حم(1) Ḥ. M̃. |
وَالْكِتَابِ الْمُبِينِ(2) Inã rantsuwa da Littãfi Mabayyani. |
إِنَّا أَنزَلْنَاهُ فِي لَيْلَةٍ مُّبَارَكَةٍ ۚ إِنَّا كُنَّا مُنذِرِينَ(3) Lalle ne, Mũ, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mũ' Mun kasance Mãsu yin gargaɗi. |
فِيهَا يُفْرَقُ كُلُّ أَمْرٍ حَكِيمٍ(4) A cikinsa (shi daren) ake rarrabe kõwane umurui bayyananne. |
أَمْرًا مِّنْ عِندِنَا ۚ إِنَّا كُنَّا مُرْسِلِينَ(5) Umurni na daga wurinMu. Lalle Mũ ne Muka kasanceMãsu aikãwã. |
رَحْمَةً مِّن رَّبِّكَ ۚ إِنَّهُ هُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ(6) Sabõda rahama daga Ubangijinka. Lalle Shĩ, Shi ne Mai ji, Mãsani. |
رَبِّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا ۖ إِن كُنتُم مُّوقِنِينَ(7) (Shĩ ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu yaƙĩni (za ku gãne haka). |
لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ يُحْيِي وَيُمِيتُ ۖ رَبُّكُمْ وَرَبُّ آبَائِكُمُ الْأَوَّلِينَ(8) Babu abin bautãwa fãce Shi. Yana rãyarwa Kuma Yana kashẽwa. (Shi ne) Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko. |
بَلْ هُمْ فِي شَكٍّ يَلْعَبُونَ(9) A'a sũ, sunã wãsã a cikin shakka. |
فَارْتَقِبْ يَوْمَ تَأْتِي السَّمَاءُ بِدُخَانٍ مُّبِينٍ(10) Sabõda haka, ka dakata rãnar da sama zã tã zo da hayãƙi bayyananne. |
يَغْشَى النَّاسَ ۖ هَٰذَا عَذَابٌ أَلِيمٌ(11) Yanã rufe mutãne. Wannan wata azãba ce mai raɗaɗi. |
رَّبَّنَا اكْشِفْ عَنَّا الْعَذَابَ إِنَّا مُؤْمِنُونَ(12) Ya Ubangijinmu! Ka kuranye mana azãba. Lalle Mũ, mãsu ĩmãni ne. |
أَنَّىٰ لَهُمُ الذِّكْرَىٰ وَقَدْ جَاءَهُمْ رَسُولٌ مُّبِينٌ(13) Inã tunãwa take a gare su, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanãwa Ya je musu (da gargaɗin saukar azãbar, ba su karɓa ba)? |
ثُمَّ تَوَلَّوْا عَنْهُ وَقَالُوا مُعَلَّمٌ مَّجْنُونٌ(14) Sa'an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: "Wanda ake gayãwa ne, mahaukaci." |
إِنَّا كَاشِفُو الْعَذَابِ قَلِيلًا ۚ إِنَّكُمْ عَائِدُونَ(15) Lalle Mũ, Mãsu kuranyẽwar azãba ne, a ɗan lõkaci kaɗan, lalle kũ, mãsu kõmãwa ne (ga laifin). |
يَوْمَ نَبْطِشُ الْبَطْشَةَ الْكُبْرَىٰ إِنَّا مُنتَقِمُونَ(16) Rãnar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ mãsu azãbar rãmuwa ne. |
۞ وَلَقَدْ فَتَنَّا قَبْلَهُمْ قَوْمَ فِرْعَوْنَ وَجَاءَهُمْ رَسُولٌ كَرِيمٌ(17) Kuma lalle ne haƙĩƙa a gabaninsu, Mun fitini mutãnen Fir'auna, kuma wani Manzo karĩmi ya jẽ musu. |
أَنْ أَدُّوا إِلَيَّ عِبَادَ اللَّهِ ۖ إِنِّي لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ(18) (Mazon ya ce): "Ku kãwo mini (ĩmãninku) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne amintacce zuwa gare ku." |
وَأَن لَّا تَعْلُوا عَلَى اللَّهِ ۖ إِنِّي آتِيكُم بِسُلْطَانٍ مُّبِينٍ(19) "Kuma kada ku nẽmi ɗaukaka a kan Allah. Lalle nĩ mai zo muku ne da dalĩli bayyananne." |
وَإِنِّي عُذْتُ بِرَبِّي وَرَبِّكُمْ أَن تَرْجُمُونِ(20) "Kuma lalle nĩ na nẽmi tsari da Ubangijĩna, kuma Ubangijinku, dõmin kada ku jẽfe ni." |
وَإِن لَّمْ تُؤْمِنُوا لِي فَاعْتَزِلُونِ(21) "Kuma idan ba ku yi ĩmãni sabõda nĩ ba, to, ku nĩsance ni." |
فَدَعَا رَبَّهُ أَنَّ هَٰؤُلَاءِ قَوْمٌ مُّجْرِمُونَ(22) Sai ya kirayi Ubangjinsa cẽwa waɗannan mutãnene mãsu laifi. |
فَأَسْرِ بِعِبَادِي لَيْلًا إِنَّكُم مُّتَّبَعُونَ(23) (Allah Ya ce): "To, ka yi tafiyar dare da bayiNa, da dare. Lalle kũ, waɗanda ake bĩ ne (dõmin a kãma ku.)" |
وَاتْرُكِ الْبَحْرَ رَهْوًا ۖ إِنَّهُمْ جُندٌ مُّغْرَقُونَ(24) "Kuma ka bar tẽku rarrabe. Lalle sũ, runduna ce abar nutsarwa." |
كَمْ تَرَكُوا مِن جَنَّاتٍ وَعُيُونٍ(25) Da yawa suka bar gõnaki da marẽmari. |
وَزُرُوعٍ وَمَقَامٍ كَرِيمٍ(26) Da shuke-shuke da matsayi mai kyau. |
وَنَعْمَةٍ كَانُوا فِيهَا فَاكِهِينَ(27) Da wata ni'ima da suka kasance a cikinta sunã mãsu hutu. |
كَذَٰلِكَ ۖ وَأَوْرَثْنَاهَا قَوْمًا آخَرِينَ(28) Kamar haka! Kuma Muka gãdar da ita ga waɗansu mutãne na dabam. |
فَمَا بَكَتْ عَلَيْهِمُ السَّمَاءُ وَالْأَرْضُ وَمَا كَانُوا مُنظَرِينَ(29) Sa'an nan samã da ƙasã ba su yi kũka a kansu ba, Kuma ba su kasance waɗanda ake yi wa jinkiri ba. |
وَلَقَدْ نَجَّيْنَا بَنِي إِسْرَائِيلَ مِنَ الْعَذَابِ الْمُهِينِ(30) Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun tsĩrar da Banĩ Isrã'ĩla daga, azãba mai wulãkantãwa. |
مِن فِرْعَوْنَ ۚ إِنَّهُ كَانَ عَالِيًا مِّنَ الْمُسْرِفِينَ(31) Daga Fir'auna. Lalle shi, ya kasance maɗaukaki daga cikin mãsu ɓarna. |
وَلَقَدِ اخْتَرْنَاهُمْ عَلَىٰ عِلْمٍ عَلَى الْعَالَمِينَ(32) Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe su sabõda wani ilmi (na Taurata) a kan mutãne. |
وَآتَيْنَاهُم مِّنَ الْآيَاتِ مَا فِيهِ بَلَاءٌ مُّبِينٌ(33) Kuma Muka bã su, daga ãyõyin mu'ujizõji, abin da yake a cikinsa, akwai ni'ima bayyananna |
إِنَّ هَٰؤُلَاءِ لَيَقُولُونَ(34) Lalle waɗannan mutãne, haƙĩka, sunã cẽwa, |
إِنْ هِيَ إِلَّا مَوْتَتُنَا الْأُولَىٰ وَمَا نَحْنُ بِمُنشَرِينَ(35) "Babu wani abu sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba." |
فَأْتُوا بِآبَائِنَا إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ(36) "Sai ku zo da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya." |
أَهُمْ خَيْرٌ أَمْ قَوْمُ تُبَّعٍ وَالَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۚ أَهْلَكْنَاهُمْ ۖ إِنَّهُمْ كَانُوا مُجْرِمِينَ(37) shin, sũ ne mafĩfĩta kõ kuwa mutãnen Tubba'u, kuma da waɗanda ke a gabãninsu? Mun halaka su, lalle sũ, sun kasance mãsu laifi. |
وَمَا خَلَقْنَا السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا لَاعِبِينَ(38) Kuma ba Mu halitta slmmai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu ba, alhãli kuwa Munã mãsu wãsã. |
مَا خَلَقْنَاهُمَا إِلَّا بِالْحَقِّ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ(39) Ba Mu halitta su ba fãce da manufa ta gaskiya, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba. |
إِنَّ يَوْمَ الْفَصْلِ مِيقَاتُهُمْ أَجْمَعِينَ(40) Lalle rãnar rarrabẽwa, ita ce lõkacin wa'adinsu gabã ɗaya. |
يَوْمَ لَا يُغْنِي مَوْلًى عَن مَّوْلًى شَيْئًا وَلَا هُمْ يُنصَرُونَ(41) Rãnar da wani zumu bã ya amfãnin wani zumu da kõme kuma ba su zama anã taimakon su ba. |
إِلَّا مَن رَّحِمَ اللَّهُ ۚ إِنَّهُ هُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُ(42) fãce wanda Allah Ya yi wa rahama. Lalle Shi (Allah), shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai. |
إِنَّ شَجَرَتَ الزَّقُّومِ(43) Lalle itãciyar zaƙƙũm (ɗanyen wutã), |
طَعَامُ الْأَثِيمِ(44) Ita ce abincin mai laifi. |
كَالْمُهْلِ يَغْلِي فِي الْبُطُونِ(45) Kamar narkakken kwalta yanã tafasa a cikin cikunna. |
كَغَلْيِ الْحَمِيمِ(46) Kamar tafasar ruwan zãfi. |
خُذُوهُ فَاعْتِلُوهُ إِلَىٰ سَوَاءِ الْجَحِيمِ(47) (A cẽ wa malã'ikun wutã), "Ku kãmã shi, sa'an nan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar Jahĩm." |
ثُمَّ صُبُّوا فَوْقَ رَأْسِهِ مِنْ عَذَابِ الْحَمِيمِ(48) "Sa'an nan ku zuba, a kansa, daga azãbar ruwan zãfi." |
ذُقْ إِنَّكَ أَنتَ الْعَزِيزُ الْكَرِيمُ(49) (A ce masã), "Ka ɗanɗana! Lalle kai, kai ne mabuwãyi mai girma!" |
إِنَّ هَٰذَا مَا كُنتُم بِهِ تَمْتَرُونَ(50) "Lalle wannan, shi ne abin da kuka kasance kunã shakka game da shi." |
إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي مَقَامٍ أَمِينٍ(51) Lalle mãsu taƙawa sunã cikin matsayi amintacce. |
فِي جَنَّاتٍ وَعُيُونٍ(52) A cikin gidãjen Aljanna da marẽmari. |
يَلْبَسُونَ مِن سُندُسٍ وَإِسْتَبْرَقٍ مُّتَقَابِلِينَ(53) Sunã tufanta daga tufãfin alharĩni raƙĩƙi, da mai kauri, sunã mãsu zaman fuskantar jũna. |
كَذَٰلِكَ وَزَوَّجْنَاهُم بِحُورٍ عِينٍ(54) Kamar haka, kuma Mun aurar da su da mãtã mãsu kyaun idãnu, mãsu girmansu. |
يَدْعُونَ فِيهَا بِكُلِّ فَاكِهَةٍ آمِنِينَ(55) Sunã kira, a cikinsu (gidẽjen) ga dukan 'ya'yan itãcen marmari, sunã amintattu (daga dukan abin tsõro). |
لَا يَذُوقُونَ فِيهَا الْمَوْتَ إِلَّا الْمَوْتَةَ الْأُولَىٰ ۖ وَوَقَاهُمْ عَذَابَ الْجَحِيمِ(56) Bã su ɗanɗanar mutuwa, a cikinsu, fãce mutuwar farko, kuma (Allah), Ya tsare musu azãbar Jahĩm. |
فَضْلًا مِّن رَّبِّكَ ۚ ذَٰلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ(57) Sabõda falala daga Ubangijinka. Wancan shi ne babban rabo, mai girma. |
فَإِنَّمَا يَسَّرْنَاهُ بِلِسَانِكَ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ(58) Dõmin haka kawai Muka sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) da harshenka, tsammãninsu, su riƙa tunãwa. |
فَارْتَقِبْ إِنَّهُم مُّرْتَقِبُونَ(59) Sai ka yi jira. Lalle sũ, mãsu jira ne. |