Surah Al-Balad Larabci da Hausa

Karanta Surah Al-Balad tare da cikakkiyar fassarar Hausa da sauti. Fassara aya bayan aya. (20 Aya — مكية). Al-Balad Saurara, Al-Balad Fassara, Al-Balad mp3, Al-Balad pdf.

Karanta da Saurara Surah Al-Balad

🎧 Aya
M Mishary Rashid Alafasy
M Mahmoud Khalil Al-Husary
A Abdurrahman As-Sudais
M Mohamed Siddiq Al-Minshawi
A Abdul Basit Abdul Samad
A Ali Al-Hudhaify
A Ahmed ibn Ali al-Ajamy
A Abu Bakr Ash-Shaatree
M Muhammad Ayyoub
A Abdullah Basfar
A Abdullah Al-Juhani
M Maher Al Muaiqly
x1
لَا أُقْسِمُ بِهَٰذَا الْبَلَدِ ۝١
📖 Fassara Aya 1
Bã sai Na yi rantsuwa da wannan gari ba.
وَأَنتَ حِلٌّ بِهَٰذَا الْبَلَدِ ۝٢
📖 Fassara Aya 2
Alhãli kai kanã mai sauka a cikin wannan gari.
وَوَالِدٍ وَمَا وَلَدَ ۝٣
📖 Fassara Aya 3
Da mahaifi da abin da ya haifa.
لَقَدْ خَلَقْنَا الْإِنسَانَ فِي كَبَدٍ ۝٤
📖 Fassara Aya 4
Lalle ne, Mun halitta mutum cikin wahala.
أَيَحْسَبُ أَن لَّن يَقْدِرَ عَلَيْهِ أَحَدٌ ۝٥
📖 Fassara Aya 5
Kõ yanã zaton bãbu wani mai iya sãmun iko, a kansa?
يَقُولُ أَهْلَكْتُ مَالًا لُّبَدًا ۝٦
📖 Fassara Aya 6
Yana cẽwa "Na halakarda dũkiya mai yawa,"
أَيَحْسَبُ أَن لَّمْ يَرَهُ أَحَدٌ ۝٧
📖 Fassara Aya 7
Shin, yana zaton cewa wani bai gan shi ba?
أَلَمْ نَجْعَل لَّهُ عَيْنَيْنِ ۝٨
📖 Fassara Aya 8
Shin, ba Mu sanya masa idãnu biyu ba?
وَلِسَانًا وَشَفَتَيْنِ ۝٩
📖 Fassara Aya 9
Da harshe, da leɓɓa biyu.
وَهَدَيْنَاهُ النَّجْدَيْنِ ۝١٠
📖 Fassara Aya 10
Kuma ba Mu shiryar da shi ga hanyõyi biyu ba?
فَلَا اقْتَحَمَ الْعَقَبَةَ ۝١١
📖 Fassara Aya 11
To, don mene ne bai shiga Aƙabã ba?
وَمَا أَدْرَاكَ مَا الْعَقَبَةُ ۝١٢
📖 Fassara Aya 12
Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake cẽ wa Aƙabã?
فَكُّ رَقَبَةٍ ۝١٣
📖 Fassara Aya 13
Ita ce fansar wuyan bãwa.
أَوْ إِطْعَامٌ فِي يَوْمٍ ذِي مَسْغَبَةٍ ۝١٤
📖 Fassara Aya 14
Ko kuwa ciyarwa, a cikin yini ma'abũcin yunwa.
يَتِيمًا ذَا مَقْرَبَةٍ ۝١٥
📖 Fassara Aya 15
Ga marãya ma'abũcin zumunta.
أَوْ مِسْكِينًا ذَا مَتْرَبَةٍ ۝١٦
📖 Fassara Aya 16
Ko kuwa wani matalauci ma'abũcin turɓãya.
ثُمَّ كَانَ مِنَ الَّذِينَ آمَنُوا وَتَوَاصَوْا بِالصَّبْرِ وَتَوَاصَوْا بِالْمَرْحَمَةِ ۝١٧
📖 Fassara Aya 17
Sa'an nan kuma ya kasance daga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi wa jũna wasiyya da yin haƙuri, kuma suka yi wa jũna wasiyya da tausayi.
أُولَٰئِكَ أَصْحَابُ الْمَيْمَنَةِ ۝١٨
📖 Fassara Aya 18
Waɗannan ne ma'abũta albarka
وَالَّذِينَ كَفَرُوا بِآيَاتِنَا هُمْ أَصْحَابُ الْمَشْأَمَةِ ۝١٩
📖 Fassara Aya 19
Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyinMu, sũ ne ma'abũta shu'umci
عَلَيْهِمْ نَارٌ مُّؤْصَدَةٌ ۝٢٠
📖 Fassara Aya 20
A kansu akwai wata wuta abar kullewa.
← 89 Al-Balad (90/114) 91 →
Karatu Surah Al-Balad Hausa – Fassara da Audio

90البلد Al-Balad 📚 20 Aya مكية



Al-Kur'ani


Tuesday, August 18, 2026

Don't forget us in your sincere prayers