Surah Al-Layl Larabci da Hausa

Karanta Surah Al-Layl tare da cikakkiyar fassarar Hausa da sauti. Fassara aya bayan aya. (21 Aya — مكية). Al-Layl Saurara, Al-Layl Fassara, Al-Layl mp3, Al-Layl pdf.

Karanta da Saurara Surah Al-Layl

🎧 Aya
M Mishary Rashid Alafasy
M Mahmoud Khalil Al-Husary
A Abdurrahman As-Sudais
M Mohamed Siddiq Al-Minshawi
A Abdul Basit Abdul Samad
A Ali Al-Hudhaify
A Ahmed ibn Ali al-Ajamy
A Abu Bakr Ash-Shaatree
M Muhammad Ayyoub
A Abdullah Basfar
A Abdullah Al-Juhani
M Maher Al Muaiqly
x1
وَاللَّيْلِ إِذَا يَغْشَىٰ ۝١
📖 Fassara Aya 1
Inã rantsuwa da dare a lõkacin da yake rufẽwa.
وَالنَّهَارِ إِذَا تَجَلَّىٰ ۝٢
📖 Fassara Aya 2
Da yini a lõkacin da yake kuranyẽwa.
وَمَا خَلَقَ الذَّكَرَ وَالْأُنثَىٰ ۝٣
📖 Fassara Aya 3
Da abin da ya halitta namiji da mace.
إِنَّ سَعْيَكُمْ لَشَتَّىٰ ۝٤
📖 Fassara Aya 4
Lãlle ne ayyukanku, dabam-dabam suke.
فَأَمَّا مَنْ أَعْطَىٰ وَاتَّقَىٰ ۝٥
📖 Fassara Aya 5
To, amma wanda ya yi kyauta, kuma ya yi taƙawa.
وَصَدَّقَ بِالْحُسْنَىٰ ۝٦
📖 Fassara Aya 6
Kuma ya gaskata kalma mai kyãwo.
فَسَنُيَسِّرُهُ لِلْيُسْرَىٰ ۝٧
📖 Fassara Aya 7
To, zã Mu sauƙaƙe masa har ya kai ga sauƙi.
وَأَمَّا مَن بَخِلَ وَاسْتَغْنَىٰ ۝٨
📖 Fassara Aya 8
Kuma amma wanda ya yi rõwa, kuma ya wadãtu da kansa.
وَكَذَّبَ بِالْحُسْنَىٰ ۝٩
📖 Fassara Aya 9
Kuma ya ƙaryatar da kalma mai kyãwo.
فَسَنُيَسِّرُهُ لِلْعُسْرَىٰ ۝١٠
📖 Fassara Aya 10
To, zã Mu sauƙaƙke masa har ya kai ga tsanani.
وَمَا يُغْنِي عَنْهُ مَالُهُ إِذَا تَرَدَّىٰ ۝١١
📖 Fassara Aya 11
Kuma dũkiyarsa ba ta wadãtar masa da kõme ba, a lõkacin da ya gangara (a wuta).
إِنَّ عَلَيْنَا لَلْهُدَىٰ ۝١٢
📖 Fassara Aya 12
Lãlle aikinMu ne, Mu bayyana shiriya.
وَإِنَّ لَنَا لَلْآخِرَةَ وَالْأُولَىٰ ۝١٣
📖 Fassara Aya 13
Kuma lalle ne Lãhira da duniya Namu ne.
فَأَنذَرْتُكُمْ نَارًا تَلَظَّىٰ ۝١٤
📖 Fassara Aya 14
Sabõda haka, Na yi maku gargaɗi da wuta mai babbaka.
لَا يَصْلَاهَا إِلَّا الْأَشْقَى ۝١٥
📖 Fassara Aya 15
Bãbu mai shigarta sai mafi shaƙãwa.
الَّذِي كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ ۝١٦
📖 Fassara Aya 16
Wanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya.
وَسَيُجَنَّبُهَا الْأَتْقَى ۝١٧
📖 Fassara Aya 17
Kuma mafi taƙawa zai nisance ta.
الَّذِي يُؤْتِي مَالَهُ يَتَزَكَّىٰ ۝١٨
📖 Fassara Aya 18
Wanda yake bãyar da dũkiyarsa, alhãli yana tsarkaka.
وَمَا لِأَحَدٍ عِندَهُ مِن نِّعْمَةٍ تُجْزَىٰ ۝١٩
📖 Fassara Aya 19
Alhãli bãbu wani mai wata ni'ima wurinsa wadda ake nẽman sakamakonta.
إِلَّا ابْتِغَاءَ وَجْهِ رَبِّهِ الْأَعْلَىٰ ۝٢٠
📖 Fassara Aya 20
Fãce dai nẽman yardar Ubangijinsa Mafi ɗaukaka.
وَلَسَوْفَ يَرْضَىٰ ۝٢١
📖 Fassara Aya 21
To, lalle ne zai yarda (da sakamakon da zã a bã shi).
← 91 Al-Layl (92/114) 93 →
Karatu Surah Al-Layl Hausa – Fassara da Audio

92الليل Al-Layl 📚 21 Aya مكية



Al-Kur'ani


Tuesday, August 18, 2026

Don't forget us in your sincere prayers