Surah Al-Infitar Larabci da Hausa

Karanta Surah Al-Infitar tare da cikakkiyar fassarar Hausa da sauti. Fassara aya bayan aya. (19 Aya — مكية). Al-Infitar Saurara, Al-Infitar Fassara, Al-Infitar mp3, Al-Infitar pdf.

Karanta da Saurara Surah Al-Infitar

🎧 Aya
M Mishary Rashid Alafasy
M Mahmoud Khalil Al-Husary
A Abdurrahman As-Sudais
M Mohamed Siddiq Al-Minshawi
A Abdul Basit Abdul Samad
A Ali Al-Hudhaify
A Ahmed ibn Ali al-Ajamy
A Abu Bakr Ash-Shaatree
M Muhammad Ayyoub
A Abdullah Basfar
A Abdullah Al-Juhani
M Maher Al Muaiqly
x1
إِذَا السَّمَاءُ انفَطَرَتْ ۝١
📖 Fassara Aya 1
Idan sama ta tsãge.
وَإِذَا الْكَوَاكِبُ انتَثَرَتْ ۝٢
📖 Fassara Aya 2
Kuma idan taurãri suka wãtse.
وَإِذَا الْبِحَارُ فُجِّرَتْ ۝٣
📖 Fassara Aya 3
Kuma idan tẽkuna aka facce su.
وَإِذَا الْقُبُورُ بُعْثِرَتْ ۝٤
📖 Fassara Aya 4
Kuma idan kaburbura aka tõne su.
عَلِمَتْ نَفْسٌ مَّا قَدَّمَتْ وَأَخَّرَتْ ۝٥
📖 Fassara Aya 5
Rai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar.
يَا أَيُّهَا الْإِنسَانُ مَا غَرَّكَ بِرَبِّكَ الْكَرِيمِ ۝٦
📖 Fassara Aya 6
Yã kai mutum! Mẽ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karimci.
الَّذِي خَلَقَكَ فَسَوَّاكَ فَعَدَلَكَ ۝٧
📖 Fassara Aya 7
Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka.
فِي أَيِّ صُورَةٍ مَّا شَاءَ رَكَّبَكَ ۝٨
📖 Fassara Aya 8
A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta.
كَلَّا بَلْ تُكَذِّبُونَ بِالدِّينِ ۝٩
📖 Fassara Aya 9
A'aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako!
وَإِنَّ عَلَيْكُمْ لَحَافِظِينَ ۝١٠
📖 Fassara Aya 10
Lalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara.
كِرَامًا كَاتِبِينَ ۝١١
📖 Fassara Aya 11
Mãsu daraja, marubũta.
يَعْلَمُونَ مَا تَفْعَلُونَ ۝١٢
📖 Fassara Aya 12
Sunã sanin abin da kuke aikatãwa.
إِنَّ الْأَبْرَارَ لَفِي نَعِيمٍ ۝١٣
📖 Fassara Aya 13
Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni'ima.
وَإِنَّ الْفُجَّارَ لَفِي جَحِيمٍ ۝١٤
📖 Fassara Aya 14
Kuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm.
يَصْلَوْنَهَا يَوْمَ الدِّينِ ۝١٥
📖 Fassara Aya 15
Zã su shigẽ ta a rãnar sakamako.
وَمَا هُمْ عَنْهَا بِغَائِبِينَ ۝١٦
📖 Fassara Aya 16
Bã zã su faku daga gare ta ba.
وَمَا أَدْرَاكَ مَا يَوْمُ الدِّينِ ۝١٧
📖 Fassara Aya 17
Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rẽnar sakamako?
ثُمَّ مَا أَدْرَاكَ مَا يَوْمُ الدِّينِ ۝١٨
📖 Fassara Aya 18
Sa'an nan, mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rãnar sakamako?
يَوْمَ لَا تَمْلِكُ نَفْسٌ لِّنَفْسٍ شَيْئًا ۖ وَالْأَمْرُ يَوْمَئِذٍ لِّلَّهِ ۝١٩
📖 Fassara Aya 19
Rãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al'amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake.
← 81 Al-Infitar (82/114) 83 →
Karatu Surah Al-Infitar Hausa – Fassara da Audio

82الإنفطار Al-Infitar 📚 19 Aya مكية



Al-Kur'ani


Tuesday, August 18, 2026

Don't forget us in your sincere prayers