Fa in tallaqahaa falaa tahillu lahoo mim ba`du hattaa tankiha zawjan ghairah; fa in tallaqahaa falaa junaaha `alaihimaaa ai yataraaja`aaa in zannaaa ai yuqeemaa hudoodal laa; wa tilka hudoodul laahi yubaiyinuhaa liqawminy ya`lamoon
📖 Fassara (Da Hausa)
📖 Da Hausa
Sa'an nan idan ya sake ta (na uku), to, bã ta halatta a gare shi, daga bãya, sai tã yi jima'i da wani miji waninsa. Sa'an nan idan (sãbon mijin, watau na biyu) ya sake ta, to, bãbu laifi a kansu ga su kõma wa (auren) jũna, idan sun (mijin farko da matar) yi zaton cẽwa zã su tsayar da iyãkõkin Allah, kuma waɗancan dõkõkin Allah ne Yana bayyana su ga mutãne waɗanda suke sani.
"Fain tallaqaha": Idan mijin ya sake ta (a karo na uku).
"Fala tahillu lahu min ba’du": Ba ta halatta a gare shi ba bayan wannan saki.
"Hatta tankiha zaujan ghayrahu": Sai ta auri wani miji dabam da shi.
"Fain tallaqaha": Idan mijin na biyu ya sake ta.
"Yataraja’a": Su koma ga juna (da aure).
"Yaqima hududallah": Su tsai da iyakokin Allah (dokokin aure).
Fassarar Ayar:
Idan mijin ya sake matarsa a karo na uku (saki na uku), to ba ta halatta a gare shi ba har sai ta auri wani miji dabam da shi, auren da yake na gaske kuma mai cikakkiyar niyya, ba don neman halatta mata komawa ga mijinta na farko ba. Kuma dole ne a sadu da ita a cikin wannan aure (a kwana da ita). Idan mijin na biyu ya sake ta, ko kuma ya rasu ya bar ta, bayan ta gama idda, to babu laifi a kan matar da mijinta na farko su koma ga juna da sabon aure da sabon sadaki, idan sun yi tunanin cewa za su iya tsai da dokokin Allah da ya shimfida game da aure. Waɗannan su ne iyakokin Allah da ya bayyana ga mutanen da suke da ilimi da fahimta, domin su ne masu amfana da waɗannan dokokin.
Fa’idodin Ayar:
Wannan ayar tana koyar da mu cewa Musulunci ya sanya tsari mai kyau ga rayuwar iyali, don kada saki ya zama abin wasa da sake komawa ba tare da wani dalili ba.
Tana nuna mana cewa Allah yana son zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin ma’aurata, don haka ya sanya waɗannan sharudda don kare mutuncin mace da kuma darajar aure.
Tana ƙarfafa mu mu riƙe dokokin Allah da iyakokinsa, domin waɗanda suke da ilimi ne kawai suke fahimtar hikimomin waɗannan dokoki da kuma amfaninsu.
Tana nuna cewa komawa ga juna bayan saki na uku ba abu ne mai sauƙi ba, don haka ya kamata ma’aurata su yi tunani sosai kafin su yanke shawarar saki, domin su kiyaye iyalansu daga rushewa.
Sa'an nan idan ya sake ta (na uku), to, bã ta halatta a gare shi, daga bãya, sai tã yi jima'i da wani miji waninsa. Sa'an nan idan (sãbon mijin, watau na biyu) ya sake ta, to, bãbu laifi a kansu ga su kõma wa (auren) jũna, idan sun (mijin farko da matar) yi zaton cẽwa zã su tsayar da iyãkõkin Allah, kuma waɗancan dõkõkin Allah ne Yana bayyana su ga mutãne waɗanda suke sani.
Kuma mãtã waɗanda aka saki aurensu, suna jinkiri da kansu tsarki uku. Kuma bã ya halatta a gare su, su ɓõye abin da Allah Ya halitta a cikin mahaifunsu, idan sun kasance suna yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Kuma mazan aurensu su ne mafiya haƙƙi ga mayar da su a cikin wancan, idan sun yi nufin gyãrawa. Kuma sũ mãtan suna da kamar abin da yake a kansu, yadda aka sani. Kuma maza suna da wata daraja a kansu (su mãtan). Kuma Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.
Saki sau biyu yake, sai a riƙa da alh ẽri, ko kuwa a sallama bisa kyautatãwa. Kuma ba ya halatta a gare ku (maza) ku karɓe wani abu daga abin da kuka bã su, fãce fa idan su (ma'auran) na tsõron bã zã su tsayar da iyãkõkin Allah ba, Idan kun (danginsu) ji tsõron bã zã su tsayar da iyãkõkin Allah ba, to, bãbu laifi a kansu a cikin abin da ta yi fansa da shi. Waɗancan iyãkõkin Allah ne sabõda haka kada ku kẽtare su. Kuma wanda ya ƙẽtare iyãkõkin Allah, to waɗannan su ne azzãlumai.
Sa'an nan idan ya sake ta (na uku), to, bã ta halatta a gare shi, daga bãya, sai tã yi jima'i da wani miji waninsa. Sa'an nan idan (sãbon mijin, watau na biyu) ya sake ta, to, bãbu laifi a kansu ga su kõma wa (auren) jũna, idan sun (mijin farko da matar) yi zaton cẽwa zã su tsayar da iyãkõkin Allah, kuma waɗancan dõkõkin Allah ne Yana bayyana su ga mutãne waɗanda suke sani.
Kuma idan kun saki mãta, sa'an nan suka isa ga ajalinsu (iddarsu), sai ku riƙe su da alhẽri ko ku sallame su da alhẽri, kuma kada ku riƙe su a kan cũtarwa dõmin ta tsawaita idda. Kuma wanda ya aikata wancan, to, haƙĩƙa, yã zãlunci kansa. Kuma kada ku riƙi ãyõyin Allah da izgili. Kuma ku tuna ni'imar Allah da abin da Ya saukar a kanku na Littãfi da hikima. Yana yi muku wa'azi da shi. Kuma ku bi Allah da takawa kuma ku sani cewa lalle ne Allah ga dukan kõme Masani ne.
Kuma idan kuka saki mãta, har suka isa ga ajalinsu (iddarsu), to, kada ku (waliyyansu) hana su, su auri mazansu (da suka sake su) idan sun yarda da jũna a tsakãninsu (tsõhon miji da tsõhuwar mãta) da alhẽri. Wancan ana yin wa'azi da shi ga wanda ya kasance daga gare ku yana ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Wancan ne mafi mutunci a gare ku, kuma mafi tsarki. Kuma Allah Yana sani, kuma kũ ba ku sani ba.
SurahQuran.com was founded as a humble effort to serve the Noble Book and the pure Sunnah, to invite people to Allah, and to make the religious sciences accessible according to the methodology of the Quran and Sunnah. We praise and thank Allah for His grace, and we ask Him to accept our work and make it sincere for His noble Face.