الْحَاقَّةُ(1) Kiran gaskiya! |
مَا الْحَاقَّةُ(2) Mẽne ne kiran gaskiya? |
وَمَا أَدْرَاكَ مَا الْحَاقَّةُ(3) Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽwa kiran gaskiya? |
كَذَّبَتْ ثَمُودُ وَعَادٌ بِالْقَارِعَةِ(4) Samũdãwa da Ãdãwa sun ƙaryatar da kiran gaskiya mai dũkar zũciya! |
فَأَمَّا ثَمُودُ فَأُهْلِكُوا بِالطَّاغِيَةِ(5) To, amma Samũdãwa to, an halakãsu da tsãwa mai tsanani. |
وَأَمَّا عَادٌ فَأُهْلِكُوا بِرِيحٍ صَرْصَرٍ عَاتِيَةٍ(6) Kuma amma Ãdãwa to, an halaka su da wata iska mai tsananin sauti wadda ta ƙẽtare haddi. |
سَخَّرَهَا عَلَيْهِمْ سَبْعَ لَيَالٍ وَثَمَانِيَةَ أَيَّامٍ حُسُومًا فَتَرَى الْقَوْمَ فِيهَا صَرْعَىٰ كَأَنَّهُمْ أَعْجَازُ نَخْلٍ خَاوِيَةٍ(7) (Allah) Ya hõre ta a kansu a cikin dare bakwai da yini takwas, biye da jũna, sabõda haka, kana ganin mutãne a cikinta kwance. Kamar sũ ƙirãruwan dabĩno ne, waɗanda suka fãɗi. |
فَهَلْ تَرَىٰ لَهُم مِّن بَاقِيَةٍ(8) To, kõ kanã ganin abin da ya yi saurã daga cikinsu? |
وَجَاءَ فِرْعَوْنُ وَمَن قَبْلَهُ وَالْمُؤْتَفِكَاتُ بِالْخَاطِئَةِ(9) Kuma Fir'auna yã zo da waɗanda ke gabãninsa, da waɗannan da aka kife ƙasarsu, sabõda laifi. |
فَعَصَوْا رَسُولَ رَبِّهِمْ فَأَخَذَهُمْ أَخْذَةً رَّابِيَةً(10) Dõmin sun sãɓã wa manzon Ubangijinsu, sabõda haka ya kãmã su da wani irin kãmu mai ƙãruwar (tsanani). |
إِنَّا لَمَّا طَغَى الْمَاءُ حَمَلْنَاكُمْ فِي الْجَارِيَةِ(11) Lalle ne, Mũ, a lõkacin da ruwa ya ƙẽtare haddi, Munɗauke aaku a cikin jirgin ruwan nan. |
لِنَجْعَلَهَا لَكُمْ تَذْكِرَةً وَتَعِيَهَا أُذُنٌ وَاعِيَةٌ(12) Dõmin Mu sanya shi, gare ku abin tunãwa kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye (shi). |
فَإِذَا نُفِخَ فِي الصُّورِ نَفْخَةٌ وَاحِدَةٌ(13) To, idan an yi bũsa a cikin ƙaho, bũsa ɗaya. |
وَحُمِلَتِ الْأَرْضُ وَالْجِبَالُ فَدُكَّتَا دَكَّةً وَاحِدَةً(14) Kuma aka ɗauki ƙasa da duwãtsu, kuma aka niƙa su niƙãwa ɗaya. |
فَيَوْمَئِذٍ وَقَعَتِ الْوَاقِعَةُ(15) A ran nan, mai aukuwa zã ta auku. |
وَانشَقَّتِ السَّمَاءُ فَهِيَ يَوْمَئِذٍ وَاهِيَةٌ(16) Kuma sama zã ta tsãge, dõmin ita a ran nan, mai rauni ce. |
وَالْمَلَكُ عَلَىٰ أَرْجَائِهَا ۚ وَيَحْمِلُ عَرْشَ رَبِّكَ فَوْقَهُمْ يَوْمَئِذٍ ثَمَانِيَةٌ(17) Kuma malã'iku (su bayyana) a kan sãsanninta, kuma wasu (malã'iku) takwas na ɗauke da Al'arshin Ubangijinka, a sama da su, a wannan rãnar. |
يَوْمَئِذٍ تُعْرَضُونَ لَا تَخْفَىٰ مِنكُمْ خَافِيَةٌ(18) A rãnar nan zã a bijirã ku (dõmin hisãbi), bãbu wani rai, mai ɓoyewa, daga cikinku, wanda zai iya ɓõyẽwa. |
فَأَمَّا مَنْ أُوتِيَ كِتَابَهُ بِيَمِينِهِ فَيَقُولُ هَاؤُمُ اقْرَءُوا كِتَابِيَهْ(19) To, amma wanda aka bai wa littãfinsa a dãmansa, sai ya ce wa (makusantansa), "Ku karɓa, ku karanta littafina." |
إِنِّي ظَنَنتُ أَنِّي مُلَاقٍ حِسَابِيَهْ(20) "Lalle ne ni, nã tabbata cewa ni mai haɗuwa da hisãbina ne." |
فَهُوَ فِي عِيشَةٍ رَّاضِيَةٍ(21) Sabõda haka, shi yana cikin wata rãyuwa yardadda. |
فِي جَنَّةٍ عَالِيَةٍ(22) A cikin Aljanna maɗaukakiya. |
قُطُوفُهَا دَانِيَةٌ(23) Nunannun 'yã'yan itãcenta makusantã ne (ga mai son ɗĩba), |
كُلُوا وَاشْرَبُوا هَنِيئًا بِمَا أَسْلَفْتُمْ فِي الْأَيَّامِ الْخَالِيَةِ(24) (Ana ce musu) "Ku ci, kuma ku sha a cikin ni'ima, sabõda abin da kuka gabãtar a cikin kwãnukan da suka shige." |
وَأَمَّا مَنْ أُوتِيَ كِتَابَهُ بِشِمَالِهِ فَيَقُولُ يَا لَيْتَنِي لَمْ أُوتَ كِتَابِيَهْ(25) Kuma wanda aka bai wa littãfinsa ga hagunsa, sai ya ce: "Kaitona, ba a kãwo mini littãfina ba!" |
وَلَمْ أَدْرِ مَا حِسَابِيَهْ(26) "Kuma ban san abin da (ke sakamakon) hisãbina ba!" |
يَا لَيْتَهَا كَانَتِ الْقَاضِيَةَ(27) "In dã dai ita, tã kasance mai halakã ni gabã ɗaya ce! |
مَا أَغْنَىٰ عَنِّي مَالِيَهْ ۜ(28) "Dukiyãta ba ta wadatar da ni ba!" |
هَلَكَ عَنِّي سُلْطَانِيَهْ(29) "Ĩkona ya ɓace mini!" |
خُذُوهُ فَغُلُّوهُ(30) (Sai a ce wa malã'iku) "Ku kãmã shi, sa'an nan ku sanyã shi a cikin ƙuƙumi." |
ثُمَّ الْجَحِيمَ صَلُّوهُ(31) "Sa'an nan, a cikin Jahĩm, ku ƙõna shi." |
ثُمَّ فِي سِلْسِلَةٍ ذَرْعُهَا سَبْعُونَ ذِرَاعًا فَاسْلُكُوهُ(32) "Sa'an nan, acikin sarƙa, tsawonta zirã'i saba'in, sai ku sanya shi." |
إِنَّهُ كَانَ لَا يُؤْمِنُ بِاللَّهِ الْعَظِيمِ(33) "Lalle ne, shi ya kasance ba ya yin ĩmãni da Allah, Mai girma!" |
وَلَا يَحُضُّ عَلَىٰ طَعَامِ الْمِسْكِينِ(34) "Kuma ba ya kwaɗaitarwa ga (bãyar da) abincin matalauci!" |
فَلَيْسَ لَهُ الْيَوْمَ هَاهُنَا حَمِيمٌ(35) "Sabõda haka, a yau, a nan, bã ya da masõyi." |
وَلَا طَعَامٌ إِلَّا مِنْ غِسْلِينٍ(36) "Kuma bãbu wani abinci, sai daga (itãcen) gislĩn." |
لَّا يَأْكُلُهُ إِلَّا الْخَاطِئُونَ(37) "Bãbu mai cin sa sai mãsu ganganci." |
فَلَا أُقْسِمُ بِمَا تُبْصِرُونَ(38) To, ba sai Nã yi rantsuwa da abin da kuke iya gani ba, |
وَمَا لَا تُبْصِرُونَ(39) Da abin da bã ku iya gani. |
إِنَّهُ لَقَوْلُ رَسُولٍ كَرِيمٍ(40) Lalle ne, shi (Alƙur'ani) tabbas maganar wani manzo (Jibirilu) mai daraja ne. |
وَمَا هُوَ بِقَوْلِ شَاعِرٍ ۚ قَلِيلًا مَّا تُؤْمِنُونَ(41) Kuma shi ba maganar wani mawãƙi ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku gaskata. |
وَلَا بِقَوْلِ كَاهِنٍ ۚ قَلِيلًا مَّا تَذَكَّرُونَ(42) Kuma bã maganar bõka ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku iya tunãwa. |
تَنزِيلٌ مِّن رَّبِّ الْعَالَمِينَ(43) Abin saukarwã ne daga Ubangijin halitta duka. |
وَلَوْ تَقَوَّلَ عَلَيْنَا بَعْضَ الْأَقَاوِيلِ(44) Kuma dã (Muhammadu) yã faɗi wata maganã, yã jingina ta garẽ Mu. |
لَأَخَذْنَا مِنْهُ بِالْيَمِينِ(45) Dã Mun kãma shi da dãma. |
ثُمَّ لَقَطَعْنَا مِنْهُ الْوَتِينَ(46) sa'an nan, lalle ne, dã Mun kãtse masa lakã. |
فَمَا مِنكُم مِّنْ أَحَدٍ عَنْهُ حَاجِزِينَ(47) Kuma daga cikinku bãbu wasu mãsu iya kãre (azãbarMu) daga gare shi. |
وَإِنَّهُ لَتَذْكِرَةٌ لِّلْمُتَّقِينَ(48) Kuma lalle ne shi (Alƙur'ãni) tanãtarwa ce ga mãsu taƙawa. |
وَإِنَّا لَنَعْلَمُ أَنَّ مِنكُم مُّكَذِّبِينَ(49) Kuma lalle, ne Mũ, wallahi Munã sane da cẽwa daga cikinku alwwai mãsu ƙaryatãwa. |
وَإِنَّهُ لَحَسْرَةٌ عَلَى الْكَافِرِينَ(50) Kuma lalle ne shi (Alƙarãni) wallahi baƙin ciki ne ga kãfirai. |
وَإِنَّهُ لَحَقُّ الْيَقِينِ(51) Kuma lalle, ne shi gaskiya ce ta yaƙshẽni. |
فَسَبِّحْ بِاسْمِ رَبِّكَ الْعَظِيمِ(52) Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangjinka, mai girma. |