PDF —
50 Aya Meccan PDF
Built right in your browser — download starts automatically

Surah Al-Mursalat pdf — Sauke (Hausa)

Surah Al-Mursalat pdf Hausa — Sauke Surah Al-Mursalat Fassara. Surah Al-Mursalat (Meccan) 50 Aya.

← Al-InsanSurah Al-Mursalat An-Naba →


50 Aya · Meccan · Hausa
bismillah
ﮑﮒﮓ
77:1 Ina rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna.
ﮔﮕﮖ
77:2 Sa'an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi.
ﮗﮘﮙ
77:3 Kuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa.
ﮚﮛﮜ
77:4 sa'an nan, da ãyõyi mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa.
ﮝﮞﮟ
77:5 Sa'an nan da malã'iku mãsu jẽfa tunãtarwa ga Manzanni.
ﮠﮡﮢﮣ
77:6 Domin yanke hamzari ko dõmin gargadi.
ﮤﮥﮦﮧ
77:7 Lalle ne, abin da ake yi muku wa'adi da shi tabbas mai aukuwa ne
ﮨﮩﮪﮫ
77:8 To, idan taurãri aka shãfe haskensu.
ﮬﮭﮮﮯ
77:9 Kuma, idan sama aka tsãge ta.
ﮰﮱﯓﯔ
77:10 Kuma, idan duwãtsu aka nike su.
ﯕﯖﯗﯘ
77:11 Kuma, idan manzanni aka ƙayyade lõkacin tãra su.
ﯙﯚﯛﯜ
77:12 Domin babbar rãnar da aka yi wa ajali.
ﯝﯞﯟ
77:13 Domin rãnar rarrabẽwa.
ﯠﯡﯢﯣﯤﯥ
77:14 Kuma, me ya sanar da kai rãnar rarrabẽwa?
ﯦﯧﯨﯩ
77:15 Bone yã tabbata a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
ﯪﯫﯬﯭ
77:16 Ashe, ba Mu halakar da (mãsu ƙaryatãw) na farko ba.
ﯮﯯﯰﯱ
77:17 Sa'an nan, kuma zã Mu biyar musu da na ƙarshe?
ﯲﯳﯴﯵ
77:18 Haka nan, Muke aikatãwa da mãsu yin laifi.
ﯶﯷﯸﯹ
77:19 Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!
ﭑﭒﭓﭔﭕﭖ
77:20 Ashe, ba Mu halitta ku daga wani ruwa wulakantacce ba.
ﭗﭘﭙﭚﭛ
77:21 Sa'an nan Muka sanya shi a cikin wani wurin natsuwa amintacce.
ﭜﭝﭞﭟ
77:22 Zuwa ga wani gwargwadon mudda sananna.
ﭠﭡﭢﭣ
77:23 Sa'an nan, Muka nũna iyãwarMu? Madalla da Mu, Mãsu nũna iyãwa.
ﭤﭥﭦﭧ
77:24 Bone ya tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!
ﭨﭩﭪﭫﭬ
77:25 Ashe, ba Mu sanya ƙasa matattarã ba.
ﭭﭮﭯ
77:26 Ga rãyayyu da matattu,
ﭰﭱﭲﭳﭴﭵﭶﭷ
77:27 Kuma, Muka sanya, a cikinta, kafaffun duwãtsu maɗaukaka, kuma Muka shayar da ku ruwa mai dãɗi?
ﭸﭹﭺﭻ
77:28 Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
ﭼﭽﭾﭿﮀﮁﮂ
77:29 Ku tafi zuwa ga abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi!
ﮃﮄﮅﮆﮇﮈﮉ
77:30 Ku tafi zuwa ga wata inuwa mai rassa uku.
ﮊﮋﮌﮍﮎﮏﮐ
77:31 Ita ba inuwar ba, kuma ba ta wadãtarwa daga harshen wuta.
ﮑﮒﮓﮔﮕ
77:32 Lalle ne, ita, tanã jifã da tartsatsi kamar sõraye.
ﮖﮗﮘﮙ
77:33 Kamar dai su raƙumma ne baƙãƙe.
ﮚﮛﮜﮝ
77:34 Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
ﮞﮟﮠﮡﮢ
77:35 Wannan, yini ne da bã zã su iya yin magana ba.
ﮣﮤﮥﮦﮧ
77:36 Bã zã a yi musu izni ba, balle su kãwo hanzari.
ﮨﮩﮪﮫ
77:37 Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
ﮬﮭﮮﮯﮰﮱﯓ
77:38 Wannan rãnar rarrabẽwa ce, Mun tattara ku tare da mutãnen farko.
ﯔﯕﯖﯗﯘﯙ
77:39 To, idan akwai wata dabara gare ku, sai ku yi ma Ni ita.
ﯚﯛﯜﯝ
77:40 Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
ﯞﯟﯠﯡﯢﯣ
77:41 Lalle ne, mãsu taƙawa suna a cikin inuwõwi da marẽmari.
ﯤﯥﯦﯧ
77:42 Da wasu 'ya'yan itãce irin waɗanda suke marmari.
ﯨﯩﯪﯫﯬﯭﯮ
77:43 (A ce musu) "Ku ci ku sha cikin ni'ima sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa."
ﯯﯰﯱﯲﯳ
77:44 Lalle ne, Mũ haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
ﯴﯵﯶﯷ
77:45 Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
ﯸﯹﯺﯻﯼﯽ
77:46 (Ana ce musu) "Ku ci ku ji ɗan dãdi kaɗan, lalle ne dai ku mãsu laifi ne."
ﯾﯿﰀﰁ
77:47 Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
ﰂﰃﰄﰅﰆﰇﰈ
77:48 Kuma, idan an ce musu: "Ku yi rukũ'i; bã zã su yi rukũ'in (salla) ba."
ﰉﰊﰋﰌ
77:49 Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
ﰍﰎﰏﰐﰑ
77:50 To, da wane lãbãri (Littãfi), waninsa (Alƙur'ãni) zã su yi ĩmãni

Al-Kur'ani


Wednesday, September 9, 2026

Don't forget us in your sincere prayers