Surah At-Tariq Larabci da Hausa

Karanta Surah At-Tariq tare da cikakkiyar fassarar Hausa da sauti. Fassara aya bayan aya. (17 Aya — مكية). At-Tariq Saurara, At-Tariq Fassara, At-Tariq mp3, At-Tariq pdf.

Karanta da Saurara Surah At-Tariq

🎧 Aya
M Mishary Rashid Alafasy
M Mahmoud Khalil Al-Husary
A Abdurrahman As-Sudais
M Mohamed Siddiq Al-Minshawi
A Abdul Basit Abdul Samad
A Ali Al-Hudhaify
A Ahmed ibn Ali al-Ajamy
A Abu Bakr Ash-Shaatree
M Muhammad Ayyoub
A Abdullah Basfar
A Abdullah Al-Juhani
M Maher Al Muaiqly
x1
وَالسَّمَاءِ وَالطَّارِقِ ۝١
📖 Fassara Aya 1
Inã rantsuwa da sama da mai aukõwa da dare.
وَمَا أَدْرَاكَ مَا الطَّارِقُ ۝٢
📖 Fassara Aya 2
To, mẽ yã sanar da kai abin da ake cẽwa mai aukõwa da dare?
النَّجْمُ الثَّاقِبُ ۝٣
📖 Fassara Aya 3
Shi ne taurãron nan mai tsananin haske.
إِن كُلُّ نَفْسٍ لَّمَّا عَلَيْهَا حَافِظٌ ۝٤
📖 Fassara Aya 4
Bãbu wani rai fãce a kansa akwai wani mai tsaro.
فَلْيَنظُرِ الْإِنسَانُ مِمَّ خُلِقَ ۝٥
📖 Fassara Aya 5
To, mutum ya dũba, daga mẽ aka halittã shi?
خُلِقَ مِن مَّاءٍ دَافِقٍ ۝٦
📖 Fassara Aya 6
An halittã shi daga wani ruwa mai tunkuɗar jũna.
يَخْرُجُ مِن بَيْنِ الصُّلْبِ وَالتَّرَائِبِ ۝٧
📖 Fassara Aya 7
Yanã fita daga tsakanin tsatso da karankarman ƙirji.
إِنَّهُ عَلَىٰ رَجْعِهِ لَقَادِرٌ ۝٨
📖 Fassara Aya 8
Lalle ne Shi (Allah), ga mayar da shi (mutum), tabbas Mai iyãwa ne.
يَوْمَ تُبْلَى السَّرَائِرُ ۝٩
📖 Fassara Aya 9
Rãnar da ake jarrabawar asirai.
فَمَا لَهُ مِن قُوَّةٍ وَلَا نَاصِرٍ ۝١٠
📖 Fassara Aya 10
Saboda haka, bã shi da wani ƙarfi, kuma bã shi da wani mai taimako (da zai iya kãre shi daga azãbar Allah).
وَالسَّمَاءِ ذَاتِ الرَّجْعِ ۝١١
📖 Fassara Aya 11
Ina rantsuwa da sama ma'abũciyar ruwa mai kõmãwa yana yankẽwa.
وَالْأَرْضِ ذَاتِ الصَّدْعِ ۝١٢
📖 Fassara Aya 12
Da ƙasa ma'abũciyar tsãgẽwa,
إِنَّهُ لَقَوْلٌ فَصْلٌ ۝١٣
📖 Fassara Aya 13
Lalle ne shĩ (Alƙur'ãni), haƙĩƙa magana ce daki-daki
وَمَا هُوَ بِالْهَزْلِ ۝١٤
📖 Fassara Aya 14
Kuma shĩ bã bananci bane
إِنَّهُمْ يَكِيدُونَ كَيْدًا ۝١٥
📖 Fassara Aya 15
Lalle ne sũ, suna ƙulla kaidi na sõsai.
وَأَكِيدُ كَيْدًا ۝١٦
📖 Fassara Aya 16
Kuma Ni, Ina mayar da kaidi (gare su) kamar yadda suke ƙulla kaidi.
فَمَهِّلِ الْكَافِرِينَ أَمْهِلْهُمْ رُوَيْدًا ۝١٧
📖 Fassara Aya 17
Saboda haka, ka yi wa kafirai jinkiri, ka dakata musu, sannu-sannu.
← 85 At-Tariq (86/114) 87 →
Karatu Surah At-Tariq Hausa – Fassara da Audio

86الطارق At-Tariq 📚 17 Aya مكية



Al-Kur'ani


Tuesday, August 18, 2026

Don't forget us in your sincere prayers