وَالْمُرْسَلَاتِ عُرْفًا(1) Ina rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna. |
فَالْعَاصِفَاتِ عَصْفًا(2) Sa'an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi. |
وَالنَّاشِرَاتِ نَشْرًا(3) Kuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa. |
فَالْفَارِقَاتِ فَرْقًا(4) sa'an nan, da ãyõyi mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa. |
فَالْمُلْقِيَاتِ ذِكْرًا(5) Sa'an nan da malã'iku mãsu jẽfa tunãtarwa ga Manzanni. |
عُذْرًا أَوْ نُذْرًا(6) Domin yanke hamzari ko dõmin gargadi. |
إِنَّمَا تُوعَدُونَ لَوَاقِعٌ(7) Lalle ne, abin da ake yi muku wa'adi da shi tabbas mai aukuwa ne |
فَإِذَا النُّجُومُ طُمِسَتْ(8) To, idan taurãri aka shãfe haskensu. |
وَإِذَا السَّمَاءُ فُرِجَتْ(9) Kuma, idan sama aka tsãge ta. |
وَإِذَا الْجِبَالُ نُسِفَتْ(10) Kuma, idan duwãtsu aka nike su. |
وَإِذَا الرُّسُلُ أُقِّتَتْ(11) Kuma, idan manzanni aka ƙayyade lõkacin tãra su. |
لِأَيِّ يَوْمٍ أُجِّلَتْ(12) Domin babbar rãnar da aka yi wa ajali. |
لِيَوْمِ الْفَصْلِ(13) Domin rãnar rarrabẽwa. |
وَمَا أَدْرَاكَ مَا يَوْمُ الْفَصْلِ(14) Kuma, me ya sanar da kai rãnar rarrabẽwa? |
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ(15) Bone yã tabbata a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! |
أَلَمْ نُهْلِكِ الْأَوَّلِينَ(16) Ashe, ba Mu halakar da (mãsu ƙaryatãw) na farko ba. |
ثُمَّ نُتْبِعُهُمُ الْآخِرِينَ(17) Sa'an nan, kuma zã Mu biyar musu da na ƙarshe? |
كَذَٰلِكَ نَفْعَلُ بِالْمُجْرِمِينَ(18) Haka nan, Muke aikatãwa da mãsu yin laifi. |
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ(19) Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa! |
أَلَمْ نَخْلُقكُّم مِّن مَّاءٍ مَّهِينٍ(20) Ashe, ba Mu halitta ku daga wani ruwa wulakantacce ba. |
فَجَعَلْنَاهُ فِي قَرَارٍ مَّكِينٍ(21) Sa'an nan Muka sanya shi a cikin wani wurin natsuwa amintacce. |
إِلَىٰ قَدَرٍ مَّعْلُومٍ(22) Zuwa ga wani gwargwadon mudda sananna. |
فَقَدَرْنَا فَنِعْمَ الْقَادِرُونَ(23) Sa'an nan, Muka nũna iyãwarMu? Madalla da Mu, Mãsu nũna iyãwa. |
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ(24) Bone ya tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa! |
أَلَمْ نَجْعَلِ الْأَرْضَ كِفَاتًا(25) Ashe, ba Mu sanya ƙasa matattarã ba. |
أَحْيَاءً وَأَمْوَاتًا(26) Ga rãyayyu da matattu, |
وَجَعَلْنَا فِيهَا رَوَاسِيَ شَامِخَاتٍ وَأَسْقَيْنَاكُم مَّاءً فُرَاتًا(27) Kuma, Muka sanya, a cikinta, kafaffun duwãtsu maɗaukaka, kuma Muka shayar da ku ruwa mai dãɗi? |
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ(28) Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! |
انطَلِقُوا إِلَىٰ مَا كُنتُم بِهِ تُكَذِّبُونَ(29) Ku tafi zuwa ga abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi! |
انطَلِقُوا إِلَىٰ ظِلٍّ ذِي ثَلَاثِ شُعَبٍ(30) Ku tafi zuwa ga wata inuwa mai rassa uku. |
لَّا ظَلِيلٍ وَلَا يُغْنِي مِنَ اللَّهَبِ(31) Ita ba inuwar ba, kuma ba ta wadãtarwa daga harshen wuta. |
إِنَّهَا تَرْمِي بِشَرَرٍ كَالْقَصْرِ(32) Lalle ne, ita, tanã jifã da tartsatsi kamar sõraye. |
كَأَنَّهُ جِمَالَتٌ صُفْرٌ(33) Kamar dai su raƙumma ne baƙãƙe. |
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ(34) Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! |
هَٰذَا يَوْمُ لَا يَنطِقُونَ(35) Wannan, yini ne da bã zã su iya yin magana ba. |
وَلَا يُؤْذَنُ لَهُمْ فَيَعْتَذِرُونَ(36) Bã zã a yi musu izni ba, balle su kãwo hanzari. |
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ(37) Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! |
هَٰذَا يَوْمُ الْفَصْلِ ۖ جَمَعْنَاكُمْ وَالْأَوَّلِينَ(38) Wannan rãnar rarrabẽwa ce, Mun tattara ku tare da mutãnen farko. |
فَإِن كَانَ لَكُمْ كَيْدٌ فَكِيدُونِ(39) To, idan akwai wata dabara gare ku, sai ku yi ma Ni ita. |
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ(40) Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! |
إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي ظِلَالٍ وَعُيُونٍ(41) Lalle ne, mãsu taƙawa suna a cikin inuwõwi da marẽmari. |
وَفَوَاكِهَ مِمَّا يَشْتَهُونَ(42) Da wasu 'ya'yan itãce irin waɗanda suke marmari. |
كُلُوا وَاشْرَبُوا هَنِيئًا بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ(43) (A ce musu) "Ku ci ku sha cikin ni'ima sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa." |
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ(44) Lalle ne, Mũ haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. |
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ(45) Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! |
كُلُوا وَتَمَتَّعُوا قَلِيلًا إِنَّكُم مُّجْرِمُونَ(46) (Ana ce musu) "Ku ci ku ji ɗan dãdi kaɗan, lalle ne dai ku mãsu laifi ne." |
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ(47) Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! |
وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ارْكَعُوا لَا يَرْكَعُونَ(48) Kuma, idan an ce musu: "Ku yi rukũ'i; bã zã su yi rukũ'in (salla) ba." |
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ(49) Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! |
فَبِأَيِّ حَدِيثٍ بَعْدَهُ يُؤْمِنُونَ(50) To, da wane lãbãri (Littãfi), waninsa (Alƙur'ãni) zã su yi ĩmãni |