Al-A'raf · 33/206
Fassara Rubutun sauti — Surah Al-A'raf
قُلْ إِنَّمَا حَرَّمَ رَبِّيَ الْفَوَاحِشَ مَا ظَهَرَ مِنْهَا وَمَا بَطَنَ وَالْإِثْمَ وَالْبَغْيَ بِغَيْرِ الْحَقِّ وَأَن تُشْرِكُوا بِاللَّهِ مَا لَمْ يُنَزِّلْ بِهِ سُلْطَانًا وَأَن تَقُولُوا عَلَى اللَّهِ مَا لَا تَعْلَمُونَ ۝٣٣
Qul innamaa harrama Rabbiyal fawaahisha maa zahara minhaa wa maa bataa wal isma walbaghya bighairil haqqi wa an tushrikoo billaahi maa lam yunazzil bihee sultaananw wa an taqooloo `alal laahi maa laa ta`lamoon
📖 Da Hausa
Ka ce: "Abin sani kawai, Ubangijina Yã hana abũbuwanalfãsha; abin da ya bayyana daga gare su da abin da ya ɓõyu, da zunubi da rarraba jama'a, bã da wani hakki ba, kuma da ku yi shirki da Allah ga abin da bai saukar da wani dalĩli ba gare shi, kuma da ku faɗi abin da ba ku sani ba, ga Allah."

🎧 Saurara


📜 Aya 31-35 — Surah Al-A'raf

31۞ يَا بَنِي آدَمَ خُذُوا زِينَتَكُمْ عِندَ كُلِّ مَسْجِدٍ وَكُلُوا وَاشْرَبُوا وَلَا تُسْرِفُوا ۚ إِنَّهُ لَا يُحِبُّ الْمُسْرِفِينَ
Yã ɗiyan Ãdam! Ku riƙi ƙawarku a wurin kõwane masallãci kuma ku ci, kuma ku sha; Kuma kada ku yi ɓarna. Lalle ne Shĩ (Allah), bã Ya son mãsu ɓarna.
32قُلْ مَنْ حَرَّمَ زِينَةَ اللَّهِ الَّتِي أَخْرَجَ لِعِبَادِهِ وَالطَّيِّبَاتِ مِنَ الرِّزْقِ ۚ قُلْ هِيَ لِلَّذِينَ آمَنُوا فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا خَالِصَةً يَوْمَ الْقِيَامَةِ ۗ كَذَٰلِكَ نُفَصِّلُ الْآيَاتِ لِقَوْمٍ يَعْلَمُونَ
Ka ce: "Wãne ne ya haramta ƙawar Allah, wadda Ya fitar sabõda bãyinSa, da mãsu dãɗi daga abinci?" Ka ce: "Sũ, dõmin waɗanda suka yi ĩmani suke a cikin rãyuwar dũniya, suna keɓantattu a Rãnar Kiyãma. "Kamar wannan ne Muke bayyana ãyõyi, daki-daki, ga mutãnen da suke sani.
33قُلْ إِنَّمَا حَرَّمَ رَبِّيَ الْفَوَاحِشَ مَا ظَهَرَ مِنْهَا وَمَا بَطَنَ وَالْإِثْمَ وَالْبَغْيَ بِغَيْرِ الْحَقِّ وَأَن تُشْرِكُوا بِاللَّهِ مَا لَمْ يُنَزِّلْ بِهِ سُلْطَانًا وَأَن تَقُولُوا عَلَى اللَّهِ مَا لَا تَعْلَمُونَ
Ka ce: "Abin sani kawai, Ubangijina Yã hana abũbuwanalfãsha; abin da ya bayyana daga gare su da abin da ya ɓõyu, da zunubi da rarraba jama'a, bã da wani hakki ba, kuma da ku yi shirki da Allah ga abin da bai saukar da wani dalĩli ba gare shi, kuma da ku faɗi abin da ba ku sani ba, ga Allah."
34وَلِكُلِّ أُمَّةٍ أَجَلٌ ۖ فَإِذَا جَاءَ أَجَلُهُمْ لَا يَسْتَأْخِرُونَ سَاعَةً ۖ وَلَا يَسْتَقْدِمُونَ
Kuma ga kõwace al'umma akwai ajali. Sa'an nan idan ajalinsu ya je, bã zã a yi musu jinkiri ba, sa'a guda, kuma bã zã su gabãce shi ba.
35يَا بَنِي آدَمَ إِمَّا يَأْتِيَنَّكُمْ رُسُلٌ مِّنكُمْ يَقُصُّونَ عَلَيْكُمْ آيَاتِي ۙ فَمَنِ اتَّقَىٰ وَأَصْلَحَ فَلَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ
Yã ɗiyan Ãdam! Ko dai wasu manzanni, daga cikinku, su jẽ muku, sunã gaya muku ayõyiNato, wanda ya yi taƙawa, kuma ya gyara aikinsa, to, bãbu tsoro a kansu, kuma bã su yin baƙin ciki.
Al-A'rafJerin Alqur'ani
206Aya
MeccanRevelation
33Aya

Fassara — Al-A'raf 33

Surah Al-A'raf Aya 33 - Karatu, Saurara, Fassara, Hausa : Ka ce: "Abin sani kawai, Ubangijina Yã hana abũbuwanalfãsha; abin…

Surah Aya 33/206 — Surah Al-A'raf الأعراف (Meccan). Karatu Saurara Fassara (Hausa). Saurara: Surah Al-A'raf Saurara, Surah Al-A'raf Fassara, Surah Al-A'raf mp3, Surah Al-A'raf pdf. Aya 31–35. Da Hausa: العربية.




Al-Kur'ani


Monday, September 7, 2026

Don't forget us in your sincere prayers