إِذَا وَقَعَتِ الْوَاقِعَةُ(1) Idan mai aukuwa ta auku. |
لَيْسَ لِوَقْعَتِهَا كَاذِبَةٌ(2) Bãbu wani (rai) mai ƙaryatãwa ga aukuwarta. |
خَافِضَةٌ رَّافِعَةٌ(3) (Ita) mai ƙasƙantãwa ce, mai ɗaukakãwa. |
إِذَا رُجَّتِ الْأَرْضُ رَجًّا(4) Idan aka girgiza ƙasã girgizwa. |
وَبُسَّتِ الْجِبَالُ بَسًّا(5) Kuma aka niƙe duwãtsu, niƙẽwa. |
فَكَانَتْ هَبَاءً مُّنبَثًّا(6) Sai suka kasance ƙũra da ake wãtsarwa. |
وَكُنتُمْ أَزْوَاجًا ثَلَاثَةً(7) Kuma kun kasance nau'i uku. |
فَأَصْحَابُ الْمَيْمَنَةِ مَا أَصْحَابُ الْمَيْمَنَةِ(8) Watau mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma? |
وَأَصْحَابُ الْمَشْأَمَةِ مَا أَصْحَابُ الْمَشْأَمَةِ(9) Da mazõwa hagu. Mẽne ne mazõwa hagu? |
وَالسَّابِقُونَ السَّابِقُونَ(10) Da waɗanda suka tsẽre. Sũ wɗanda suka tsẽren nan, |
أُولَٰئِكَ الْمُقَرَّبُونَ(11) Waɗancan, sũ ne waɗanda aka kusantar. |
فِي جَنَّاتِ النَّعِيمِ(12) A ckin Aljannar ni'ima. |
ثُلَّةٌ مِّنَ الْأَوَّلِينَ(13) Jama'a ne daga mutãnen farko. |
وَقَلِيلٌ مِّنَ الْآخِرِينَ(14) Da kaɗan daga mutãnen ƙarshe. |
عَلَىٰ سُرُرٍ مَّوْضُونَةٍ(15) (Sunã) a kan wasu gadãje sãƙaƙƙuu. |
مُّتَّكِئِينَ عَلَيْهَا مُتَقَابِلِينَ(16) Sunã gincire a kansu, sunã mãsu kallon jũna. |
يَطُوفُ عَلَيْهِمْ وِلْدَانٌ مُّخَلَّدُونَ(17) Wasu yara samãri na dindindin gẽwaya a kansu. |
بِأَكْوَابٍ وَأَبَارِيقَ وَكَأْسٍ مِّن مَّعِينٍ(18) Da wasu kõfuna da shantula da hinjãlai daga (giya) mai ɓuɓɓuga. |
لَّا يُصَدَّعُونَ عَنْهَا وَلَا يُنزِفُونَ(19) Bã a sanya musu cĩwon jirĩ sabõda ita, kuma bã su buguwa. |
وَفَاكِهَةٍ مِّمَّا يَتَخَيَّرُونَ(20) Da wasu 'ya'yan itãcen marmari daga irin waɗanda suke zãɓe. |
وَلَحْمِ طَيْرٍ مِّمَّا يَشْتَهُونَ(21) Da nãman tsuntsãye daga wanda suke ganin sha'awa. |
وَحُورٌ عِينٌ(22) Da wasu mãtã mãsu fararen idanu da girmansu. |
كَأَمْثَالِ اللُّؤْلُؤِ الْمَكْنُونِ(23) Kamar misãlan lu'ulu'u wanda aka ɓõye. |
جَزَاءً بِمَا كَانُوا يَعْمَلُونَ(24) A kan sakamakon, dõmin abin da suka kasance sunã aikatãwa. |
لَا يَسْمَعُونَ فِيهَا لَغْوًا وَلَا تَأْثِيمًا(25) Bã su jin wata yãsassar magana a cikinta, kuma bã su jin sun yi laifi. |
إِلَّا قِيلًا سَلَامًا سَلَامًا(26) Sai dai wata magana (mai dãɗi): Salãmun, Salãmun. |
وَأَصْحَابُ الْيَمِينِ مَا أَصْحَابُ الْيَمِينِ(27) Da mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma? |
فِي سِدْرٍ مَّخْضُودٍ(28) (Sunã) a cikin itãcen magarya maras ƙaya. |
وَطَلْحٍ مَّنضُودٍ(29) Da wata ayaba mai yawan 'ya'ya. |
وَظِلٍّ مَّمْدُودٍ(30) Da wata inuwa mĩƙaƙƙiya. |
وَمَاءٍ مَّسْكُوبٍ(31) Da wani ruwa mai gudãna. |
وَفَاكِهَةٍ كَثِيرَةٍ(32) Da wasu 'ya'yan itacen marmari mãsu yawa. |
لَّا مَقْطُوعَةٍ وَلَا مَمْنُوعَةٍ(33) Bã su yankẽwa kuma bã a hana su. |
وَفُرُشٍ مَّرْفُوعَةٍ(34) Da wasu shimfiɗu maɗaukaka. |
إِنَّا أَنشَأْنَاهُنَّ إِنشَاءً(35) Lalle Mũ, Mun ƙãga halittarsu ƙãgãwa. |
فَجَعَلْنَاهُنَّ أَبْكَارًا(36) Sa'an nan Muka sanya su budurwai. |
عُرُبًا أَتْرَابًا(37) Mãsu son mazansu, a cikin tsãrã ɗaya. |
لِّأَصْحَابِ الْيَمِينِ(38) Ga mazõwa dãma. |
ثُلَّةٌ مِّنَ الْأَوَّلِينَ(39) Wata ƙungiya ce daga mutãnen farko. |
وَثُلَّةٌ مِّنَ الْآخِرِينَ(40) Da wata ƙungiya daga mutãnen ƙarshe. |
وَأَصْحَابُ الشِّمَالِ مَا أَصْحَابُ الشِّمَالِ(41) Mazõwa hagu, Mẽne ne mazõwa hagu? |
فِي سَمُومٍ وَحَمِيمٍ(42) Sunã a cikin wata iskar zãfi da wani ruwan zãfi. |
وَظِلٍّ مِّن يَحْمُومٍ(43) Da wata inuwa ta hayãƙi mai baƙi. |
لَّا بَارِدٍ وَلَا كَرِيمٍ(44) Bã mai sanyi ba, kuma bã mai wata ni'ima ba. |
إِنَّهُمْ كَانُوا قَبْلَ ذَٰلِكَ مُتْرَفِينَ(45) Lalle sũ, sun kasance a gabãnin wannan waɗanda aka jiyar dãɗi. |
وَكَانُوا يُصِرُّونَ عَلَى الْحِنثِ الْعَظِيمِ(46) Kuma sun kasance sunã dõgẽwa a kan mummũnan zunubi mai girma. |
وَكَانُوا يَقُولُونَ أَئِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا وَعِظَامًا أَإِنَّا لَمَبْعُوثُونَ(47) Kuma sun kasance sunã cẽwa: "Shin idan mun mutukuma muko kasance turɓãya da ƙasũsuwa shin lalle mũ waɗanda zã a kõma rãyarwa ne haƙĩƙatan?" |
أَوَآبَاؤُنَا الْأَوَّلُونَ(48) "Shin, kuma da ubanninmu na farko?" |
قُلْ إِنَّ الْأَوَّلِينَ وَالْآخِرِينَ(49) Ka ce: "Lalle mutãnen farko da na ƙarshe." |
لَمَجْمُوعُونَ إِلَىٰ مِيقَاتِ يَوْمٍ مَّعْلُومٍ(50) "Tabbas, waɗanda ake tãrãwa ne a cikin wani yini sananne." |
ثُمَّ إِنَّكُمْ أَيُّهَا الضَّالُّونَ الْمُكَذِّبُونَ(51) "Sa'an nan lalle ku, ya kũ ɓatattu, mãsu ƙaryatãwa!" |
لَآكِلُونَ مِن شَجَرٍ مِّن زَقُّومٍ(52) "Lalle mãsu cĩ ne daga wata itãciya ta zaƙƙum (ɗanyen wutã)." |
فَمَالِئُونَ مِنْهَا الْبُطُونَ(53) "Har za ku zama mãsu cika cikunna daga gare ta." |
فَشَارِبُونَ عَلَيْهِ مِنَ الْحَمِيمِ(54) "Sa'an nan kuma mãsu shã ne, a kan wannan abin cin, daga ruwan zãfi." |
فَشَارِبُونَ شُرْبَ الْهِيمِ(55) "Ku zama mãsu shã irin shan rãƙuma mãsu ƙishirwa." |
هَٰذَا نُزُلُهُمْ يَوْمَ الدِّينِ(56) Wannan ita ce liyãfarsu a rãnar sakamako. |
نَحْنُ خَلَقْنَاكُمْ فَلَوْلَا تُصَدِّقُونَ(57) Mũ ne Muka halitta ku, to, don me bã zã ku gaskata ba? |
أَفَرَأَيْتُم مَّا تُمْنُونَ(58) Shin kuma kun ga abin da kuke fitarwa na maniyyi? |
أَأَنتُمْ تَخْلُقُونَهُ أَمْ نَحْنُ الْخَالِقُونَ(59) Shin kũ ne kuke halitta shi, kõ kuwa mũ ne Mãsu halittãwa? |
نَحْنُ قَدَّرْنَا بَيْنَكُمُ الْمَوْتَ وَمَا نَحْنُ بِمَسْبُوقِينَ(60) Mũ ne Muka ƙaddara mutuwa a tsakãninku, kuma ba Mu zama Mãsu gajiyãwa ba, |
عَلَىٰ أَن نُّبَدِّلَ أَمْثَالَكُمْ وَنُنشِئَكُمْ فِي مَا لَا تَعْلَمُونَ(61) A kan Mu musanya waɗansu (mutãne) kamarku, kuma Mu mayar da ku a cikin wata halitta da ba ku sani ba. |
وَلَقَدْ عَلِمْتُمُ النَّشْأَةَ الْأُولَىٰ فَلَوْلَا تَذَكَّرُونَ(62) Kuma lalle, ne haƙĩƙa, kun san halittar farko, to, don me ba zã ku yi tunãni ba? |
أَفَرَأَيْتُم مَّا تَحْرُثُونَ(63) Shin, kuma kun ga abin da kũke nõmãwa? |
أَأَنتُمْ تَزْرَعُونَهُ أَمْ نَحْنُ الزَّارِعُونَ(64) Shin, kũ ne ke tsirar da shi kõ kuwa Mũ ne Mãsu tsirarwa? |
لَوْ نَشَاءُ لَجَعَلْنَاهُ حُطَامًا فَظَلْتُمْ تَفَكَّهُونَ(65) Dã Munã so lalle, da Mun sanya shi bũsasshiyar ciyãwa, sai ku yini kunã mãmãkin bãƙin ciki. |
إِنَّا لَمُغْرَمُونَ(66) (Kunã cẽwa) "Lalle haƙĩƙa an azã mana tãra!" |
بَلْ نَحْنُ مَحْرُومُونَ(67) "Ã'a, mun dai zama waɗanda aka hanã wa!" |
أَفَرَأَيْتُمُ الْمَاءَ الَّذِي تَشْرَبُونَ(68) Shin, kuma kun ga ruwa wannan da kuke sha? |
أَأَنتُمْ أَنزَلْتُمُوهُ مِنَ الْمُزْنِ أَمْ نَحْنُ الْمُنزِلُونَ(69) Shin, kũ ne kuke saukar da shi daga girgije, kõ kuwa Mũne Mãsu saukarwa? |
لَوْ نَشَاءُ جَعَلْنَاهُ أُجَاجًا فَلَوْلَا تَشْكُرُونَ(70) Dã Mun so, dã Mun mayar da shi ruwan zartsi. To don me bã ku gõdẽwa? |
أَفَرَأَيْتُمُ النَّارَ الَّتِي تُورُونَ(71) Shin, kuma kun ga wutã wannan da kuke ƙyastãwa? |
أَأَنتُمْ أَنشَأْتُمْ شَجَرَتَهَا أَمْ نَحْنُ الْمُنشِئُونَ(72) Shin, kũ ne kuke ƙagã halittar itãciyarta, kõ kuwa Mũ ne Mãsu ƙãgãwa? |
نَحْنُ جَعَلْنَاهَا تَذْكِرَةً وَمَتَاعًا لِّلْمُقْوِينَ(73) Mũ ne Muka sanya ta wata abar wa'azi da jin dãɗi ga matafiya a cikin jẽji. |
فَسَبِّحْ بِاسْمِ رَبِّكَ الْعَظِيمِ(74) Sai ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mai girma. |
۞ فَلَا أُقْسِمُ بِمَوَاقِعِ النُّجُومِ(75) To, bã sai Na yi rantsuwa ba da lõkutan fãɗuwar taurãri. |
وَإِنَّهُ لَقَسَمٌ لَّوْ تَعْلَمُونَ عَظِيمٌ(76) Kuma lalle ne' haƙĩƙa, rantsuwa ce mai girma, dã kun sani. |
إِنَّهُ لَقُرْآنٌ كَرِيمٌ(77) Lalle shi (wannan littãfi), haƙĩƙa, abin karantãwa ne mai daraja. |
فِي كِتَابٍ مَّكْنُونٍ(78) A cikin wani littafi tsararre. |
لَّا يَمَسُّهُ إِلَّا الْمُطَهَّرُونَ(79) Bãbu mai shãfa shi fãce waɗanda aka tsarkake. |
تَنزِيلٌ مِّن رَّبِّ الْعَالَمِينَ(80) Wanda aka saukar ne daga Ubangijin halitta. |
أَفَبِهَٰذَا الْحَدِيثِ أَنتُم مُّدْهِنُونَ(81) Shin, to, wannan lãbãrin ne kuke mãsu wulãkantãwa? |
وَتَجْعَلُونَ رِزْقَكُمْ أَنَّكُمْ تُكَذِّبُونَ(82) Kuma kunã sanya arzikinku (game da shi) lalle kũ, ku ƙaryata (shi)? |
فَلَوْلَا إِذَا بَلَغَتِ الْحُلْقُومَ(83) To, don me idan rai ya kai ga maƙõshi? (Kusa da mutuwa). |
وَأَنتُمْ حِينَئِذٍ تَنظُرُونَ(84) Alhãli kuwa kũ, a lõklcin nan, kunã kallo. |
وَنَحْنُ أَقْرَبُ إِلَيْهِ مِنكُمْ وَلَٰكِن لَّا تُبْصِرُونَ(85) Kuma Mũ ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma kũ bã ku gani. |
فَلَوْلَا إِن كُنتُمْ غَيْرَ مَدِينِينَ(86) To, don me in dai kun kasance bã waɗanda zã a yi wa sakamako ba? |
تَرْجِعُونَهَا إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ(87) Ku mayar da shi (cikin jikinsa) har idan kun kasance mãsu gaskiya. |
فَأَمَّا إِن كَانَ مِنَ الْمُقَرَّبِينَ(88) To, amma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta, |
فَرَوْحٌ وَرَيْحَانٌ وَجَنَّتُ نَعِيمٍ(89) Sai hũtawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni'ima. |
وَأَمَّا إِن كَانَ مِنْ أَصْحَابِ الْيَمِينِ(90) Kuma amma idan ya kasance daga mazõwa dãma, |
فَسَلَامٌ لَّكَ مِنْ أَصْحَابِ الْيَمِينِ(91) Sai (a ce masa) aminci ya tabbata a gare ka daga mazõwa dãma. |
وَأَمَّا إِن كَانَ مِنَ الْمُكَذِّبِينَ الضَّالِّينَ(92) Kuma amma idan ya kasance daga mãsu ƙaryatãwar, ɓatattun, |
فَنُزُلٌ مِّنْ حَمِيمٍ(93) Sai wata liyãfa ta ruwan zãfi. |
وَتَصْلِيَةُ جَحِيمٍ(94) Da ƙõnuwa da Jahĩm, |
إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ حَقُّ الْيَقِينِ(95) Lalle wannan, haƙĩƙa, ita ce gaskiya ta yaƙĩni. |
فَسَبِّحْ بِاسْمِ رَبِّكَ الْعَظِيمِ(96) Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangijinka, Mai karimci. |