Az-Zumar · 69/75
Fassara Rubutun sauti — Surah Az-Zumar
وَأَشْرَقَتِ الْأَرْضُ بِنُورِ رَبِّهَا وَوُضِعَ الْكِتَابُ وَجِيءَ بِالنَّبِيِّينَ وَالشُّهَدَاءِ وَقُضِيَ بَيْنَهُم بِالْحَقِّ وَهُمْ لَا يُظْلَمُونَ ۝٦٩
Wa ashraqatil ardu binoori Rabbihaa wa wudi`al Kitaabu wa jeee`a bin nabiyyeena wash shuhadaaa`i wa qudiya bainahum bilhaqqi wa hum laa yuzlamoon
📖 Da Hausa
Kuma ƙasã ta yi haske da hasken Ubangijinta, kuma aka aza littãfi, kuma aka zo da Annabãwa da mãsu shaida, kuma aka yi hukunci a tsakãninsu, da gaskiya, alhãli kuwa, sũ, bã zã a zãlunce su ba.

🎧 Saurara
📜

Fassara — Tafsir

Ma'anar Kalmomin Ayar:

  • أَشْرَقَتِ: Ta haskaka, ta annuri.
  • بِنُورِ رَبِّهَا: Da hasken Ubangijinta, wato hasken Allah Madaukakin Sarki.
  • وُضِعَ الْكِتَابُ: An ajiye littattafan ayyuka (sahifofin da aka rubuta ayyukan mutane).
  • الشُّهَدَاءُ: Shaidu, wato al'ummar Muhammad (S.A.W) da Mala'iku da sauran shaidu.
  • قُضِيَ بَيْنَهُمْ: An yanke hukunci a tsakaninsu.

Fassarar Ayar:

A ranar kiyama, duniya (wajen taron) za ta haskaka da hasken Ubangijinta sa’ad da ya bayyana ga halittu domin yanke hukunci tsakaninsu. Sa’an nan za a ajiye littattafan ayyuka, kuma a kawo annabawa da shaidu. Annabawa za su zo su shaida wa al’ummominsu cewa sun isar da sakon Allah, kuma al’ummar Muhammad (S.A.W) za su zo su zama shaidu a kan annabawa cewa sun isar da sakonni ga al’ummominsu, musamman idan al’ummar da suka gabata suka musanta cewa annabawan sun isar da sakon. Sa’an nan Allah zai yi hukunci tsakanin dukkan halittu da adalci cikakke, ba za a zalunci kowa ba, ba za a rage masa lada ba, kuma ba za a kara masa azaba ba.

Darussa da Fa'idodin Ayar:

  1. Ranar kiyama za ta kasance ranar bayyana ikon Allah, inda duniya za ta haskaka da hasken Ubangijinta, wanda ke nuna girman Allah da daukakarsa a wannan ranar.
  2. A kowace al’umma, annabawa za su shaida wa al’ummominsu, kuma al’ummar Muhammad (S.A.W) suna da daraja mai girma domin su ne shaidu a kan sauran al’ummomi.
  3. Adalcin Allah a ranar kiyama cikakke ne, ba wanda za a zalunta, kuma wannan yana kara wa muminai kwarin gwiwa da natsuwa, domin sun san cewa Allah ba ya bata ladan masu kyautatawa.
  4. Ayat tana tunatar da mu muhimmancin ayyukanmu, domin duk abin da muka aikata za a rubuta shi a cikin littafin ayyuka, kuma za a gabatar da shi a gabanmu a ranar kiyama.
  5. Tana kara wa mumini imani da cewa kowane zalunci a duniya za a biya shi a ranar kiyama, kuma kowane alheri za a sami ladan sa, wanda hakan yake sa mutum ya himmatu ga kyawawan ayyuka kuma ya nisanci munanan ayyuka.


📜 Aya 67-71 — Surah Az-Zumar

67وَمَا قَدَرُوا اللَّهَ حَقَّ قَدْرِهِ وَالْأَرْضُ جَمِيعًا قَبْضَتُهُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ وَالسَّمَاوَاتُ مَطْوِيَّاتٌ بِيَمِينِهِ ۚ سُبْحَانَهُ وَتَعَالَىٰ عَمَّا يُشْرِكُونَ
Kuma ba su ƙaddara Allah a kan haƙĩƙanin ĩkon yinsa ba: ¡asã duka damƙarSa ce, a Rãnar ¡iyãma, kuma sammai abũbuwan naɗewa ne ga dãmanSa. Tsarki ya tabbata a gare Shi, kuma Ya ɗaukaka daga barin abin da suke shirki da shi.
68وَنُفِخَ فِي الصُّورِ فَصَعِقَ مَن فِي السَّمَاوَاتِ وَمَن فِي الْأَرْضِ إِلَّا مَن شَاءَ اللَّهُ ۖ ثُمَّ نُفِخَ فِيهِ أُخْرَىٰ فَإِذَا هُمْ قِيَامٌ يَنظُرُونَ
Kuma aka busa a cikin ƙaho, sai waɗanda ke a cikin sammai da ƙasã suka sũma sai wanda Allah Ya so (rashin sumansa) sa'an nan aka hũra a cikinsa, wata hũrãwa, sai gã su tsaitsaye, sunã kallo.
69وَأَشْرَقَتِ الْأَرْضُ بِنُورِ رَبِّهَا وَوُضِعَ الْكِتَابُ وَجِيءَ بِالنَّبِيِّينَ وَالشُّهَدَاءِ وَقُضِيَ بَيْنَهُم بِالْحَقِّ وَهُمْ لَا يُظْلَمُونَ
Kuma ƙasã ta yi haske da hasken Ubangijinta, kuma aka aza littãfi, kuma aka zo da Annabãwa da mãsu shaida, kuma aka yi hukunci a tsakãninsu, da gaskiya, alhãli kuwa, sũ, bã zã a zãlunce su ba.
70وَوُفِّيَتْ كُلُّ نَفْسٍ مَّا عَمِلَتْ وَهُوَ أَعْلَمُ بِمَا يَفْعَلُونَ
Kuma aka cika wa kõwane rai abin da ya aikata. Kuma (Allah) Shĩ ne Mafi sani game da abin da suke aikatãwa.
71وَسِيقَ الَّذِينَ كَفَرُوا إِلَىٰ جَهَنَّمَ زُمَرًا ۖ حَتَّىٰ إِذَا جَاءُوهَا فُتِحَتْ أَبْوَابُهَا وَقَالَ لَهُمْ خَزَنَتُهَا أَلَمْ يَأْتِكُمْ رُسُلٌ مِّنكُمْ يَتْلُونَ عَلَيْكُمْ آيَاتِ رَبِّكُمْ وَيُنذِرُونَكُمْ لِقَاءَ يَوْمِكُمْ هَٰذَا ۚ قَالُوا بَلَىٰ وَلَٰكِنْ حَقَّتْ كَلِمَةُ الْعَذَابِ عَلَى الْكَافِرِينَ
Kuma aka kõra waɗanda suka kãfirta zuwa Jahannama, jama'a-jama'a har a lõkacin da suka je mata, sai aka buɗe ƙõfõfinta, kuma matsaranta suka ce musu, "Ashe, waɗansu Manzanni, daga cikinku ba su je muku ba, sunã karanta ãyõyin Ubangijinku a kanku, kuma sunã yi muku gargaɗin gamuwa da yininku wannan?" Suka ce, "Na'am, "kuma amma kalmar azãba ita ce ta wajaba a kan kãfirai!"
Az-ZumarJerin Alqur'ani
75Aya
MeccanRevelation
69Aya

Fassara — Az-Zumar 69

Surah Az-Zumar Aya 69 - Karatu, Saurara, Fassara, Hausa : Kuma ƙasã ta yi haske da hasken Ubangijinta, kuma aka…

Surah Aya 69/75 — Surah Az-Zumar الزمر (Meccan). Karatu Saurara Fassara (Hausa). Saurara: Surah Az-Zumar Saurara, Surah Az-Zumar Fassara, Surah Az-Zumar mp3, Surah Az-Zumar pdf. Aya 67–71. Da Hausa: العربية.




Al-Kur'ani


Monday, September 7, 2026

Don't forget us in your sincere prayers