Al-Baqarah · 138/286
Fassara Rubutun sauti — Surah Al-Baqarah
صِبْغَةَ اللَّهِ ۖ وَمَنْ أَحْسَنُ مِنَ اللَّهِ صِبْغَةً ۖ وَنَحْنُ لَهُ عَابِدُونَ ۝١٣٨
Sibghatal laahi wa man ahsanu minal laahi sibghatanw wa nahnu lahoo `aabidoon
📖 Da Hausa
Rinin Allah! Kuma wãne ne mafi kyau ga rini daga Allah? Kuma mu, a gare Shi, mãsu bautãwa ne.

🎧 Saurara
📜

Fassara — Tafsir

Ma’anonin Kalmomin Ayar:

  • صِبْغَةَ اللهِ: Addinin Allah, wato Musulunci. An kira shi da “sibgha” (rini) domin addini yana bayyana a kan mai shi kamar yadda rini yake bayyana a kan tufa.
  • عَابِدُونَ: Masu bauta wa Allah shi kaɗai, masu tawali’u da biyayya gare Shi.

Fassarar Ayar:

Ku tsaya tsayin daka a kan addinin Allah wanda Ya halicce ku a kansa, wato Musulunci, a bayyane da kuma a ɓoye. Babu wani addini da ya fi addinin Allah kyau, domin shi ne ya dace da dabi’ar halitta, yana kawo amfani ga mutane, kuma yana hana cutarwa. Ku ce: “Mu masu bauta wa Allah ne shi kaɗai, ba mu yin shirka da kowa a cikin ibadarsa.” An kira wannan addini da “sibgha” (rini) ne domin yana bayyana a kan mai shi kamar yadda rini yake bayyana a kan tufa, don haka addinin Musulunci yana bayyana a kan halayyar musulmi da kyawawan ayyukansa.

Fa’idojin Ayar:

  1. Addinin Musulunci shi ne addinin halitta wanda Allah Ya halicci mutane a kansa, don haka duk wanda ya bi shi, to ya dace da halittarsa ta asali.
  2. Babu wani addini da ya fi addinin Allah kyau da inganci, domin shi ne addinin gaskiya wanda ke kare mutum daga duk wata cuta ta addini ko ta duniya.
  3. Imani da ibada ga Allah shi kaɗai ne ke ba da daraja da ɗaukaka ga musulmi, kuma shi ne tushen farin ciki a duniya da lafiya a lahira.
  4. Kyawawan halaye da ayyukan musulmi su ne shaidar addininsa, kamar yadda rini yake bayyana a kan tufa, don haka ya kamata mu nuna kyawawan halaye domin jawo mutane zuwa ga addinin Allah.


📜 Aya 136-140 — Surah Al-Baqarah

136قُولُوا آمَنَّا بِاللَّهِ وَمَا أُنزِلَ إِلَيْنَا وَمَا أُنزِلَ إِلَىٰ إِبْرَاهِيمَ وَإِسْمَاعِيلَ وَإِسْحَاقَ وَيَعْقُوبَ وَالْأَسْبَاطِ وَمَا أُوتِيَ مُوسَىٰ وَعِيسَىٰ وَمَا أُوتِيَ النَّبِيُّونَ مِن رَّبِّهِمْ لَا نُفَرِّقُ بَيْنَ أَحَدٍ مِّنْهُمْ وَنَحْنُ لَهُ مُسْلِمُونَ
Ku ce: "Mun yi ĩmãni da Allah, da abin da aka saukar zuwa gare mu, da abin da aka saukar zuwa ga Ibrãhĩm da Ismã'ĩla da Is'hãka da Ya'aƙũbu da jĩkõki, da abin da aka bai wa Mũsã da Ĩsã, da abin da aka bai wa annabãwa daga Ubangijinsu, bã mu rarrabẽwa a tsakãnin kõwa daga gare su, kuma mu, a gare Shi, mãsu miƙa wuya ne."
137فَإِنْ آمَنُوا بِمِثْلِ مَا آمَنتُم بِهِ فَقَدِ اهْتَدَوا ۖ وَّإِن تَوَلَّوْا فَإِنَّمَا هُمْ فِي شِقَاقٍ ۖ فَسَيَكْفِيكَهُمُ اللَّهُ ۚ وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ
To, idan sun yi ĩmãni da misãlin abin da kuka yi ĩmãni da shi, to, lalle ne sun shiryu, kuma idan sun jũya bãya, to, suna a cikin sãɓãni kawai sabõda haka Allah zai isar maka a gare su, kuma Shi ne Mai ji, Masani.
138صِبْغَةَ اللَّهِ ۖ وَمَنْ أَحْسَنُ مِنَ اللَّهِ صِبْغَةً ۖ وَنَحْنُ لَهُ عَابِدُونَ
Rinin Allah! Kuma wãne ne mafi kyau ga rini daga Allah? Kuma mu, a gare Shi, mãsu bautãwa ne.
139قُلْ أَتُحَاجُّونَنَا فِي اللَّهِ وَهُوَ رَبُّنَا وَرَبُّكُمْ وَلَنَا أَعْمَالُنَا وَلَكُمْ أَعْمَالُكُمْ وَنَحْنُ لَهُ مُخْلِصُونَ
Ka ce: Shin kuna jãyayyar hujia ne da mu a cikin al'amarin Allah, alhãli kuwa Shi ne Ubangijinmu kuma Ubangijinku, kuma muna da ayyukanmu, kuma kuna da ayyukanku, kuma mũ, a gare Shi, mãsu tsarkakẽwane?
140أَمْ تَقُولُونَ إِنَّ إِبْرَاهِيمَ وَإِسْمَاعِيلَ وَإِسْحَاقَ وَيَعْقُوبَ وَالْأَسْبَاطَ كَانُوا هُودًا أَوْ نَصَارَىٰ ۗ قُلْ أَأَنتُمْ أَعْلَمُ أَمِ اللَّهُ ۗ وَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّن كَتَمَ شَهَادَةً عِندَهُ مِنَ اللَّهِ ۗ وَمَا اللَّهُ بِغَافِلٍ عَمَّا تَعْمَلُونَ
Ko kuna cẽwa: Lalle ne, Ibrãhĩm da Ismã'ĩla da Is'hãƙa da Ya'aƙũbu da Jĩkõki, sun kasance Yahũdãwa kõ kuwa Nasãra? Ka ce: Shin kũ ne kuke mafi sani kõAllah? Kuma wãne ne ya zama mafi zãlunci daga wanda ya bõye shaida a wurinsa daga Allah? Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga abin da kuke aikatãwa!
Al-BaqarahJerin Alqur'ani
286Aya
MedinanRevelation
138Aya

Fassara — Al-Baqarah 138

Surah Al-Baqarah Aya 138 - Karatu, Saurara, Fassara, Hausa : Rinin Allah! Kuma wãne ne mafi kyau ga rini daga…

Surah Aya 138/286 — Surah Al-Baqarah البقرة (Medinan). Karatu Saurara Fassara (Hausa). Saurara: Surah Al-Baqarah Saurara, Surah Al-Baqarah Fassara, Surah Al-Baqarah mp3, Surah Al-Baqarah pdf. Aya 136–140. Da Hausa: العربية.




Al-Kur'ani


Monday, September 7, 2026

Don't forget us in your sincere prayers