Alam tara ilal lazeena qeela lahum kuffooo aidiyakum wa aqeemus Salaata w aaatuz Zakaata falammaa kutiba `alaihimul qitaalu izaa fareequm minhum yakhshawnnan naasa kakhashyatil laahi aw ashadda khashyah; wa qaaloo Rabbanaa lima katabta `alainal qitaala law laaa akhkhartanaa ilaaa ajalin qareeb; qul mataa`ud dunyaa qaleelunw wal Aakhiratu khairul limanit taqaa wa laa tuzlamoona fateelaa
📖 Fassara (Da Hausa)
📖 Da Hausa
Shin, ba ka gani ba zuwa ga waɗanda aka ce musu: "Ku kange hannuwanku, kuma ku tsayar da salla, kuma ku bãyar da zakka."? To a lõkacin da aka wajabta musu yãƙi sai ga wani ɓangare daga cikinsu sunã tsõron mutãne kamar tsõron Allah kõ kuwa mafi tsanani ga tsõron, kuma suka ce: "Ya Ubangijinmu! Don me Ka wajabta yãƙi a kanmu? Me ya hana Ka jinkirta mana zuwa ga wani ajali na kusa?"Ka ce: "Jin dãɗin dũniya kaɗan ne, kuma Lãhira ce mafi alhẽri ga wanda ya yi taƙawa. Kuma bã a zãluntar ku da sĩlĩlin hancin gurtsun dabĩno!
Fatīl: Zaren siririn da yake tsakiyar ƙwayar dabino.
Tafsirin Ayar:
Shin ba ka sani ba, ya Manzo, halin waɗanda aka ce musu a lokacin da suke Makka kafin a wajabta yaƙi: "Ku hana hannuwanku daga yaƙi da kuma masu shirka, kuma ku tsayar da salla, ku kuma bayar da zakka." Amma a lokacin da suka yi hijira zuwa Madina, kuma aka wajabta musu yaƙi da mawuyata, sai ga wasu daga cikinsu suna tsoron mutane (masu shirka) kamar tsoron da suke yi wa Allah, ko ma fiye da haka. Sun ce: "Ya Ubangijinmu! Don me ka wajabta mana yaƙi? Da ma ka jinkirta mana zuwa wani ajali makusanci, domin mu more rayuwar duniya." Ka ce musu, ya Manzo: "Abin morewa na duniya kaɗan ne, kuma lalle ne lahira ita ce mafi alheri ga wanda ya bi Allah da taƙawa, ya aikata abin da aka umarce shi, ya kuma nisanci abin da aka hana shi. Kuma ba za a zalunce ku ba ko kaɗan, har ma da gwargwadon fatīl (zaren siririn da ke tsakiyar ƙwayar dabino) na ayyukanku na alheri."
Fa'idodin Darasi:
Nuna cewa wajabta yaƙi yana zuwa ne bisa hikimar Allah, kuma ba shi ne abin da mutane ke so ba, domin mutum yana son jin daɗi, amma Allah ne Mafi sanin abin da yake da kyau ga bayinsa.
Ƙarfafa imani da cewa rayuwar duniya ba ta da wani daraja idan aka kwatanta da lahira, don haka ya kamata mumini ya ba da fifiko ga abin da yake dawwama a kan abin da yake ƙarewa.
Gargaɗi ga muminai daga son rai da tsoron halitta a kan tsoron Allah, domin tsoron Allah shi ne tushen taƙawa da samun nasara.
Ƙarfafa zuciya da cewa Allah ba ya zaluntar kowa, ko da gwargwadon ƙanƙanin abu, domin yana cika lada da kuma ƙara wa masu kyautatawa alheri.
Nuna cewa yaƙi a Musulunci ba don son ɓarna ba ne, amma don kare addini da kuma tabbatar da 'yanci ga mutane, kuma wajabta shi yana zuwa ne bisa buƙata da shari'a.
Shin, ba ka gani ba zuwa ga waɗanda aka ce musu: "Ku kange hannuwanku, kuma ku tsayar da salla, kuma ku bãyar da zakka."? To a lõkacin da aka wajabta musu yãƙi sai ga wani ɓangare daga cikinsu sunã tsõron mutãne kamar tsõron Allah kõ kuwa mafi tsanani ga tsõron, kuma suka ce: "Ya Ubangijinmu! Don me Ka wajabta yãƙi a kanmu? Me ya hana Ka jinkirta mana zuwa ga wani ajali na kusa?"Ka ce: "Jin dãɗin dũniya kaɗan ne, kuma Lãhira ce mafi alhẽri ga wanda ya yi taƙawa. Kuma bã a zãluntar ku da sĩlĩlin hancin gurtsun dabĩno!
Kuma mẽne ne ya sãme ku, bã ku yin yãƙi a cikin hanyar Allah, da waɗanda aka raunanar daga maza da mata da yãra sunã cewa: "Yã Ubangijinmu! Ka fitar da mu daga wannan alƙarya wadda mutãnenta suke da zãlunci, kuma Ka sanya mana majiɓinci daga gunKa, kuma Ka sanya mana mataimaki daga gunKa."?
Waɗanda suka yi ĩmãni, sunã yãki a cikin hanyar Allah, kuma waɗanda suka kãfirta sunã yãƙi a cikin hanyar ¦ãgũtu (Shaiɗan). To, ku yãƙi majiɓintan Shaiɗan. Lalle ne kaidin Shaiɗan yã kasance mai rauni.
Shin, ba ka gani ba zuwa ga waɗanda aka ce musu: "Ku kange hannuwanku, kuma ku tsayar da salla, kuma ku bãyar da zakka."? To a lõkacin da aka wajabta musu yãƙi sai ga wani ɓangare daga cikinsu sunã tsõron mutãne kamar tsõron Allah kõ kuwa mafi tsanani ga tsõron, kuma suka ce: "Ya Ubangijinmu! Don me Ka wajabta yãƙi a kanmu? Me ya hana Ka jinkirta mana zuwa ga wani ajali na kusa?"Ka ce: "Jin dãɗin dũniya kaɗan ne, kuma Lãhira ce mafi alhẽri ga wanda ya yi taƙawa. Kuma bã a zãluntar ku da sĩlĩlin hancin gurtsun dabĩno!
"Inda duk kuka kasance, mutuwa zã ta riske ku, kuma kõ da kun kasance ne a cikin gãnuwõyi ingãtattu!"Kuma idan wani alhẽri ya sãme su sai su ce: "Wannan daga wurin Allah ne," kuma idan wata cũta ta sãme su, sai su ce: "Wannan daga gare ka ne."Ka ce: "Dukkansu daga Allah ne." To, me ya sãmi waɗannan mutãne, bã su kusantar fahimtar magana?
Abin da ya sãme ka daga alhẽri, to, daga Allah yake, kuma abin da ya sãme ka daga sharri, to, daga kanka yake, kuma Mun aike ka zuwa ga mutãne, (kana) Manzo, kuma Allah Yã isa ga zama shaida.
SurahQuran.com was founded as a humble effort to serve the Noble Book and the pure Sunnah, to invite people to Allah, and to make the religious sciences accessible according to the methodology of the Quran and Sunnah. We praise and thank Allah for His grace, and we ask Him to accept our work and make it sincere for His noble Face.