Yusuf · 38/111
Fassara Rubutun sauti — Surah Yusuf
وَاتَّبَعْتُ مِلَّةَ آبَائِي إِبْرَاهِيمَ وَإِسْحَاقَ وَيَعْقُوبَ ۚ مَا كَانَ لَنَا أَن نُّشْرِكَ بِاللَّهِ مِن شَيْءٍ ۚ ذَٰلِكَ مِن فَضْلِ اللَّهِ عَلَيْنَا وَعَلَى النَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لَا يَشْكُرُونَ ۝٣٨
Wattab`tu millata aabaaa`eee Ibraaheema wa Ishaaqa wa Ya`qoob; maa kaana lanaaa an nushrika billaahi min shai` zaalikamin fadlil laahi `alainaa wa `alan naasi wa laakinna aksaran naasi laa yashkuroon
📖 Da Hausa
"Kuma na bi addinin iyayẽna, Ibrãhĩm da Is'hãka da Yãƙũba. Bã ya yiwuwa a gare mu mu yi shirka da Allah da kõme. Wannan yana daga falalar Allah a kanmu da mutãne, amma mafi yawan mutãne bã su gõdewa."

🎧 Saurara
📜

Fassara — Tafsir

Ma'anar Kalmomin:

  • Milla: Addini ko hanya.
  • Fadl: Kyauta ko alheri.

Tafsiri:

Na bi addinin kakannina: Ibrahim, Ishaq da Ya'akubu, wato addinin tauhidi (bauta wa Allah Shi Kaɗai ba tare da wani abin tarayya ba). Ba ya kamata ba mu yi shirka da Allah da kome ba, domin mu annabawa an tsare mu daga shirka. Wannan tauhidi da imani da nake a kai shi da kakannina, wani falala ne daga Allah a gare mu, domin Ya shiryar da mu zuwa gare shi, kuma falala ce a kan dukan mutane, domin Ya aiko mana da annabawa da suka kira zuwa gare shi. Amma mafi yawan mutane ba su godewa Allah ba a kan wannan falala mai girma, sai dai suna musun ni'imarsa.



📜 Aya 36-40 — Surah Yusuf

36وَدَخَلَ مَعَهُ السِّجْنَ فَتَيَانِ ۖ قَالَ أَحَدُهُمَا إِنِّي أَرَانِي أَعْصِرُ خَمْرًا ۖ وَقَالَ الْآخَرُ إِنِّي أَرَانِي أَحْمِلُ فَوْقَ رَأْسِي خُبْزًا تَأْكُلُ الطَّيْرُ مِنْهُ ۖ نَبِّئْنَا بِتَأْوِيلِهِ ۖ إِنَّا نَرَاكَ مِنَ الْمُحْسِنِينَ
Kuma waɗansu samãri biyu suka shiga kurkuku tãre da shi. ¦ayansu ya ce: "Lalle ne nĩ, nã yi mafarkin gã ni inã mãtsar giya." Kuma ɗayan ya ce: "Lalle ne nĩ, nã yi Mafarkin gã ni inã ɗauke da waina a bisa kaina, tsuntsãye sunã ci daga gare ta. Ka bã mu lãbãri game da fassararsu. Lalle ne mũ, Munã ganin ka daga mãsu kyautatãwa."
37قَالَ لَا يَأْتِيكُمَا طَعَامٌ تُرْزَقَانِهِ إِلَّا نَبَّأْتُكُمَا بِتَأْوِيلِهِ قَبْلَ أَن يَأْتِيَكُمَا ۚ ذَٰلِكُمَا مِمَّا عَلَّمَنِي رَبِّي ۚ إِنِّي تَرَكْتُ مِلَّةَ قَوْمٍ لَّا يُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَهُم بِالْآخِرَةِ هُمْ كَافِرُونَ
Ya ce: "Wani abinci bã zai zo muku ba wanda ake azurtã ku da shi fãce nã bã ku lãbãrin fassararsa, kãfin ya zo muku. Wannan kuwa yanã daga abin da Ubangijĩna Ya sanar da ni. Lalle ne nĩ nã bar addinin mutãne waɗanda ba su yi ĩmãni da Allah ba, kuma game da lãhira, sũ kãfirai ne."
38وَاتَّبَعْتُ مِلَّةَ آبَائِي إِبْرَاهِيمَ وَإِسْحَاقَ وَيَعْقُوبَ ۚ مَا كَانَ لَنَا أَن نُّشْرِكَ بِاللَّهِ مِن شَيْءٍ ۚ ذَٰلِكَ مِن فَضْلِ اللَّهِ عَلَيْنَا وَعَلَى النَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لَا يَشْكُرُونَ
"Kuma na bi addinin iyayẽna, Ibrãhĩm da Is'hãka da Yãƙũba. Bã ya yiwuwa a gare mu mu yi shirka da Allah da kõme. Wannan yana daga falalar Allah a kanmu da mutãne, amma mafi yawan mutãne bã su gõdewa."
39يَا صَاحِبَيِ السِّجْنِ أَأَرْبَابٌ مُّتَفَرِّقُونَ خَيْرٌ أَمِ اللَّهُ الْوَاحِدُ الْقَهَّارُ
"Yã abõkaina biyu na kurkuku! Shin iyãyen giji dabam-dabam ne mafiya alhẽri kõ kuwa Allah Makaɗaici Mai tanƙwasãwa?"
40مَا تَعْبُدُونَ مِن دُونِهِ إِلَّا أَسْمَاءً سَمَّيْتُمُوهَا أَنتُمْ وَآبَاؤُكُم مَّا أَنزَلَ اللَّهُ بِهَا مِن سُلْطَانٍ ۚ إِنِ الْحُكْمُ إِلَّا لِلَّهِ ۚ أَمَرَ أَلَّا تَعْبُدُوا إِلَّا إِيَّاهُ ۚ ذَٰلِكَ الدِّينُ الْقَيِّمُ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ
"Ba ku bauta wa kõme, baicinSa, fãce waɗansu sũnãye waɗanda kuka ambace su, kũ da ubanninku. Allah bai saukar da wani dalĩli ba game da su. Bãbu hukunci fãce na Allah. Ya yi umurnin kada ku bauta wa kõwa fãce Shi. Wancan ne addini madaidaici, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba."
YusufJerin Alqur'ani
111Aya
MeccanRevelation
38Aya

Fassara — Yusuf 38

Surah Yusuf Aya 38 - Karatu, Saurara, Fassara, Hausa : "Kuma na bi addinin iyayẽna, Ibrãhĩm da Is'hãka da Yãƙũba.…

Surah Aya 38/111 — Surah Yusuf يوسف (Meccan). Karatu Saurara Fassara (Hausa). Saurara: Surah Yusuf Saurara, Surah Yusuf Fassara, Surah Yusuf mp3, Surah Yusuf pdf. Aya 36–40. Da Hausa: العربية.




Al-Kur'ani


Monday, September 7, 2026

Don't forget us in your sincere prayers