PDF —
19 Aya Meccan PDF
Built right in your browser — download starts automatically

Surah Al-Infitar pdf — Sauke (Hausa)

Surah Al-Infitar pdf Hausa — Sauke Surah Al-Infitar Fassara. Surah Al-Infitar (Meccan) 19 Aya.



19 Aya · Meccan · Hausa
bismillah
ﭑﭒﭓﭔ
82:1 Idan sama ta tsãge.
ﭕﭖﭗﭘ
82:2 Kuma idan taurãri suka wãtse.
ﭙﭚﭛﭜ
82:3 Kuma idan tẽkuna aka facce su.
ﭝﭞﭟﭠ
82:4 Kuma idan kaburbura aka tõne su.
ﭡﭢﭣﭤﭥﭦ
82:5 Rai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar.
ﭧﭨﭩﭪﭫﭬﭭ
82:6 Yã kai mutum! Mẽ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karimci.
ﭮﭯﭰﭱﭲ
82:7 Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka.
ﭳﭴﭵﭶﭷﭸﭹ
82:8 A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta.
ﭺﭻﭼﭽﭾ
82:9 A'aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako!
ﭿﮀﮁﮂ
82:10 Lalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara.
ﮃﮄﮅ
82:11 Mãsu daraja, marubũta.
ﮆﮇﮈﮉ
82:12 Sunã sanin abin da kuke aikatãwa.
ﮊﮋﮌﮍﮎ
82:13 Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni'ima.
ﮏﮐﮑﮒﮓ
82:14 Kuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm.
ﮔﮕﮖﮗ
82:15 Zã su shigẽ ta a rãnar sakamako.
ﮘﮙﮚﮛﮜ
82:16 Bã zã su faku daga gare ta ba.
ﮝﮞﮟﮠﮡﮢ
82:17 Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rẽnar sakamako?
ﮣﮤﮥﮦﮧﮨﮩ
82:18 Sa'an nan, mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rãnar sakamako?
ﮪﮫﮬﮭﮮﮯﮰﮱﯓﯔﯕ
82:19 Rãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al'amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake.

Al-Kur'ani


Wednesday, September 9, 2026

Don't forget us in your sincere prayers