, Yã kafe ta. |
مَتَاعًا لَّكُمْ وَلِأَنْعَامِكُمْ(33) Domin jiyarwa dãɗi a gare ku, kuma ga dabbõbinku. |
فَإِذَا جَاءَتِ الطَّامَّةُ الْكُبْرَىٰ(34) To, idan uwar masĩfu, mafi girma, ta zo. |
يَوْمَ يَتَذَكَّرُ الْإِنسَانُ مَا سَعَىٰ(35) Rãnar da mutum zai yi tunãnin abin da ya aikata. |
وَبُرِّزَتِ الْجَحِيمُ لِمَن يَرَىٰ(36) Kuma, a bayyana Jahĩm ga mai gani. |
فَأَمَّا مَن طَغَىٰ(37) To, amma wanda ya yi girman kai. |
وَآثَرَ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا(38) Kuma, ya zãɓi rãyuwa ta kusa, (wato dũniya). |
فَإِنَّ الْجَحِيمَ هِيَ الْمَأْوَىٰ(39) To, lalle ne Jahĩm, ita ce makõma. |
وَأَمَّا مَنْ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِ وَنَهَى النَّفْسَ عَنِ الْهَوَىٰ(40) Kuma, amma wanda ya ji tsõron tsayi a gaba ga Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai. |
فَإِنَّ الْجَنَّةَ هِيَ الْمَأْوَىٰ(41) To, lalle ne Aljanna ita ce makõma. |
يَسْأَلُونَكَ عَنِ السَّاعَةِ أَيَّانَ مُرْسَاهَا(42) Sunã tambayar ka game da sa'a, wai yaushe ne matabbatarta? |
فِيمَ أَنتَ مِن ذِكْرَاهَا(43) Me ya haɗã ka da ambatonta? |
إِلَىٰ رَبِّكَ مُنتَهَاهَا(44) Zuwa ga Ubangijinka ƙarshen al'amarinta yake. |
إِنَّمَا أَنتَ مُنذِرُ مَن يَخْشَاهَا(45) Kai mai gargaɗi kawai ne ga mai tsõron ta. |
كَأَنَّهُمْ يَوْمَ يَرَوْنَهَا لَمْ يَلْبَثُوا إِلَّا عَشِيَّةً أَوْ ضُحَاهَا(46) Kamar sũ a rãnar da zã su gan ta, ba su zauna ba fãce a lõkacin marẽce ko hantsinsa. |