Surah Al-A'la Larabci da Hausa

Karanta Surah Al-A'la tare da cikakkiyar fassarar Hausa da sauti. Fassara aya bayan aya. (19 Aya — مكية). Al-A'la Saurara, Al-A'la Fassara, Al-A'la mp3, Al-A'la pdf.

Karanta da Saurara Surah Al-A'la

🎧 Aya
M Mishary Rashid Alafasy
M Mahmoud Khalil Al-Husary
A Abdurrahman As-Sudais
M Mohamed Siddiq Al-Minshawi
A Abdul Basit Abdul Samad
A Ali Al-Hudhaify
A Ahmed ibn Ali al-Ajamy
A Abu Bakr Ash-Shaatree
M Muhammad Ayyoub
A Abdullah Basfar
A Abdullah Al-Juhani
M Maher Al Muaiqly
x1
سَبِّحِ اسْمَ رَبِّكَ الْأَعْلَى ۝١
📖 Fassara Aya 1
Ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mafi ɗaukaka.
الَّذِي خَلَقَ فَسَوَّىٰ ۝٢
📖 Fassara Aya 2
Wanda Yã yi halitta sa'an nan Ya daidaita abin halittar.
وَالَّذِي قَدَّرَ فَهَدَىٰ ۝٣
📖 Fassara Aya 3
Kuma Wanda Ya ƙaddara (abin da Ya so) sannan Ya shiryar, (da mutum ga hanyar alhẽri da ta sharri).
وَالَّذِي أَخْرَجَ الْمَرْعَىٰ ۝٤
📖 Fassara Aya 4
Kuma Wanda Ya fitar da makiyãyã.
فَجَعَلَهُ غُثَاءً أَحْوَىٰ ۝٥
📖 Fassara Aya 5
Sa'an nan Ya mayar da ita ƙeƙasassa, baƙa.
سَنُقْرِئُكَ فَلَا تَنسَىٰ ۝٦
📖 Fassara Aya 6
Za mu karantar da kai (Alƙur'ãni) sabõda haka bã zã ka mantã (shi) ba.
إِلَّا مَا شَاءَ اللَّهُ ۚ إِنَّهُ يَعْلَمُ الْجَهْرَ وَمَا يَخْفَىٰ ۝٧
📖 Fassara Aya 7
Fãce abin da Allah Ya so, lalle ne Shi (Allah) Ya san bayyane da abin da yake bõye.
وَنُيَسِّرُكَ لِلْيُسْرَىٰ ۝٨
📖 Fassara Aya 8
Kuma za Mu sauƙaƙe maka (al'amari) zuwa ga (Shari'a) mai sauƙi.
فَذَكِّرْ إِن نَّفَعَتِ الذِّكْرَىٰ ۝٩
📖 Fassara Aya 9
Sabõda baka, ka tunãtar, idan tunatarwa zã ta yi amfãni.
سَيَذَّكَّرُ مَن يَخْشَىٰ ۝١٠
📖 Fassara Aya 10
Wanda yake tsõron (Allah) Zai tuna.
وَيَتَجَنَّبُهَا الْأَشْقَى ۝١١
📖 Fassara Aya 11
Kuma shaƙiyyi, zai nisanceta,
الَّذِي يَصْلَى النَّارَ الْكُبْرَىٰ ۝١٢
📖 Fassara Aya 12
Wanda zai shiga wutar da tã fi girma.
ثُمَّ لَا يَمُوتُ فِيهَا وَلَا يَحْيَىٰ ۝١٣
📖 Fassara Aya 13
Sa'an nan bã zai mutu ba a cikinta, kuma bã zai rãyu ba.
قَدْ أَفْلَحَ مَن تَزَكَّىٰ ۝١٤
📖 Fassara Aya 14
Lalle ne wanda ya tsarkaka (da ĩmãni) yã sãmu babban rabo.
وَذَكَرَ اسْمَ رَبِّهِ فَصَلَّىٰ ۝١٥
📖 Fassara Aya 15
Kuma ya ambaci sũnan Ubangijinsa, sa'an nan yã yi salla.
بَلْ تُؤْثِرُونَ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا ۝١٦
📖 Fassara Aya 16
Ba haka ba! Kunã zãɓin rãyuwa ta kusa dũniya.
وَالْآخِرَةُ خَيْرٌ وَأَبْقَىٰ ۝١٧
📖 Fassara Aya 17
Alhãli Lãhira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa.
إِنَّ هَٰذَا لَفِي الصُّحُفِ الْأُولَىٰ ۝١٨
📖 Fassara Aya 18
Lalle ne, wannan yanã a cikin littafan farko.
صُحُفِ إِبْرَاهِيمَ وَمُوسَىٰ ۝١٩
📖 Fassara Aya 19
Littaffan Ibrãhĩm da Mũsã.
← 86 Al-A'la (87/114) 88 →
Karatu Surah Al-A'la Hausa – Fassara da Audio

87الأعلى Al-A'la 📚 19 Aya مكية



Al-Kur'ani


Tuesday, August 18, 2026

Don't forget us in your sincere prayers